← Book details Sakar Makafi Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 57 OF 95

Sashe 57

Sakar Makafi Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read

( بِسْمِاللَّهِ، اللَّهُمَّ جَنِّبْنَا الشَّيْطَانَ وَجَنِّبِ الشَّيْطَانَ مَا رَزَقْـتَنَا) A gigice ta hannunta ƙan ƙirjinsa da iyakar karfin da Allah ya bata take tureshi, amman ko gezau. Wani irin firgitaccen kuka mai tafe da saɓulellen sauti ta sake, lokacin da taji yana ƙoƙarin amintar da kanshi gareta. Da gudu Amina dake parlour ta buɗe ƙofar ta fita tana dariya mai sauti haɗe da cewa. "Eh ai shike nan magna ta ƙare yadda suka ɗaura auren ba shawararka, haka zaka kasance da matarka ba tare da shawara dasu yadda zakayi da itaba inma kayi sakin ai yanzu dai ka maida matarka, saki kuma tunda a hannunka yake ai hike nan ni dama naji a jikina Mahmoud bai saki Fariyda ba yanzu kuma na tabbatar baiyi sakiba su Abba dai ya kindayar zan ko zuba ido inga salon wannan ta ƙaddamar.” Da ƙarfi ta taune lips ɗin ta duka biyu haɗi dasa hannunsa ta kama ɗamatsan hannunsa ta matse cike da gigita ta ɗago kanta tana jujjuya tana nemo numfashinta dayake ƙoƙarin maƙalewa a maƙoshinta dan jin raɗaɗin baƙocinsa, a fizge take magna cikin kokawa da nemo numfashinta. “Ap... Appy.... Apiypiy Za... feee...feeh zaka kasheni fa”. Ta fizgo mgnar haɗe da fizgo numfashi, ta kife kanta bisa ƙirjinsa zafin da takeji yasata dasa masa jizon da yasashu kallon fuskarta da tayi jazir zufa ne ya tsatstsafo mata tako ina, da masifar gigitan cimma buri da mamakin jinta kib tamkar bata taɓa sanin ɗa na mijiba ya kuma ƙulla SAƘAR da zai haɗe rayuwarsu, komawa tayi ta sake kanta kan pillow murya maƙale a maƙoshinta tace. "Ba.... Haka yake ba. Yah Amin ba. ya min haka... Kullum shi sai ya bini a han kali.......zan mutufa”. taja ƙarshen mgnar cikin ficewar hayyacinta tama mance batun ƙwace kai ko batun ai ya saketa. da sauri ya tallabo kanta da hannunsa ɗaya, ɗaya kuma yana ɗan marin fuskarta a ganin idanta sun ɗan kafe sunyi sama alamun zata sumemishi, ɗan marin fuskarta yakeyi yana magna cikin rawan jiki da tsananin kaɗuwar to ta yaya kenan Yah Amin ya rayu da ita har Allah yasamar da cikin su Zaid yarinya sai shegen longomi da raki ga saurin suma abu kaɗan ta sumewa mutum. “My Angle! Angel!! Farriyyhaaaah”. Ina bazata iya amsawa ba, dan kiran sunanta da yayi da ida nufinsa duk a haɗe yasata jan dogon numfashi ta fizgeshi ta feso numfashi a hautsine. Kuka mai sauti ta fara tanayi tana ɗan dukan ƙirjinsa haɗe da magiya. Baya ji bare ya gane me take nufi ko me take buƙata ko me take faɗi. Wasu surutan da shi kansa baisan ma me yake faɗaba ya farayi. “Jazakallahu khairan wa yatta ƙinallahu jami'an Yah Amin Ngd matuƙa da wannan kyautar mafi ƙololuwar daraja da daɗi da ka barmin Yah Akheeh. Allahumma Gafirlahu warahamhu Ɗan uwana, Ngd Yah Amin ka barmin gado mafi daɗi da daraja. Allah ya azurtata da janatul Firdausi”. Yana surutan da addu'ar nemawa Aminullah gafara da rahamar Allah. Yana mai ƙara tabbatar da ita matsayin matarsa ta sunna a ƙarƙashin inuwar aure. Tayi kuka tayi magiya har ta dawo tayi shiru dan disashesshiyar da muryarta tayi sai hawaye masu zafi da ke bin kuncinta suna gangara har kan pillow wani na korar wani tana jin duk abinda yake faɗa amman ko hannunta bata jin zata iya motsawa. Shi kansa bai san adadi lokacin ba ya dai jishi cikin aminci da natsuwa ta haƙiƙa, a hankali ya zame ya kwanta gefenta tare da jawota jikinsa ya ɗaurata kan ƙirjinsa bakinsa na dai-dai kunnenta ya fara magna cikin yayyankewar numfashi. "Thanks my Angel kiyi haƙuri Papi ɗinki ya wahala dake ko, ki yafe min kiyi haƙuri ki yafe min”. Sai kuma yayi shiru dan shi kansa yayi masifar mamakin jin wai yau shine bakinsa ke iya furta kalmar bada haƙuri harda neman yafiya bazai iya tuno ko ya raɓa furta wannan kalmar ba a rayuwarsa ko a wurin iyayensa sai dai yayi ta bubiyarsu. Sai kuma kawai ya kwantar da ita yayi mata rumfa da ƙirjinsa ya fara kissing nata tako wanne sashin jikinta har zuwa mararta, idon dake cike da hawaye ta rumtsa cikin tsaro da mgnar zuci ganin kamar zai koma tace. "Shike nan yau kam zai kasheni Yah Allah ka kawo min ɗauki kaga wannan mugun bawanka Mahmoud zai kashe baiwarka Fariyda mai rauni, Allah kagani bazan iya ƙwatar kainaba yafi ƙarfina, Allah ka kawo min agaji”. Sai kuma ta buɗe idonta jin ya ɗagata cak yana faɗin. "Duk wani abu na duniya da Yah Amin yake masifar so ko jin dadinsa ko bana sonshi sai yasa na soshi kuma sai ya ɗanɗana minshi yasa na fahimci daɗinsa gashi a karshe rayuwarsa na yana gargarar mutuwa ma, yayi kalmar da tasa aka mallaka min ke ya bani damar jin wannan ni'imtaccen daɗin duniyar, wlh ban taɓa jin makamancinsa ba duk abinda na aikata ke ta musamman my Angel”. Ya ƙare maganar yana shiga bathroom ɗinsa da ita, ruwa ɗumi ya haɗa a bath ɗin sannan ya shiga tare da ita. Bayan kamar 24 minute ya fito rungume da ita, yana ɗaure da towel ita kuma bathrobe nashi ya sa mata, kan 3 seatter ya kwantar da ita, haɗi da durƙusawa gabanta saboda wani irin ƙarƙarwa da jikinta keyi kuka take takmar ranta zai bar jikinta kukane na baƙin ciki da ƙuncin abinda yayi mata da raɗaɗin dake game jikinta, hannunta ya kamo ya haɗe da nashi ya sarƙafe yatsunsu kissing bayan hannunta ya rinƙaya ba ƙaƙƙautawa yana kallon idanta dake zubda ƙwalla duk da a rufe suke jikinta duk sai karkarwar yake ya ɗauki wani irin zafi mai tafe da zazzafan zazzaɓi. "Please My Angel kiyi haƙuri ki daina kukan nan ya isa haka, kimin magna mana, me kikeso inyi miki? Me kikeso a duniyar nan”. Ya ƙare maganar yana kallon yadda ya turi lips ɗinta na ƙasa, a galabaice ta buɗe idonta, jin ya manne bakinshi da nata ya na lasar lip ɗin, hannunta tasa bisa kanshi ta fara turewa tana sakin sheshheƙan kukanta murya disashe cike da rauni a murya can ƙasa a sanyaye tana rawan kuka cike da ƙara jin tsoronsa da karo dashi ya kashe mata dukkan wani kuzarinta a raunace tace. "Ka cuceni ka keta min haddi Allah zai saka min muguntar da kayi, ka sakeni ka barni in tafi gidanmu ka tsareni dan kasan ka karfi kayi min mugunta kamar zaka cinyeni”. Ta ƙare maganar tana zubda ƙwalla. Kanta ya fara shafawa yana jujjuya mata kai murya a tausashe cikin tausayawa yace. "Zaki tafi Farriyyhah har lau kuma da igiyar aurena a kanki”. Cikin iyakar gaskyarta tace. "Wallahi bani ba kai har abada, koma baka sakeni bane wlh sai ka sakeni in sha Allah ba zan ƙara dawowa gidanku ba”. Kanshi ya jujjuyawa mata yana kissing Cheek ɗinta yace. "Tunda dai saki a hannuna yake ai shike nan, ni dai kiyi haƙuri kiyi shiru my Angel kice min duk abinda kikeso ko maye ma kice min ni na yafe miki. Allah yayi miki al'barka ya miki tukuici da jannatul Firdausi”. Murya a disashe cikin kuka da tura baki tace. "Amin Ya Allah”. A hankali ya miƙe tsaye da nufin gyara gado ya koma da ita kai, sai kuma yayi sauri juyowa yana kallonta yace. “Yah salma”. Sai kuma ya ɗauki wayarsa kan hannun kujerar ya zauna yana kiran Dr Fadil yana kuma kallon kan duvet ɗin da jini ya ɓatashi kaɗan, hannunshi kuma na kan fuskarta da jikinta da yayi masifar zafi sai karkarwa takeyi. Maganar 6 minutes sukayi dashi kana ya katse kiran ya text message ya turawa Aunty Amina. Kallon Ummi dake ce mata. "Ina Fariyda ne”. Miƙewa tsaye tayi ta nufi hanyar fita tana faɗin. “Ta shiga wankane, bari inje mu gaisa dasu Maman Samira kafin ta gama shirin ta sauƙo”. Cikin gamsuwa da hakan Ummi tace. "Dama kuwa Maman Samira na zazzaɓi je ki dubata”. Daga nan ta juya ta fita, bakin ƙofar shiga part ɗin su Maman Samira ta zauna inda zata iya hango duk motar mai shiga da fita, koda suka gaisa da Maman Samira kai ta kuma sunkuyarwa tana ƙara karanta text message ɗinsa na farko da wanda ya mata yanzu. "Please Mom Hafiz help me Dr Fadil zaizo tare da wata Doctor mace, in sunzo ki kaisu wurinsu Ummi su gaisa sai ki kawosu sama zasu duba Farriyyhah bata da lfya”. Sai kuma ta kalli na biyun. "Please kisan yadda zakicewa su Ummi karkice musu bata da lfy kice sunzo duba Zaid da jikine, kije waje ki jirasu”. Numfashi ta fesar haɗi da tura masa amsa ba matsala. Shi kuwa Mahmoud a hankali ya sunkuyo kanta ya ɗagata zaune da sauri ya kuma kwantar da ita jin ta sa kuka dan tsami da raunin da yaji mata yayi murya a disashe tace. "Ni ka barni”. Kissing neck ɗinta yayi yana shafa fuskarta yace. "My Angel zan kaiki ɗakinki ne in sa miki kaya, kafin Dr ya iso”. Ido na zubda wahaye tace. "Ka barni kawai in mutu kowama ya huta”. Tallabota yayi ya ɗagata cak ya rungume kamar yar baby ya fito da ita yana faɗin. "Bana son wata mace tazo ta shigar miki turakar mijinki ne shiyasa zan medake can, dan nan ɗakinmu ne mu biyu kaɗai ba yadda wata mace zata shigo mana ciki”. Yana shiga ɗakin ya kwantar da ita Wordrobe ɗinta ya buɗe tattausar jallabiyar mata ya jawo. Dai-dai lokacin kuma Dr Fadil na biye da Amina dake ce masa. "Mu isa ku gaisa dasu Ummi tukun”. Suna shiga Ummi da Goggo Dada suka haɗa baki wurin masa maraba, Zaid ya jawo ya ɗaga yana masa wasa ita kuwa Dr Fatima Zaitoon ta jawo tana cewa. "Yah Allah ka azurtani da haihuwa kafin mutuwata”. Cikin tausayawa Dr Fadil yace. "Amin ya Allah, in sha Allah zaki haihu Dr”. Ummi ne ta amsa gaisuwar da tayi mata haɗi da cewa. "Allah ya baki yara masu al'barka”. Amin sukace duka ita kuma Dr Fatima Amina dake cewa Goggo Dada. "Sun zo duba Zaid ne da jiki”. Fadil ya ɗaura da cewa. “Tunda suka dawo ina son zuwa aiki yamin yawa sai yau”. Cikin ɓoye yanayin da suke ciki Ummi tace. "Amina jeki gayawa Mahmoud ɗin da Fariyda su zo
Chapter 57 · 0% Book details