Sashe 61
Sakar Makafi Part 2 Complete Hausa Novel · about 4 min read
ɗaukeki kizo mu haɗu a Office na zan baki shaidar a rubuce”. Da sauri tace. "Allah ya kiyaye ƙara zuwa inda kake”. A hankali yace. "Ni kuwa in baki zoba bazan bayarba, kuma dai kin sani in kowa ma bai san auren nan damaram ba ke kin sani ai ko, nasan kuma ke ba jahila bace”. Kuka ta saki haɗi da katse kiran, watoma dabaibayi yayi mata kenan. Washe gari da dare Salma ne zaune a parlour Goggo Abu cikin sanyi tace. "Ayyah Yah Mujahid ya jiki da sauƙi sosai ko”. Hannunsa dake suntume tim an saƙala masa igiya a wuya yana tallaɓe da hannun dan ɗaurin gargajiyar da akayi masa cikin yaƙini yace. "Alhamdulillah ai ni tunda aka cemin ya saki Fariyda naji na warke, kuma na yafe masa tunda dai ya sakar min matata, Alhamdulillah nan da wata ɗaya uku zuwa huɗu dai za'a ɗaura mana aure”. Salim dake kallonsa ne yayi saurin yin ƙasa da kansa yana danne dariyar ƙeta dake taso masa dan ganin yadda wawulumon bakinsa keyi in yana magna dan har yau ba'a sa masa haƙorin robarba sai wurin ya warke tunda fitar ƙarfin akayi musu, har lau kuma ga bakin a kumbure a rashi yace. "Guy nan hegene har yanzu yana nan da muguntarsa ai in dai da Mahmoud kace zakayi ka shiga uku duk sai ya sauyama kamanni mutumin da duk salon mugunta da rashin mutunci ya iyata”. Sai kuma ya ɗan danne dariyarsa yace. "To Yah Mujahid Allah ya ƙara sauƙi mu zamu wuce”. Ya ƙare maganar da ajiye masa kuɗi ya miƙe tsaye Goggo Abu da bayan sun gaisa ta tafi kitchen kawo musu dan abin taɓa wane tace. "A'a Salim har kun tashi ne ko ruwa baku shaba”. Cikin yin ƙasa da kai yace. "Mungode Goggo dayake zamu isa mu duba su Zaid ne gashi dare ya farayi shiyasa”. Tana zama tace. "Ayyah to mun gode Allah ya kiyaye hanya”. Daga nan suka fita. Dariya mai sauti yakeyi harda riƙe ciki sai yayi kamar ya tsagaita sai kuma ya kwashe da dariya in ya tuna yadda Mahmoud ɗin ya sauyawa Mujahid kamanni. Cikin dariya itama Salma tace. “Yah Salim kairfa ka turamu cikin kwalbati ka bar dariyar nan haka, kaga tuƙi kakeyi”. Yana karya kwana yace. "Ai wlh gwara da muka fito da wurin dan na kusa yi masa dariya a gabansa”. Tana kallonsa tace. “Ya kuma naga ka sauya hanya ba gidan Malam zamuje ba”. Cikin kwaɓe fuska yace. "Kiyi haƙuri sai gobe yanzu so nake in ji ɗumun jikinki shiyasa, mu koma gida gobe sai kije ki wuni”. Cikin sanyi tace. "An gama Yah Salim yadda kakeso ai haka za'ayi”. Kanta ya shafa yace. “Allah yayi miki al'barka tawan! jarumar mace”. Washe gari da safe zaune yake gaban Abba, plate ɗin abincin da Ummi tasa mishi ya miƙawa Mahmoud ɗin da cewa. “Matso kaci!”. Yana gyara ɗaurin net ɗin wuyansa da yake cikin shirin tafiya office kai a ya ɗan jujjuya a hankali yace. “Alhamdulillah Abba nayi breakfast yanzu”. Ido ya ɗan zuba mishi sai kuma ya gyara zamansa tare da cewa. “Mun gama magna da ɗan uwana bappanku Lawan ya baka auren yarsa Jidda tare da yardarta, da kuma tawa yardar da ta mahaifiyarka in sha Allah za'a ɗaura aurenku 23 January wannan hukunci ne na yanke da tattabartawa ba shawara ko neman yardarka ba, dan bazan lamunci zamanka ba aureba bayan sanin ka samu lfy, sanin halinki da gudun kar kaje kaci gaba da sheƙe ayarka kamar baya in kafaɗa tarko mata dan haka za'ayi bikin a ranar da nace maka”. Tunda Abba ya fara magna kansa na sunkuye har saida yaji ya ambaci Jidda ne ya ɗago idanunsa da tuni sun sauya launi, lokaci ɗaya jikinsa ya fara tsuma jin Abba na maimata fadin abinda ya aikata dasu Idaya a baya. Murya na rawa yace. “In sha Allah bazan sake wannan rayuwarba Abba koda ace buƙata zata kasheni bazan sake kusatar haram ba, nayiwa mahaliccin na alƙawarin ina kuma roƙon kariyar sa da shiryarsa gareni kaima kuma nayi maka al'ƙawarin har gaban abadan bazan ƙara kusantar zinnaba, in akwai ƙaddarar zina a rayuwata ta gaba Allah yasa ajali ya cimmin mutuwa ta ɗaukeni kafin lokaci yin zina ta riskeni”. Ya ƙare maganar hawaye na cika idonsa haɗi da yunƙurin tashi, cikin sanyin jiki da murya Abba yace. “Ka shirya gobe Jidda zata zo kuje kuyi.......