Sashe 34
Sakar Makafi Part 2 Complete Hausa Novel · about 7 min read
By
*GARKUWAR MARUBUUTA**SAƘAR MAKAFI*
Page 59
Na
*Aysha Aliyu Garkuwa*
Yah Mujahid ya nufi ƙauyen Wudil wurin sabon bokansa da yace su Fariyda na dawowa ya zo zai bashi kollin idonsa idonta.
Tun sassafe da ya tafi bai dawoba sai wuraren sha biyu ya baro can bayan ya ce masa sai bayan kwana biyu ya dawo ya amshi kollin.
Parlour shiru sai kamshi da sanyin AC, hirarsu take jiyowa a parlour Abba bisa alamu Aunty Amina ma tazo, baki ta ɗan taɓe ta zauna kan kujerar dinnin table,
ƙamshin turarensa daya cika mata hanci ne ya tabbatar mata bai daɗe da barin wurinba, plate and bowls da spoons dake kan Dinnin table ne ya bata tabbacin yanzu suka gama breakfast bisa dukkan alamu da Sulaiman da Salim sukaci abincin sabida ganin komai uku uku a kan Dinnin table ɗin gafen plate ɗinsa da yake tare da tea cups guda biyu ta harara.
Shigowar Goggo Dada ne yasata fitowa cikin parlour.
“A'a Fariyda kin fito ne?”. Tana gyaɗa mata kai tace. “Eh Goggo Dada baku tasheni ba na tayaku aiki”.
Inda take ta matso tana jawo plate ta fara zuba mata abinci tace.
“Ai muma ba abinda mukayi tu ƙarfe takwas Amina ta iso da komai da zamu buƙata shiyasa ko kitchen ɗin ma bamu shiga ba, muma yanzu mukayi kari a wurin Abba, Mahmoud da Salim da Sulaiman suma yanzu suka bar nan, Samira ta leƙa zata kiraki tace ta samu kin shiga wanka”. Ta ƙare maganar tana tura mata, abincin da ta saka mata haɗi da jawo mug ta haɗa mata tea.
Bayan ta gama tsakuran ɗan abinda taci, Samira data shigo yanzu ta tattare wurin.
Amina data shigo parlour ta zubawa ido jin tana faɗin. “Wannan ƙyalli da kyau haka, ai dole ƙanina yayi mubaya'a, kauda kai tayi tana faɗin.
“Ina Ummi”. Sai kuma suka dawo tsakiyar parlour jin Ummi na cewa.
“Gani nan ɗiyata”. Sallamar su Mimi ne da Matar Bappa Sani yasa Fariyda miƙewa gami da yi musu iso, ranar ma dai haka suka wuni cikin baƙi, yan uwa da abokan arziƙi masu yi musu barka da dawo da farar jinya da duba Zaid da ya murmure ya ƙara girma wanda su da basuma lura da haka sai da ake ta faɗane suka lura da girma da yaran sukayi.
Bayan sallan isha Goggo Dada ta gama shirya su Zaid cikin tattausan kayan baccinsu.
Amina dake gyara mayafinta ta ɗan jawo hannun Fariyda tare da cewa.
"Muje in rakaki side ɗinku kiga yadda muka sha hidimar gyara muku Side ɗinku, mijinki dai ɗan ƙwatsale da ba'a masa gwaninta yace ai bai saniba”. Tayi mgnar dan son maida Fariyda ɗakinta dan ganin alamunta na zama a nan.
Hafiza ɗauki Zaid mu tafi”. A hankali ta miƙe jin Goggo Dada na cewa.
"To Fariyda Saida safe ko, kar kice zaki sauƙo da sassafe dan yin aiki ki bari ki huta gajiyar hanya kafin ki fara sauƙowa”. Hand bang ɗinta ta ɗauka tare da bin bayan Amina dake jan hannunta, a parlour suka samu Ummi Sulaiman da Hafiz.
Cikin kulawa Ummi tace.
“Sai da safe ko Fariyda kar ki ce zaki sauƙo da sassafe”. Cikin sanyi tace.
"To Ummi waye zai yi aikin”.
Tana murmushi tace.
“Ga Samira ga mamanta ga Goggo Dada duk bamu isaba sai kin fito kin wahala kiji da sarakan rigimar nan ma ai aikine”. Ɗan kwantar da kai tayi tace.
“Ummi yanzu fa sun girma, na yayesu mafa tun lokacin da muka tafi”. Cikin mmki suke kallonta.
Sai kuma Amina ta jata tana faɗin.
"Amman dai Mahmoud bai sani bako”. Kai ta gyaɗa mata kana suka fita.
Suna shiga parlour Huzaifa na fitowa Hafiza tace.
“Huzy Uncle Mahmoud na ji da kai wlh yafi sonka akanmu”. Kwaɓe Huzaifa yayi cikin haki da yarfe zufar data tsatstsafo mishi yace.
“Ke nimafa motsa jiki ya sani wai yaga ƙara zama ƙato nayi, baki ganni a jiƙeba”. Dariya Amina tayi tare da cewa.
“Ai kuwa ya kyauta dan na lura kamar iska ake hura maka sai kaci ka kwanta kayi ta danna waya kana ƙara zama ƙato”. Baki ya tura yayi waje su kuma sukayi ciki.
Numfashi mai sanyi ta fesar saboda sanyi da ƙamshin parlour daya sakar mata kasala, bedroom ɗinta suka wuce komai yana nan ƙal-ƙal sai ƙelli da ƙamshi kwantar dasu Zaid sukayi kana suka juya suka tafi, suna fita ta shige bathroom tayi wanka da shirin bacci itama ta kwanta.
Washe gari da safe kamar jiya kafin ta fitoma tuni sun gama kari sun fita dan nacin Salim na Mahmoud yaje yaga gidansa.
A parlour Salim din suka zauna, Salma nata ta hidimar kawo musu abubuwan taɓawa na amare.
Tunda suka gaisa bai ƙara cewa mata ko ƙalaba gwara Sulaiman yayi mata sannu da aiki.
“Muje ciki ko”. Salim ya faɗa tare da miƙewa tsaye, kallonsa yayi a nitse yace.
“Wanne cikin kuma”.
Yana juyowa yace.
“Kaga side ɗin amarya mana”. Hanyar fita ya nufa yana faɗin.
“Baka da hankali ni ai gidanka nazo gani da Allah sanya alkhairi ba ganin ɗakin matarka ba”.
Sulaiman yace.
“A ni dai mun gani”. Yana fita yace.
“Wannan ba wani abu ai in kafin ta tare ne, yanzu kuma side ɗinta sirrintane”. Daga nan ya fice snackers box ɗin Salim ya ɗauko musu yana gyara marfinsa ya ajiye kan cinyar Sulaiman, shi kuwa Mahmoud yana maida marfin motar yace.
"Naji daɗin kasancewarka kusa damu, Allah ya baku zaman lfy dan Allah ka riƙe girmanka ka daina rawan kai kar ka nuna maitarka a fili kasa ta rainamu.” dariya mai sauti Salim yayi tare da cewa.
“Hmmm sai dai kar a kuma rawan kai ai harda na ƙafa ma yi nakeyi kai dai kaje can ka karata da kafiyarka”.
Ya ƙare maganar yana rufe musu marfin motar.
"Banza mara kai”. Mahmoud ya faɗa tare da jan motar suka fita, ba ko gida ɗaya a tsakaninsu da gidan Abba sai hanya data gifta musu.
A gida kuwa Ranar Matar Yah Faooq da Murtala suma suka zo.
Washe gari da safe zaune suke a parlour Ummi dukansu.
“Yau kwana uku kenan Amina bata leƙo muba”. Goggo Dada ta faɗa.
“Huzaifa da kullum nan yake wuni ne yace.
"Dama tace sai tayi hutun kwana biyar zata zo, Daddyn yace ya gaji da zirga-zirganta”. Ummi na kallon Fariyda data miƙe tsaye dan shigowar Raihana da Zainab tace.
“Daga ina haka”. Bayan sun gaida Ummi da Goggo Dada, Zainab tace.
“Daga gida Baba Malam ne yace wai muzo mu ɗaukar masa su Zaid mu kaisu ya gansu”. Murmurshi Ummi tayi tana kallon Fariyda dake cewa. “Wato ma Malam su Zaid ya nema ni bai nemeni ba”. Goggo tace.
"Ato ai abun cikin kwan yafi kwan daɗi.” Zainab tace.
"Abbana ma yana can wurin Baba Malam ɗin yace yana jiranmu sai ya gansu zai tafi”.
Ummi na murmushi ta miƙe ta nufi parlour Abba tana cewa.
“Bari in ɗaukosu suna wurin Abba shima sune abokan hira.
Jim kaɗan da shigarta ta fito tare dasu.
Tana faɗin.
"Ashe ma Malam ɗin ya kira ya faɗa masa zakuzo a tsammishi su.”
Suna amsarsu suka miƙe suka tafi.
Bayan idar da sallan Isha ya shigo parlour Ummi yana kiransu.
“Zaid Zaitoon ina kuke”.
Sai kuma ya kalli Goggo Dada yace.
"Ko sunyi bacci ne?”. Ummi da ta shigo riƙe da carbi a hannunta tace.
“A'a yau wuni suka kai gidan Malam”. Kwaɓe fuska ya ɗanyi yace.
"Ummi ba'a gaya min ba a kaisu anguwa har su wuni”.
Goggo Dada tace.
“To yaran da an yayesu ai ko kwana zasu iya kwana ma a can basu da damu kakansu nefa ya roƙi Abba ya turo a kai mashi su”. A hankali ya juya ba tare da yace komai ba.
Yana buɗe ƙofar Sadiq da Raihana na shigowa amsar su Zaid ɗin yayi basu Jimaba su Raihana suka koma.
Washe gari.
yau kwanansu shida cib da dawowa.
Tunda suka dawo bata ƙara ganinshi ba ko sau ɗaya, mafi akasarin kwanki da lokata sai ya fita take shogowa.