Sashe 46
Sakar Makafi Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Da yamma a hankali ta miƙe tsaye cikin sanyin jikin ƙin yarda da Baba idi yayi da batun ci gaban karatun Samira.
Parlour Ummi ta dawo ta gaya musu yadda sukayi dashi Ummi tace.
“Inaga in dai Mahmoud yayi masa magna zai iya yarda kin san mutumin sane sosai yace sunan babansane shiyasa yake mutuntashi”. Kiran Saddiqa da ya shigo yar ƙaramar wayarta ne wacce bata wani cika ta'ammali da itaba sai dan ƙwace mata wata da yayine ta ɗauki ƙaramar dan amsa kira, amsa kiran tayi dana shiga kitchen ta fara girki tana waya.
“Eh nima ina son zuwa Aunty Saddiqa inga Mamy na da Aunty da Malam”. Tana kallon jerin akwatunan lefen Raihana da aka kawo tace.
“Gashi baki zo kinga lefen Raihana bama, gashi har mun fara shirya tsare-tsaren bikin kinfa san yau saura 2 weeks ne a fara shagalin bikin ko? tuni ma Aunty Garkuwa ta fara haɗa mana kayan shirya Amarya”. Tana soya kazar da zatayi alfani da ita tace.
"Ni wlh nama fi begen ganina kan gadon Mamy gefenta Aunty na zaune kan bedside muna hira akan begen ganin lefen”.
Da sauran Saddiqa tace.
“Ke ki tambaya mana kizo ko kwana ɗaya ne muyi.” a hankali tace.
“Zan gwada in gani, mutumin da bama mgna na dashi ta ina zan fara”.
Cikin sauƙe numfashi Saddiqa tace.
"Ai kece kamar ba maceba da ace nice ke da irin wannan baiwar kyau da tsurar ai da tuni Mahmoud ya shigo hannu Amman ba damuwa ke ɗinma zan fara sa Aunty Garkuwa ta gyara min ke”. Tana soya kayan miyar tace.
"Wacece hakan ni ban santa ba”. Saddiqa tace.
"Ba matsala zaki santa ke dai ki tambaya in auren yazo kizo da wuri”.
A hankali tace.
“Yauma zan tambaya in ya yarda gobe zanzo”.
Allah ya kaimu Saddiqa tace kana sukayi sallama.
Bayan sallan isha, zaune suke a dinnin table shi da Sulaiman da Salim da tuni suka fara cin abincin da Ummi da kanta ta zuba musu, shi kuwa Mahmoud zaune yake kanshi a jingine da jikin kujerar Dinnin table ɗin idonsa rumtse da ƙarfi kamar yadda ya taune lip ɗinshi na ƙasa, Fariyda kuwa da Goggo Dada suna Parlour Zaitoon dake hannun Goggo Dada ta karɓa tare dace mata. "Kawota in je in kwantar da ita, kije ki samu kiyi wanka ki kwanta ki huta tun yamma kina kitchen”. Ta ƙare mgnar tana amsar Zaitoon ɗin, ita kuwa Fariyda plate ɗin da taci pasta data dafawa Abba ta ɗauka ta nufi kitchen dashi idonta na kan. Ummi dake kallonshi tana zuba mishi jolof ɗin pasta din da yaji naman kaza da ɗan wake kaɗan sai arish ɗaɗɗaya, sai kifi banda da sokokinsa yayi lugun da na kazar ƙamshisa Ummi ta shaƙa gami da cewa. "Gyara zamanka kaci abinci”. Da ƙyar ya yunƙuro ya zauna yana ƙara taune lip ɗinshi ya buɗe idanunsa da sukayi ja ya tsaida ganinsa kan plate ɗin data turo mishi.
Kai ya ɗan jujjuya cikin sanyi yace.
"Ummi na ƙoshi”. Fuska ta tsuke tace. "Saboda me?”. Yana yunƙurin miƙewa yace. "Wannan ba girkinki bane”. Sulaiman ne yace. "Ummi ni ƙara min”. Tana kallon Mahmoud da taga jikinsa na karkarwa tace.
"Kada Allah yasa kaci”. Tayi mgnar tana ƙarawa Sulaiman. Salim da ya cika bakinsa da tsokar kaza da kifin da ɗan Arish yace.
"Papi zo kaci girkin nan yayi masifar daɗi Ummi zan kawo Salam ki nuna mata yadda kikeyi wannan haɗin”. Ummi na kallon Fariyda da ta ɗan matso kusa da ita tacewa Salim. "Fariyda cema tayi ka turota yar uwarta ta koya mata”. Kai ya jinnina yana ƙara kai loma, ido suka zuba mishi ganin yadda yake tafiya a ɗan sunkuye bai miƙe tsawonsa duka ba a hankali yace.
"Sai kayi ta ɗurawa ai kowa yayi girki kai dai ci kamar gara”. Da harara ta rakashi, kamar yadda Ummi ma ta bishi da kallo mai cike da jin yaƙinin dole a raba aurensu da bashi da wani kekkyawar ma koma. Fariyda ne ta katse mata tunaninta da cewa. "Ummi Saida safe”. Cike da so ta kalleta tace.
“Allah ya bamu alkhairi Fariyda a huta gajiya ko! Allah yayi miki al'barka yasa sarakananki su miki yadda kike min”. Cikin jin dadi tace. "Amin ya Allah Ummi”. Salim ta cewa ya gaida Salma daga nan ta nufi ɗakin Goggo Dada.
Shi kuwa Mahmoud tuni ya haura sama.
Bata wani daɗe a ɗakin Goggo Dada ba ta fito ta wuce ɗakinta.
Wanka tayi tare da kimsawa cikin sleeping dress mai sulɓi da ƙelli, cikin gajia ta zauna bakin gado tana ɗan duba text message dinta.
"Kin tambaya ne? Ya barki zaki zone goben”. Saƙon Aunty Saddiqa ta kuma karantawa a karo na uku, haka ya tuna mata magnar da sukayi, tabbas tana son zuwa gida tayi kewar su baki ɗaya. Tsaki ta ɗan ja tuno yadda ya wani gwatsalemata girki masu yabawa ma zaginsu yayi, cikin jin takaici tayi kwaffa ido na tsatsfo hawaye.
Shiru ta ɗanyi gami da kasa kunne jiyo kamar sautin Tv a parlour, zamewa tayi ta kwanta a bakin gadon tana ɗan gyara zaman robar wonɗo jikinta, ido ta lumshe hakan ya bawa hawayenta damar zuba, abubuwa da yawa suka fara dawo mata.
"Mutum sam bashi da alƙibila wata rana ka ganshi kamar mai ɗan ɗigon mutunci kaɗan wata rana kuma ya nuna maka bai ma san menene mutunciba har ka ganshi kamar mara imani, sam na kasa tuna alkhairinsa a rayuta”. Tayi mgnar a fili tana miƙewa zaune, sai kuma ta fara girgiza kai a hankali tace.
"Iya kan su Zaid ne bashi da wani sharri sai alkhairi amman ni dai a kaina bashi da wani alkhairi ko yayi sai ya ɓatashi da wani abun da ya fishi zafi”. Sai kuma tayi murmurshi mai ɗan sauti tuno rashin mutuncin da ya fesawa Aunty Maryam da Ƙanwarta mayyar love, wai nifa zan zagi kan uwar ki, dan bana son kiga na ci miki zarafine shiyasa ban zagetaba, in bata fita harkata bafa zanci uwarta”. Yar dariya tayi tare da miƙewa tsaye tana goge wayenta a fili tace. "Haka dai shi kuma yake, ko ina zai iya fesa rashin mutunci, bari inje wlh yana cemin cuta zan ce masa ajali”. Da wannan tunanin ta fito, tana tsuke fuska ta nufo inda ta hangoshi kwance kan 3 seatter.
Shiru ta ɗanyi tana kallonsa ganin ya kunna TV ana ta zamga boxing, ya kuma kwanta rubda ciki ya juya kansa ya bawa TV ƙeya, a hankali ta ɗan ƙara matsowa ganin kamar yana motsi, tsuma jikinsa keyi kamar wanda ke jin sanyi, gajeren wondo Turkish irin masu taushi da faɗin nan mai roɓa ta ƙasa ƙafar da ya tsuke dai-dai kan guiwowinsa ta ɗan kalla a fakaice saboda yadda fatar jikinsa tayi mata kwarjini dan gashin dake kwance lif-lif akan sharaɓansan.
Kan kafaɗunsa zuwa bayansa da babu riga ta kalla a fizge ta janye kanta bayan ta danna mishi harara tare da taɓe baki, sai kuma tace.
“Salamu alaikum”. Shiru ba amsa sai motsinda jikinsa ya ƙara.
"Dama ina son zuwa gidane gobe in Allah ya kaimu, shine nace bari in gaya maka”. Har lau shiru haka yasa ta ɗan juyo ta kalleshi tana kwaɓe fuska tace.
“Kana jina baka cemin komai ba, nifa dan Allah nake tsoro da gudun fushin Mamy na shiyasa nake tambaya badan haka ba hmmm”. Da sauri ta ɗan ja da baya lokacin da ya mirgina ya juyo rigingine duk da idonta bai kai kan Papi naiba da yayi fitinennen tsalle da cika tamkar ƙosashshen Cucumber da ya samu kekkyawan bayi da takin da ya sashi girma da cika iya kar ƙololuwa. Ƙirjinsa da bata gama ganin cikar surarsa ba kasan cewar iya hasken tv ne yasa bata ga gashin dake kwance lip sai iya bakin nononsa dake zagaye babu shiba.
“Baka cemin komai ba”. Murya can ƙasan maƙoshinsa harshe a sarƙafe da fitinennen yanayin da ya shekara goma harda ɗorin watanni rabon da ya jishi a rayuwarsa. Ɗan ƙara matsoshi tayi dan bata ji abinda yace ba haka yasa ta ɗan sunkuyo kaɗan ta kan hannun kujerar tace.
"Inje ne?”. Murya a hautsine yace. "Dan Allah ki barni Please ki barni inji da abinda ke damuna”. Tana ɗan hararansa tace.
"To ni ka amsa min mana kawai sai in tafi”. A hankali yace. “Ki daina sani magna”. Tana kallon yadda yake ƙarƙarwa tace. "Baka da lfy ne”. Kai kawai ya iya gyaɗa mata tare da juyawa yayi rubda ciki. "Kan kane yake maka ciwo?”. Ta tambaya saboda tuno ciwon kan da yayi. Shiru ba magna ne yasa tace.
"In kawo maka mgnin ciwon kan na kane?”. A faɗace yace.
"Ni nace miki kai nane kemin ciwo da zaki addabeni da batun maganin”. Baki ta taɓe sanin masifarsa tafi yawa in bashi da lfy, a kufule tace.
“To me yake maka ciwo, ni kar ka mutum min anan ka cuci su Zaid shiyasa nake tambayarka me yake maka ciwo”. Cikin wata iriyar narkekkiyar muryar yace. “Marata kemin ciwo ki daina sani magna in ina magna tamkar zata fashe nakeji”. Da sauri ta ɗan matso dan sanin irin azabar ciwon da tasha lokacin da mararta tayi ciwo a hankali tace.
“Wanne irin ciwon marane”. Juyawa yayi da ƙarfi ya kwanta rigingine murya na rawa yace.
"Irin naki ciwon marar da kikayi mana, zaki wani addabeni da tambaya ai kin san ciwon”. Cikin iyakar gaskyarta har zuciyarta da rashin sanin dalilin ciwonta ma bare nasa ciwon tace.
“To ni ɗin nasan menene ya jamin ciwon bare in san abinda ya ja maka naka ciwon”. Sai kuma tayi shiru ganin yadda ya zamo daga kan kujerar ya kwanta a ƙasa kan tattausan carpert ya fara wani irin murƙusu da ya hanashi bata amsa.
Ita kuwa cikin tabbatar da lallai ciwo ya kai ciwo tunda har ya faɗi ya kwanta a ƙasa kan carpert ba riga a jikinsa, haka yasa ta cewa.
“Innalillahi Appiy bari inje in kira su Abba”. Cikin fizgo mgnar da riƙo hannunta yace.
"No please dan Allah karkije”. Ya ƙare maganar da fizgota jikinsa saboda jin tana cewa.....