← Book details Sakar Makafi Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 67 OF 95

Sashe 67

Sakar Makafi Part 2 Complete Hausa Novel · about 7 min read

gareni ba, akan me zaku matsa min da ciye-ciyen aurena ma da Yah Amin ba abunda kukayi min ai”. Adda Nana tace. "Ai dai Nan kusa zakiyi auren, sanin matsalarki ne yasa aka fara gyaraki, don ko a baya da an miki haɗi kafin aurenki da Aminullah da bazaki zama mai gudun mazaba”. Aunty Saddiqa tace. "Ni kam ma lokacin da na bada Aunry Garkuwa tayi musu haɗin ai da aurenta na dai san ba abinda ya haɗata da Mahmoud shi yasa nasa ayi mata haɗin mai kyau nata da Ban na Raihana da ban, kuma kayan Aunry Garkuwa ki shekara zasuyi a jikinki lfy laune kuma dole ke zakici tunda da sunanki na biya”. A hankali tace. “Tasaida safe zan ƙarasa , Allah cikina ya cika da damun fura da nonon da kika bani ɗazu da yamma”. Adda Nana tace. "Au damun gumbar madara da hakkinmayin ne fura da nono”. Da sauri Aunty Saddiqa ta gyaɗa mata kai tace. "ai inkiyarta kenan furar mata”. Tana jawo bowl ɗin kazar tace. "Ni bani inci, yara ana son gyara muku zaman aurenku kuna rigima”. Da sauri Aunty Saddiqa tace. “Dan Allah karkici kinga shi wannan haɗinsa na dabanne sabida Fariyda nasa Aunty Garkuwa ta haɗa mata set na gyara amare na musamman wanda zai magance matsalarta. Tunda naga alamun Yah Muhajid ɗin ma a hannu yake, wai so yake ayi aurenfa rana ɗaya dana Raihana”. Ta ƙare maganar tana miƙawa Fariyda zumar dare ɗaya wanka uku tace. “Karɓi ki shanye wannan dan ba lallai ki kuma samun wani miji mai haƙurin Yah Amin ba ina kin tsumu zafin zai miki sauƙi”. Ido ta lumshe lokacin da ta kai zumar bakimta dan daɗinta da ɗanɗanonta yasa batayi musu gardamar shaba, cup ɗin ta miƙa mata baya ta shanye tana kallon Adda Nana dake tambayarta set ɗin nawa nawa ne. Miƙawa Fariyda robar gumbar madara da kwakwa tayi tace. "Na Raihana set ɗin 120k ne na Fariyda kuma 150k ne set ɗinta ni shine gudumowata garesu, kuma dole in tsaya inga sun cinye komai”. Ta ƙare maganar tana kallon Fariyda dake tauna gumbar madara dake haɗe da dabino da kwakwa, hannu Adda Nana tasa tace. "Wannan dai sai naci”. dariya tayi tace. “In kina sofa sai in baki number GARKUWAR MA'AURATA nan 08069423567 sunanta Aysha Aliyu Garkuwa, inkiya GARKUWAR MA'AURATA ko MARUBUTA tana Saida kayan mata masu masifar kyan gaske, in kinaso kiyi mata magna akwai haɗin Amaren budurwa ko bazawara akwai ma masu jego, akwai na uwar gidaye, in matsalar matsi ko sha'awa ko ni'ima kikeso kawai ki mata bayani ki tura mata kuɗi zata haɗa miki kayan da zakiji dadinsa in ma matsalar Infection gareki tana Saida mganinsa sadidan akwai na 10k na 15k na 20k maganin Infection ɗin fa kenan na kayan mata kam iya kuɗinki iya shagalinki ne hawa biyune akwai manyan set daga 50k 60k 70k 80k 90k 100k 120k har zuwa 150k ƙananan set ɗin kuma daga 40k 35k 30k 25k 20k 15k babu haɗin ƙasa da haka kinga kamar Fariyda na mata bayanin halittarta kuma ta bani tabbacin komai zaizo da sauƙi akwai wani abu datasa a set dinta *Daɗi har maɗiga* tace wlh in dai tana amfani da wannan ba batun jin zafi kam dan sauƙar da ni'ima yakeyi dama amare ƙanana take sawa shi in an aurar dasu in farko rashin sabo da jin zafi suna fara sawa shike nan”. Murmurshi Adda Nana tayi tace. "Ai kuwa zan mata mgna dan nima kusan irin Fariydar ne kawai dauriya na fita ni bana raki dole zan sayi wannan Daɗi har maɗiga”. Washe gari da yamma Gombe Sulaiman ya kalli Mahmoud yace. "Ni dai nasan wannan hukuncin yayi tsauri a kansa saboda koma me yayi da yardarka yayi dan haka kasa a dena nemansa da bibiyarsa kai ka bashi dama”. Kwaffa yayi ya kusa kai cikin waiting area saboda lokacin tashin jirginsu ya kusa, gab da magrib ya sauƙa a Abuja. Anan cikin Abuja ya kwana da alamun bada aiki na musamman akan Faisal a wurin hukamr yan sandan ciki, sai washe gari da yamma ya dowo Kano Babu wanda yasan abinda ya aikata a Gombe da Abuja sai Allah da sai kuma Sulaiman. Bayan kwana biyu. Goye da Zaitoon take tana riƙe da cup ɗin da Aunty Saddiqa ta dama mata dakan da madara, Raihana kuma na cin gumbar ita kuwa Aunty Saddiqa waya take yi da mai musu gyaran jiki akan tazo da wuri mana su fara, koda tazo ba sonkai tace. “Fariyda da Raihana ai duk fatar jikinsu ba sai an wani musu hidimar gyara ba musanman ma Fariyda”. Aunty Sadiya tace. "Gskya dai kam dan ko aurenta da Yah Amin da aka gwada yi mata saɓulewa halawar takeyi da dilka duk basa riƙe fatarta da santsi da tsulɓin fatar”. Cikin gamsuwa da hakan Aunty Saddiqa ta bata kuɗin mai ta zuba a motarta ta sallameta. Wuraren ƙarfe tara na dare, Raihana ne goye da Zaid, ita kuma Fariyda zaune take rungume da Zaitoon kusan a tare suka kuka da kiran sunan Appiyn, Aunty Saddiqa da ta shigo riƙe da bowl biyu ta miƙa kowa ɗaya ta tsuƙe fuska ganin yadda Fariyda ta yamutsa fuska tana kwaɓe baki cikin ƙosawa da shaye-shayen da ciye-ciyen da yayun nata ke tirsasamata Aunty Saddiqa na zama kusa da ita tace. “Ya kin fara karanta littafin ne?”. Tayi tambayar tana kallon Fariyda dake riƙe da wayarta cikin yin magana a hankali dan kar Zaitoon data fara bacci ta farka tace. "Eh na fara gsky littafin kam zai yi daɗi amman bana sauri tun da safe fa dana fara har yanzu a page 16 nake”. Raihana da ta matso bakin gadon tana jijjiga Zaid tace. "Tab ai wlh ni tun tuni na gama part 1,2 har 3 din na gama da yake shi baida yawa sosai gsky littafin yayi masifar daɗi rayuwar Yah Sheikh da Aysha darasine babba”. Adda Nana tace. "Ai duk littatafan Aysha Aliyu Garkuwa ba littafin da nafi so kamar Garkuwa”. Aunty Saddiqa tace. "Ni kuma nafi son Tubali da Sakayya sun masifan bin daɗi”. Numfashi Fariyda ta ɗan ja tana kwantar da Zaitoon tace. "Gsky dai GARKUWA zai yi daɗi duk da ba wani karanta Novel nakeyi ba, amman wannan salon labarin akwai armashi sosai”. Raihana ta kwantar da Zaitoon gefen Zaid kana ta ɗauki bowl ɗin data ajiye kana dressing mirror, Adda Nana ta ɗauki na Fariyda data ajiye kan bedside drawer ta miƙa mata, dahuwar jannama da yasha haɗin ingantaccen maganin Garkuwar ma'aurata tace maza cinye kinga ba yawa. Ɗan tsaki taja tace. "Wai dan Allah ke kici mana”. Da sauri Aunry Saddiqa tace. "Ba ita ma sayawa ba, kuma kinga ni dai ba zuwa aurenki da Yah Mujahid zanyiba shiyasa duk abinda na saya yanzu zaki cinye tun kan in koma bazaki sani asaraba”. A hankali ta jawo ta fara ɗan ci tana kallon Raihana dake cin abinta ba gardama, ita kam Allah ya sani bata son magani dan ma basu da wani ɗaci ko bauri. Sunaci suna ɗan hira Fariyda kuwa tana ɗan karanta littafin. Kiran Salma da ya shigo wayartane yasata ɗan sauƙe numfashi tana kallon kiran da lokacin ƙarfe goma na dare har ya gota, katsewar kiran ne yasata ci gaba da karatun, kira da ya kuma shigowar ta zuba wa ido a fili tace. "Shegen iyayi ko me kuma zaki gaya min a daren nan”. Ta ƙare maganar tana sa tsokar naman a bakinta da ƙoƙorin amsa kiran, sai kuma ta fara sa numbers ɗin buɗe wayar saboda katsewar kiran kafin ta amsa ɗin. Kiran Salman ne ya shiga wayar Adda Nana, amsa tayi tana faɗin. "Ke ina kika bar mijinki kika faman kiran mutane a daren nan”. Sai kuma duk suka zuba wa Adda Nana ido jin tana faɗin. “Innalillahi wa inna'ilaihi raji'un! Mahmoud ɗin!? Salma yana ina yanzu?”. Ido Fariyda ta zuba mata tamkar zata fiddasu waje yadda ido ta ke buɗe haka lip ɗinta suma suke buɗe lokacin da taji Adda Nana na faɗin innalillahi y.......
Chapter 67 · 0% Book details