← Book details Sakar Makafi Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 4 OF 95

Sashe 4

Sakar Makafi Part 2 Complete Hausa Novel · about 5 min read

Shiru Abba yayi ya bada hankalinsa da nitsuwarsa duk ya maida kan Ummi da da take labarta mishi irin zaman da Mahmoud yakeyi da Fariyda tun zamanin da take tare da Aminullah da irin rashin shirinsu da saɓanin da suke samu, har ma da yadda suke zaman bayan an musu aure jin tayi shirune alamar ta dire mgnar tatane, numfashi mai nauyi ya fesar tare da kallon Ummi yace.
“Kina nufin ko abincinta bai taɓa ciba, baya mata mgna, baya shiga ɗakinta,”. Cikin sanyi tace. “Hmmm wannan ma ya isa ya tabbatar da cewa Mahmoud fa bai samu lafiya ba kamar yadda Aminullah yayi tsammanin har ya gaya maka, sam babu mace a rayuwar Mahmoud kai ka san waye Mahmoud da ace lafiyarsa ta samu da tuni labarin ya sauya dan tabbas da yace ayi mishi aure dan ko yana sonta in dai kamar da zai dawo mace ɗaya bazata iya da shiba, wata ƙil ma da yanzu yayi mata biyu a dai halin ɗanka da halittarsa da ka sani, ka kuma ji da bakinsa ya faɗa ma irin kalaman da Fariyda ta faɗa masa waɗanda sune ƙarshen tabbacin har yanzu bashi da lfy zaman aure da ita kuma cutarwa ne a shari'a”. Cikin tsaida matsaya Abba yace.
“Dole mu raba auren nan kamar yadda muka haɗashi dani da Malam Ibrahim, In sha Allah in sun dawo zan sashi ya rubuta mata takardarta”. Cikin sanyi jiki Ummi tace. “Duk da bana son rabuwa da Fariyda amman dole in haƙura tunda ɗana baida lfy mai lfyar kuma Allah ya ɗaukesa, tabbas kam nayi rashin surka mai wuyar samun irinta a wannan zamanin ta zame min kamar ƴata ta cikina, koda Mahmoud nada lfy samun irin Fariyda a wannan zamanin da matan ƴaƴa suka tsani iyayen mazansu da wuya”. Ta ƙare maganar hawaye na tsilalowa mata.
Ahmedabad.
Da sauri ta nufi parlour ba tare da ta ɗaure kantaba saboda jin kukan Zaitoon.
A hankali ta tsuguna kasa da ita ganin cikin bacci tayi ihun tofi ta farayi mata, sai kuma tayi saurin juyowa saboda jin an buɗe ƙofar parlour.
Ya maida ƙofar ya rufe tare da juyowa ya nufi tsakiyar parlour dake cike da haske wutan da duk ta kunnasu dan tsoro.
Ido cikin ido sukayi dashi, janye idanta tayi daga cikin nasa tayi ƙasa da kanta.
Sama da ƙasa ya kalleta fuska a haɗe ya ƙaraso cikin parlour, riƙe da ɗan madaidaicin travelling box sai briefcase ɗinsa dake kafaɗarsa.
A hankali ta ɗan matsa baya kaɗan tare da cewa.
“Ina yini”. Ko ƙala bai ce mata ba sai idon daya kafeta dashi, jin bai amsa bane yasa ta ɗago kanta ta kalleshi ganin irin kallon da yake mata ne yasa tayi saurin juyawa da nufin barin wurin.
Da sauri ta rumtse idonta saboda jin yadda ya damƙi jelar gashi kanta da bata kitseba ya jawota baya kusa dashi murya a daƙile yace.
“Kayana? turarena? Takalmina”.
Da sauri ta kai hannunta kan gashinta ta fara ja, gami da faɗin.
"Wayyo Allah kaina zai tsinke fa”. juyota yayi gabansa suna fuskantar juna murya a kausashe yace.
"Waya baki izinin taɓa min akwatina? Ni mate ɗinki ne da zaki samin kayana fa? Don kinga kinsa takalmina banyi mgnaba na bar miki su shine har zaki buɗe min akwati kiyi min sata”. Da sauri ta fara jujjuya masa kai ido cike da hawaye dan zafin jan gashinta da yake ƙara ja sabida suɓalewa da yakeyi dan sulɓinsa.
“Wato ke burinki dai in mutu kamar yadda Yah Amin na ya mutu, nima shine burinko to sai ki bari sai na mutum kafin ki taɓa min abina amman ina raye kam baki isaba”. Tana yarfa hannunta cikin rawan murya tace.
"Wayyo Allah kaina kayi haƙuri dan Allah kaina zai tsinke”. Cikin zare mata manyan idanunsa yace.
“Meyasa zaki samin kayana”. Ido na cikowa da kwalla tace.
“Kaya nane yayi datti, mai wanki baizo ya kwasa ba”.
Yana kallon fuskarta yace.
“Ke dama kin damu da ayi miki wanki ne dattin yana damunki ne, akan me zaki samin turarena”
Da sauri tace.
“Ni dai bansa turarenka ba, wanda Sa'ad ya kawo min na saka sai dai in na jikin rigar kaji”. Da sauri ta rumtse idonta da karfi saboda ganin yadda yake kusanto da kanshi kanta, numfashi mai ƙarfi ta sauƙe jin hancinsa kan fatar wuyanta.
Buɗe idon ta kumayi da sauri sabida jin yadda ya cukuikuye gashinta da karfi haɗi da cewa.
“Ƙarya kikeyi wanna turarenane, akan me zaki fesa min turare”. Cikin ruɗewa murya na rawa tayi rau-rau da ido tace.
"To ya zanyi kace min kar in sake saka turaren da Sa'ad ya kawo min warin ƴan bori yakeyi, ni kuma turarena ya ƙare shi yasa na fesa naka, kuma shima yanzune kaɗai na saka fa”.
Bakin rigar ya riƙo tare da cewa.
“Cire min kayana tunda ba ke kika saya min ba, tuɓe”.
Ya ƙare maganar tare da jan rigar sama da sauri tasa hannunta duka biyu ta fara kiciniyar ƙwace ƙasan rigar da ya riƙo ɗin tanayi tana haɗawa da magiya, ni ka barni zanje in cire maka shi, ko ta kanta bai biba hannunsa yasa ya janye rigar, da sauri ta kuma rarumo ƙasan rigar duka ta haɗe ta cukuikuye ta lanƙwaɓe kai tuni ido ya raina fata ganin yadda ya tsareta ya hanata gaba ya hanata baya cikin daƙilelliyar murya yace.
“Cire min kayana ko in ɓalla miki ƙafa”. Tana ƙara matsawa ganin ya sunkuyo tace.
“Ba komai fa a jikina”. Kafaɗa ya ɗaga tare da buɗe hannu alamun ko a jikinsa kana ya ɗan sunkuyo rigar ya kamo daga ƙasa yayi sama dashi, da ƙarfi ta rumtse idonta da tuni suke zubda ƙwallan tare jan wani irin hautsinenne numfashi lokacin da taji ya.........

By
*GARKUWAR MARUBUTA**SAƘAR MAKAFI*
Page 46
Na
*Aysha Aliyu Garkuwa*
Chapter 4 · 0% Book details