← Book details Sakar Makafi Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 32 OF 95

Sashe 32

Sakar Makafi Part 2 Complete Hausa Novel · about 4 min read

shafa kafaɗarta tare da ɗan janyeta daga jikinta kallon sama da ƙasa tayi mata cikin mmkin ganin wani irin mashahurin kyau da sheƙi mai haɗe da ƙyallin da ɗiyartata keyi war wani yellow ta surka a farinta, tana ƙara tureta ganin zata kuma rungumata tace. “Ke bakya girma fa to me kuma na kukan”. Sai kuma ta kalli Dr Nasir da ya bawa su Mahmoud hannu tare da yi musu iso tana gyara mayafin jikinta tace. “Mahmoud Barka da dawo ku isa ciki yanzu Malam ya dawo masallaci”. Cikin girmamawa Mahmoud yace. “Mami barka da rana”. Tana nuna musu hanya tace. “Ku isa”. Suna gaba tana biye dasu a baya riƙe da hannun Fariyda dataƙi saketa. Da sauri Baba Malam ya miƙe tsaye cikin jin dadi mai bayyana akan fuskarsa ya warewa Mahmoud ɗin hannu cike da kunya da jin nauyi ya iso gareshi haɗesu yayi dasu Zaid ya rungume tare da cewa. “Kai Alhamdulillah Mahmoud nayi farin cikin ganin ku”. Sai kuma ya sake shi ya koma ya zauna bayan ya amshi Zaid. Mami kuwa da Aunty Amarya da Dr Nasir ido suka zubawa Malam ɗin da soyayyarsa akan Mahmoud da su Zaitoon a fili ya bayyana farin cikin da ya basu mmki. Gefensa ya nuna Mahmoud ɗin da Sulaiman, sai kuma ya kalli Fariyda da Aunty Amarya ta rungumeta tana ce mata “Daga ina haka yan uwanki duk yau suna gidanki”. Cikin muryar kukan jin dadi tace. "Daga Airport nan muka fara zuwa”. Cikin so Malam yace. "Zo nan mana Mamana”. Da sauri ta sake Aunty Amarya gabanshi ta durƙusa gafen Mahmoud ɗin hannun sa yasa ya jawo kanta ya ɗaura kan guiwowinsa yana shafawa yace. “Barka da dawowa Mamana Allah yayi muku al'barka dake da yaranki da mijinki dama mu baki ɗaya”. Da Amin suka amsa baki ɗayansu sai kuma suka kalli Mami dake cewa. “Mahmoud barka da dawowa lfy, Alhamdulillah anyi farar jinya ga yadda Zaid ya murje ya zama ƙato abinsa”. Yana kallon Zaid ɗin dake ta miƙo masa hannu alamun zai dawo wurinsa yace. "Mukuma bama ganin ya girma fa Mami”. Aunty Amarya tace. "Saboda kuna tare dashi ne”. Mami ta miƙa masa hannu alamun ya bata Zaitoon da sauri ya miƙa mata ita yana faɗin. “Zaitoon je ki gaida Mami ko”. Da ɗan sassarfa ta faɗa jikin Mami dariya sukayi ganin shima Zaid ya tafi wurin Mami. “Baku isa gida bako Mahmoud?”. Malam ya tambaya cikin kulawa. Yana ɗan yin ƙasa da kai yace. “Eh Malam ta nan muka fara dan munyi miss addu'arka”. Yana shafa kanshi yace. “Ai duk inada kuke kuna tare da addu'a ta, Asma'u a kawo musu abinci”. Tana ɗan gyara zama ta kalleshi a fakaice yo ai duk wannan munafurcin gaisuwar da nuna shi ba Allah ne iya karta a nan ne ko ruwan gidanma ya taɓa shane bare abinci. Shi kuwa Mahmoud cikin girmamawa ya kalli Mami da ta ɗauko tray wormas ɗin da ta shiryawa Malam ɗin lunch a hankali yace. "Mami Alhamdulillah munyi lunch a Lagos ma”. Tana kallon Sulaiman da Malam ke ce masa. “Sulaimanu yanzu fa saura kai, yaushe zamu yi maka aure kada lokacin ya ƙure”. Cikin sanyi Sulaiman yace. “Malam ai ba wacce ke sona shiyasa”. Dariya sukayi baki ɗayansu sai kuma duk suka kalli Malam ɗin dake cewa. “To ba matsala zan sama maka mai sonka, yanzu dai Mahmoud ku isa gida nasan Abbanka yana nan ya zaƙu ya ganku, Nasir samusu abincin su tafi dashi”. Daga nan duk suka fito, suna shiga mota kiran Amina na shiga wayar Fariyda. "Wai dan Allah ina kuka tsaya ne? Su Hafiz sun inso tun tuni ba ku ba labarinku, wata nawa kuna tare har yanzu baku gaji da juna bane dan naga alamun wani zango kuke son yadawa a hotel kuma ko”. Amina ta faɗa tana kallon Aunty Saddiqa dake sa turaren wuta a parlour, da sauri sukayi dariya jin tana faɗin. "Allah ya kiyaye, gidafa muka zo wurin Malam gamu mun fito yanzu”. Murmushin Aunty Saddiqa tayi tana kallon Sadiya matar Dr Nasir ta gama karantunta a Misra ta dawo tace. “Allah sarki bawan Allah kamar yasan Malam yayi kewarku cewa yake har mafarkinku yake yi, ya kyauta da ya fara kaiki can, Allah ya kawoku lfy”. Amin tace tana kallon layin unguwar tasu suna isa bakin gate ɗin gidan kiran Faisal na shigowa wayar Yah Amin, yana kallon number har kiran ya katse bai ɗaukaba sai kuma ya kalli wayarsa ganin sakon ne yasa ya ɗan buɗe saƙo Idaya ce. “Barka da dawo, ka huta gajia zanzo har gida yima sannu da hanya da duba jikin Zaid”. Shine abinda ta rubuta mishi wanda ya bashi tabbacin tana sane da duk motsinsa da kuma tabbacin tana cikin kano lip ɗinshi na ƙasa ya datse da karfi sai kuma ya kalli kiran Faisal daya kuma shigowa a kufule ya amsa kiran. Juyowa yayi yana mata kallon da yasata yin ƙasa da kanta, kusan 3 minute wayar na maƙale a kunensa kuma bai ce ko ƙalaba bai kuma katse kiranba sai kuma duk suka kalleshi dai-dai lokacin da suka kutsa kai cikin gidan jin yadda ya......
Chapter 32 · 0% Book details