← Book details Sakar Makafi Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 73 OF 95

Sashe 73

Sakar Makafi Part 2 Complete Hausa Novel · about 3 min read

suna musu hidima. Ta ƙare maganar tana kallon Khadija dake cewa. Ni tun ɗazufa na aiki Sadiq yaje akwai kifi a fridge na ya kwatso mana amman har yanzu shiru. Aunty Amarya na zama gefen ta tace. “Tab ai kuwa Sadiq kam bai tafi aikenki ba dan tare da Malam suka fita wai yau kuma jikin Mahmoud ya tashi shine yace bari yaje ya dubashi. Fariyda dake riƙe da cup ɗin da Aunty Rashida ta haɗa mata damun gumba da garin daka da zuwar da Aunty Saddiqa tasata shane ta ajiye mug ɗin dan ta gama shanyeshi saboda daɗinsa yasa take shanyesa a marmarce gyatsar da ke nuna ƙoshi tayi tana kallon Mamy da ke cewa. "Yaron nan dai abin yaƙi barinsa, ɗazu Malam ɗin ke cewa Nasir ko su fiddashi waje, Nasir ɗin yace wai ba amfanin fiddashi waje dan suma zasu iya masa abinda za'a masa a wajen shune yaƙi yarda a masa aiki”. Mimy ne tace. “Allah ya bashi lfy”. Da Amin suka amsa baki ɗayansu. Washe gari ranar Alhamis da yamma tsaye suke a farfajiyar gidan motoci nata ɗaukarsu dan tafiya wurin gudanar da zazzafan walimar da wani abokin Baba Malam babban malami zai gudanar. Kusan a tare duk suka juyo suna kallon inda Zubaida yar ƙanwar Mamy take kallo tana faɗin. “Masha Allah, fatabarakallahu feeh ahsanil khaliƙin, gskya Fariyda kinyi kyau. Mafi akasarinsu kab abayoyine masu tsada a jikinsu amman fitowar Fariyda da tata shigar Abaya ta alfarma ɗaya daga cikin waɗannan Mahmoud ya aiko mata, mai kyan gaske da tsada na nunawa sai ƙyalli yake bazawa. Abayar tata Royal Blue ce irin mai faɗin nan da wadatar zare na alfarma da duwatsu masu ƙyallin Diamond, tayi masifar kyau na gasken gaske. Numfashi mai tsawo Aunty Rashida da Aisha sukaja a tare lokacin da ta iso wurin saboda Ni'imtaccen ƙamshin da take bazawa. Adda Nana tace. “Kai gskya Fariyda bazakije walimar nan ba, wannan kyau haka ta yaya zamu yarda kifi amarya kyau ai ba'a haka.” Murmurshi Raihana tayi cikin son yar uwar tata tace. "Ai kuwa itace ma a gefen damana”. Tana kallon Salma dake gyarawa Zaitoon ribbons ɗinta tace. “Dan Allah mu tafi kuga fa har huɗu ta wuce”. Humarai dake riƙe da Zaid ne tace. “To ai dama ke muke jira, kuma dama munfi son sai kowa ya tafi kafin amarya da tawagar ta su iso”. Aunty Rashida ne ta buɗe motarta hakama Khadija da A'isha, sun fara shiga motocin kenan Motar Malam ta kutso kai cikin gida, ganin haka ne yasa duk suka tsaya suna ƙara gyara mayafansu tare da gaishi bayan ya fito. Sadiq ya fito riƙe da car key ɗin Malam. Kai yake junjinina yana kallon Malam ɗin dake cewa. "Koma ciki Saddiqu ɗauki Fariyda da yaranta ka kaisu Asibiti su duba Mahmoud da jiki tun da safe da naje yake ta roƙo da magiyar a kai mishi yaran”. Sai kuma ya juyo kan Fariyda cikin bad umarni yace. "Karɓi yaranki kije ki duba Mahmoud da jiki, tun da akayi sallan la'asar da jikinsa ya tashi har yanzu bai lafaba, sai kiran yaran yake yana a kai mishi su, maza taho ki shiga ku tafi, in kunje sai Sadiq ya jiraki in kun fita ya kaiki wurin walimar”. Cikin sanyi jiki da ɓoye ɓacin ranta ta amshi su Zaid kana ta buɗe front seat ta shiga, shima Sadiq ya shiga drivern seat. Su Rashida Malam yacewa. "Ku kutafi wurin walimar ko”. Da sauri suka shiga motocin suka tafi. tuni Sadiq ya bar harabar gidan. Shi kuwa Malam Side ɗinsa ya wuce. Asbiti tana shiga cikin ɗakin tayi saurin isowa bakin gadon saboda ganin yadda ya.......
Chapter 73 · 0% Book details