← Book details Sakar Makafi Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 2 OF 95

Sashe 2

Sakar Makafi Part 2 Complete Hausa Novel · about 4 min read

Washe gari da safe waya take yi da Ummi,
Murmushin Ummi tayi tana kallon jikokin nata.
“Fariyda ina Appiy nasu suke ta kiransa, ni yau kwana uku kenan banyi magna da shiba”. Cikin mmki take kallon Ummi sai kuma ta ɗan kalli akwatinsa zuciyar ta na harbawa tace.
"Ummi to ki kira layinsa mana, ya bar wayar Yah Amin ɗin a parlour ne”. Tana ɗan kallon Amina data matso Ummi tace.
"Ai layinsa ma baya tafiya Fariyda”. Sai kuma tayi saurin kallon Amina da tace.
“Nima nayi ta kiransa baya shiga, kin san dama shi WhatsApp kuma yana daɗewa bai leƙaba”. A hankali ta sauƙe nannauyan ajiyan zuciya cikin sanyi tace.
“Hummmm”. Daga nan bata iya ƙara cewa komai ba, baƙin da suka shigo Parlour Ummin ne yasa suka katse kiran.
Tunda ta idar da sallan magrib take zaune bisa sallayar yau dare na huɗu kenan da tafiyarsa. Zaid daya matso bakin gadon yana riƙo wuyanta da fadin Appiy. Appiy. Ammiy Appiy, Zaitoon dake kwance a ƙasa a gabanta itama ta kama Appiy. Cikin sanyi murya ido cike da tsoro tace.
"Na shiga uku na”. Wayarta ta jawo tare da kunna Wi-Fi Amina ta kira, cikin sa'a kuwa bugu ɗaya ta ɗaga. Fariyda ya dai”. Ta tambaya tana kallon yadda take ta kiciniya da yaran, da suke ta kuka da kiran Appiy, cikin sanyi tace. “Aunty Amina nifa ina jin tsoro”. Da sauri tace.
“Tsoro kuma Fariyda to ina Mahmoud ɗin”. Kai ta sunkuyar tare da cewa.
“Yau kwana uku fa cib ban ganshi ba, gashi har yanzu bai dawoba kuma kunce bakwa samunsa a waya”. Cikin tsaro Amina tace.
“Ban ganeba Fariyda kiyi min bayani”. Cikin sanyi tace.
“Faɗa mukayi kuma ya fita yana kuka, har yanzu kuma bai dawoba, gasu Zaid nata min kuka suna kiransa, kuma bai dawoba yauma”. Ta dire mgnar cikin rawan murya ido na cike da ƙwalla”. Da sauri Amina tace.
“innalillahi bari in tambayi Abba ko sunyi waya dashi, dan har su Salim ɗazu da suka zo ɗaukan abinci sunce basa samunsa, ke kuma ki kira driver ku kiji ko akwai inda ya kaishi”. Daga nan ta katse kiran.
A parlour Abba ta samesu bisa alamu yanzu ya dawo sallan isha.
Ummi da Goggo Dada sai Sulaiman da tarin fufun goro a gefe da alamu na ɗaurin auren Salim ɗin ne gobe jumma'a. Shiru Abba yayi yana sauraron jawabin ta, kai ya jinjina cikin shiga tunani yace. Baban nawane yayi fushi ya bar gidan, yau kwana uku, hmmmm to lallai kuwa babban faɗane da yafi duk faɗa da sukeyi, fushi har ya bar gidan ya bar su Zaid”. Cikin tsoro Goggo Dada tace.
"To me ya haɗasu?”. Kai Amina ta jujjuya alamar bata sani ba.
Ummi kuwa ajiyan zuciya mai nauyi ta sauƙe tare da cewa.
“Lallai koma menene abu mai zafi ta gaya mishi ko tayi masa, irin zafinda bazai iya komaiba sai hawaye Mahmoud dai yayi hawaye kan abu lallai lamarin babbane kuma lamirine mai ƙara ɓata komai a cikin zamansu, abinda muke fata bazai taɓa samuwa ba, na san waye Mahmoud da irin zuciyarsa duk abinda ya sashi kuka to wlh ya barranta dashi kenan”. Da sauri Sulaiman dake ta gwada kiransa baya shaga yace.
"Ni matsalata ina yake wanne hali yake ciki? Gashi har yanzu layinsa baya tafiya”. Kai Abba ya jinjina tare da cewa.
“Kada ku damu, duk inda Mahmoud yake a doron duniya baya wuce adadin kwana uku duk rintsin halin da yake ciki zai nemeni zamuyi magna, in dai yau kwana uku kenan in sha Allah zuwa safiya zai kirani”. Daga nan yace suje suyi harkokin gabansu.
Suna fita ya miƙe ya shiga bedroom ɗinsa, alwalar kwanciya yayi tare da yin nafila kana ya ɗau Qur'ani ya fara bita.
Hasken da wayarsa keyi ne yasa yayi saurin kai ƙarshen suratul yaseen da yake, ya jawo wayar.
Ganin kiran Mahmoud yasashi amsa kiran da sauri, cikin sauƙe numfashi yake amsa gaisuwar Mahmoud ɗin da tambayar Ummi da Goggo Dada
Gyara zama Abba yayi saboda jin Mahmoud ɗin yayi shiru, cikin sanyi yace.
"Babana kayi shiru, ko bacci kakeji”. Cikin sanyi yace
"A'a Abba ina jinka”. Cikin fahimta irin ta uba da ɗansa da yayi gadon halinsa yace.
"Nima ina jinki?”.Cikin sanyin muryar can ƙasan maƙoshinsa yace.
“Abba tambaya ce nake so inyi kuma na rasa wanda zan tambaya, dama ace da Yah Amin na raye shi zan tambaya”. Cikin sauri da rauni Abba yace.
“Tambaye ni Mahmoud faɗi ina jinka duk abinda Aminullah zai maka fiye dashi zan maka ai”.
Cikin ƙoƙarin danne rawar da muryarsa keyi yace.
“Abba wai menene ke sa a cewa mutum nakasashshe wanda ba cikekken mutum”...........

By
*GARKUWAR MARUBUTA**SAƘAR MAKAFI*
Page 45
Na
*Aysha Aliyu Garkuwa*
Chapter 2 · 0% Book details