Sashe 92
Sakar Makafi Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Dariya Salma tayi tana amsar su Zaid Sadiq yace.
"Wai ashe dama kece Mrs Salim, wato ko sunanki ma bazai kiraba kai Guy nan Duniya ne akwaishi da class ga ƙwarjini da kare girma. Yah Mujahid nacan raɓe a mota yayi shiru kamar wanda ubansa yayi masa faɗa.
Farooq ne ya miƙe yana faɗin.
"To kuma zamuyi gaba fa dan naga tafiyar Gembu 2 Taraba kamar ya kusa kano to Gombe”.
Miƙewa su Adda Nana sukayi suna faɗin.
"Muma muje abokan suna jiranmu a waje mun barsu kamar drivers ɗin mu ba daɗi”. Nan sukayi sallama da kakannin nasu, suna fitowa suka shiga gidan kawunsu yayan Mamy, daga nan gidan Aunty Jamila sukaje, acan suka samu Ango Bashir da amarya sun kaiwa Aunty Jamila ziyara daga nan kuma suma gidan Hajja inna zasuje dan daga tafiya dinner zasu tare a gidansu na taraba su da Gembu kuma sai ziyara.
Ƙarfe ɗaya dai-dai na rana zaune yake tsakiyar gadon ya miƙe sawunsa tana kwance tayi pillow da sawunsa a dolen da yasata ta kwanta tayi bacci haka tana ƙumƙuni da kukan takaicin yadda ya hanata zama cikin ƴan uwanta a haka bacci yayi awon gaba da ita.
Duk jikinta na cikin duvet ɗin sai kanta kawai da yake kan cimyarsa ɗaya tana fuskarsa ɗaya gefen kuma system nashi ne a kan pillow yana daddannawa sai woyoyinsa dake kan bedside drawer.
A hankali ta ɗan gyara kwanciyarta haɗi da miƙar da hannunta ta zagayo ƙugunsa tana kifa kanta kan mararsa.
Numfashi mai nauyi ya sauƙe jin ana Knocking yasan Sulaiman ne dan shi ya uzzura masa da kira yana son magna dashi wayarsa ya ɗaga ya kira Sulaiman ɗin yana ɗagawa murya a daƙile yace.
"Sai ka gwada buɗewa ai sai in kaji bai buɗu bane kafin ka uxzuramin da bugu”. Yana kaiwa nan ya katse kiran, murɗa handle ɗin ƙofar yayi haɗe turawa bakinsa ɗauke da sallama.
Yana ƙara rufe jikinta ya nunawa Sulaiman ɗin kujera, tun kallon forko da yayi masa bai kuma kallonsa ba har ya zauna Admiral dake kan table ɗin dake gaban kujerar ya ɗauka ya ɓalle marfin yace.
"Yaushe zaka koma?”. Yana danna system nashi yace.
"Kana da matsala da komawata ne?”. Fuska a haɗe Sulaiman yace.
"Eh ina dashi wai dan Allah kai Papi wacce iriyar zuciyace gareka, nidai kasan bazan iya abinda kai zaka iyaba, kasa an kama Sa'ad an rufeshi da manyan hujjojinka da kai ka bashi damar yin haka ka dawo kace yana neman matarka, ka haɗa harda Faisal ni ko ganinsa ban taɓayi ba, iyaye Sa'ad ni suke sawa a gaba da neman alfmar a basu belinsa kasa an hana, shima Faisal ɗazu yayansa yake ta kirana akan su beli suke so, kasa an maida Sa'ad Abuja anje an haɗashi da Faisal iyayensu na takura min Mom Sa'ad har kuka takeyi nima ta sani kuka kayiwa Allah da Manzonsa kasa a bada belinsu in ma shariyar kakeso kuyi sai kuyi suna gaban iyayensu”.
Tunda ga Knocking ɗin da Sulaiman ɗin yayi ta farka shigowarsa ne yasa ta kasa motsawa.
Shi kuwa Mahmoud tunda Sulaiman ɗin ya fara magna bai ƙatseshi ba. Sai danne-dannensa yake yi saida yaji yayi shirune ya ɗan ture system nashi, yana gyarawa Fariyda kanta ya ɗan sunkuyo ya manna mata kiss a goshinta haɗe da tattare ɗan gashinta daya fito ya cusa cikin hular kanta kana a hankali ya ɗago kanshi yana kallon Sulaiman ɗin murya cike tab da ɓakin ciki yace.
“Sai sun kasheni ne zan ɗauki mataki a kansu, ka kuwa san irin azabtar dani da zuciyata da sukeyi? Yaron nanfa Sa'ad ko sunansa bana sonji, yadda kasan tsohon maye haka yake daga ganinta fa a hotel a Ethiopia inda mukayi transit ya maƙale kamar kaska sanadin shi na kusan mutuwa a cikin flight dole dan azabtar ƙuna da zuciyata keyi ya sakar min fiver kamar zai ɗauke raina haka dole na kwana a Mumbai, da yake shi mugune haka ya addabi rayuwata da kira, ka kuwa san yadda nakejine duk sanda suka kira, ji nake kamar zan haukace barin na haɗewa da jini yake yi fa da irin kankane da ka haukace, a haka fa ya bimu har Ahmedabad lokacin da akayi wa Zaid aiki, inaji ina gani bana son inyi nesa da Zaid amman dole nake barin inda suke dan nasan zan iya kai masa hannu in kasheshi a banzan duk ya gigitamin kai na kasa haɗa inuwa ɗaya dashi, shi kuma wannan jakin mai baya kamar na kura kan kiransa na jarabar tsiya yasa na targaɗata a banza na kwace wayarta amman da yake duk shegune basu san darajar igiyar auren ba wai sai suyi ta kiran wayar Yah Amin a kanshi aka cemin wai nakasashshe ne ko mene ai wlh sai na nakasa hege in bai cire idonsa kan matataba, shi kuma wannan Zubairu ne ko Faisal banza mai kama da bayahuden daga ganinta a Airport a Istanbul shima ya maƙale, su makafine basa ganin ita matatace ko su Zaid da Zaitoon ai sun isa su san matatace amman da yake kwakwalen kifi garesu haka suke ta zura mata ido kamar mayu, ai wlh ba don haƙƙin raiba wlh kashesu zansa ayi ko zuciyata zata samu salama”.
Cikin mmki Sulaiman yace.
"To wai ba kaine ka basu dama ba, shima yaushe ka fara son Oum Zaid ɗin ni dai na sanka farin sani ciki da waje nasan baka shiri da ita tun tana matsayin matar Yah Amin ka tsaneta kana faɗa da bakinka kuma har zuciyarka nasan haka ne kuma koda aka muku aure baka sonta yaushe ka fara sonta har irin wannan son ba kaine ke faɗin zaka aura mata Sa'ad ba”.
Yana datse lips ɗinshi yace.
"Makahon sone, nima kaina ban san yaushe bane ko ta yayabane koma dai menene, na dai san kawai na fara jin tausayinta ne tun ranar da Yah Amin ya rasu, iya kar tausayune a wannan lokaci bana jin komai face tausayin kaina da ita, inajin tana bani tausayi saboda su Zaid nasan irin son da Yah Amin yake yi mata nasan ta rasa masoyi na gskya ta bani tausayi yadda tayi ta suma tana farfaɗowa na gamsu tana masifa son Yah Amin ɗina, ni kuma duk maison Yah Amin ɗina ina sonshi, a ranar naji cewa tana jin irin azabar da nakeji na rashin ɗan uwana in ta suma daɗi nakeji zuciyarta zata samu ta huta akan irin azabar da nakeji, wlh iya wannan na sani ban san yaushe ne kuma a inaba kuma ta yaya so yakeba, ka sani ban taɓayi ba bansan ya so yakeba bayan son Ummi da Goggo Dada Aunty Amina Hafiza babufa son wata ya mace a raina su kuma sonsu da nakeyi ba irin wanda nakejin inayi mata bane ko son da nakewa Zaitoon ba irin nata bane nata wani irine na daban mai hana zuciya sukuni more Especially in bata kusa dani ji nake kamar zuciyata zata fito waje yawon nemota”.
Sai kuma ya ɗago kansa ido na zubda ƙwallan yace.
"Kawai dai inajin son da nakewa Yah Amin ne ya dawo kanta, inajin itace zata meye min gurbinsa Sulaiman kasan waye Yah Amin a wurina ta yaya zanƙi abinda yakeso ya kuma mallakamin”.
Ya ƙare maganar yana shafa kanta.
Ita kuwa Fariyda wasu tafasassun hawaye ne wani ke korar wani.
Shima Sulaiman shiru yayi indo cike da kwalla yake kallon yadda Mahmoud ya sunkuya yana kissing ɗinta tako ina na jikinta haɗi da cewa.
"I love har bazan taɓa jin daɗin rayuwarnan ba in babu ita, zan iya kauda duk wani abu da zai rabani da ita, babu wani mahaluƙin ɗan adam da zan iya barwa ita Sulaiman ji nake kamar zuciyata zata fashefa in na tuna yadda tsinannun karnukan can ke kallonta suna waya da ita suji muryarta suga fuskarta shi matsiyacin harda shaƙar ƙamshinta ba kamata yayi insa a kashe min su kawai bama?”. Ya ƙare maganar da alamun tambaya da iyakar gskyar zuciyarsa.
A hankali Sulaiman ke girgiza masa kai haɗi da cewa.
"Rai yana da girma da daraja, ka daina ambaton kisa, kayi haƙuri ka yafe musu koda suna da laifi naka yafi yawa, dan kaine ka basu dama dafa yardarka sukeyi ko a wurin Allah ka fisu laifi”. A hankali ya fara motsa lips ɗinshi yana istigfari haɗe da cewa.
"Bana son tunowa Yah Allah na tuba nayi wasa da igiyar aurena Allah kada ka jarabceni da abinda zai rabani da wannan baiwar taka Allah na tuba”. A hankali Sulaiman yace. “Amin amman dan Allah da Manzonsa kasa a sakesu kaji ka yafe musu Mom Sa'ad tana ban tausayi”. Kwaffa yayi haɗe da cewa.
"Dama Abba yace ƙarshen wata kaje ai, dan haka kai zaka wuce da motata Kano Sadiq ya kaima taka Gombe in kunje Aunty Rashida Da Saddiqa da Mrs Salim zaka ɗauka a baya Sadiq ɗin a gefe ya tayaka tuƙi na sanka baka son dogon tafiya, ko Kano zakaje sai kabi Flight zuwa abuja daga Abuja ka tabo kano”.
Numfashi ya fesar fahimtar akwai abinda mgnar ke nufi yace.
"Kai yaushe zaku wuce?”.
Yana ɗan jijjiga sawunshi kaɗan-kaɗan kamar wanda yaro ke kan cinyarsa a hankali yace.
"Flights zamubi zuwa Abuja daga nan zamu bi na Kano Angle bata da lfy iskar mota yasata mura”. Kwaffa Sulaiman yayi yace.
"Nima dai na kusa yin auren nan”.
Yana kallon shi yace.
"Naga ai sai wani irin kallon maita kake tayiwa wata yarinya me ma sunanta”. Yana kai goran Admiral bakinsa yace....
By
*GARKUWAR MARUBUTA**SAƘAR MAKAFI*
Page 85
Na
*Aysha Aliyu Garkuwa*