Sashe 25
Sakar Makafi Part 2 Complete Hausa Novel · about 4 min read
ya ɗauki kiran iyayensa ba yace. “Abba ina sonta wlh ina son Fariyda irin son da nima ban san adadinsa ba, bana son rasata domin itace kaɗai matar da nakeji zan iya rayuwa da ita, ina kiran layinshi baya picking call na ɗaya number da ta bani kuma ko na kira baya shiga sai WhatsApp da nayi magna yafi sau goma ba amsa, kawai dai muje Kano nan tunda ganesu bazaiyi wuyaba da sunan Al'ummah zan gano inda yake”. Numfashi mai sanyi Mom da son da Sa'ad ɗin ke yiwa Fariyda yasata jin ƙaunar ta tamkar ranta tace. “Nima ina sonta Sa'ad kuma in sha Allah sai ka sameta bi'izinillahi ta ala burinka zai cika domin inayi maka addu'a, amman gskyar Fariyda da take kinyin mgna da kai kuyi ta istigfari na mgna da kayi da ita lokacin da kaje na tunda da aurenta ka daure mu kara sati uku zuwa wata ɗaya muga in har bai kiraka ba, kuma ba amsa a WhatsApp sai muje Kano”. Cikin gamsuwa da hakan Alaji Usman ɗin yace. "Yauwa hakan shi yafi”. Istanbul Tunda ya fita bai dawo ba, itama bata sa ran dawowarsa ba dan tunda suka zo Istanbul in ba jiyaba bai kwana anan ba kai ko awa biyu ma baiyi ba. Shi kuwa Mahmoud tunda ya fita bai zauna ba, aikin haɗa kan kayyakinsu da yayi kwanaki yana duba aikin da ake yi musu da hada kayansu kafin ciwon yaci ƙarfinsa ya kwantar dashi, komai ya haɗu kama daga carperts darduma blankets da labulayen yan gaske da shi ya bada samfurin ko wanne aka buga musu, Alhamdulillah kuwa ko wanne Company sun gama hada dukkan abin da ya nema har an fara parking na kayyakin ana libgawa a manyan kontenoni dake bakin tekun da sakasu cikin jirgin ruwa zuwa Lagos. Gab da magrib ya baro bakin tekun dan tirelan takalma da rigunan da akayi musu ya iso har an gama sasu a kontenarsu an sa a jirgin ruwan har ta kama hanya ne yasa ya fito cikin gamsuwa da kammala komai da yake da nufin yi a Istanbul ɗin gidansu ya wuce kai tsaye . Bayan sallan isha kwance take tana lulluɓe da duvet ɗin iya kantane kaɗai a waje waya da ke kan kunnenta ta gyara riƙewa tana kallon su Zaid da keta harkokinsu a kan gadonsu. "Nima ban san yaushe zamu dawoba Yah Mujahid amman in sha Allah mun kusa”. Ta faɗa cikin jin gamsuwa da magna dashi a tudu biyu ɗan uwa kuma miji a gare ta in Allah yasa sun koma. Kai ta ɗan ɗago jin an tura ƙofar ɗakin an shigo. Wurin su Zaid dake ta ɗaga hannu suna haɗa bakin faɗin. "Owo Appiy! Appiy!!”. Ya nufa tare da buɗe musu hannu rungumesu yayi a jikinsa yana kissing neck ɗinsu dariyar da sukeyi ne yasa ta ɗan kallesu ta gefen ido, sanye yake cikin tattausar Turkish jallabiya maroon color mai masifar kyau da ƙelli tayi cib da jikinsa hulɗar dake haɗe da jallabiyar na kwance kan kafaɗunsa sai takalmi sauci milk color da hular saƙa shima milk color da yasa a kansa, hakama Scarf din wuyansa shima milk ne, ƙamshi yake zubawa tamkar fure flower, baki ta taɓe ta maida hankalinta kan wayar da take yi murya can ƙasa tace. “Yah Mujahid nima nayi missing ɗinkufa, ina son ganin Mamy na dasu Ummi”. Ɗauke kunnensa yayi daga jin maganar da take yi ɗin, ya ajiye su Zaid ɗin bakin gadon travelling luggage dinsa dake can gefe ya kalla komai a kimtse yake wuri ɗaya sai jakar dake gefe na kayan da yasa Arda ya kawo musu ya bada a Reception aka kawo mata, wayarshi ya zaro time ya ɗan duba takwas harda kwata na dare. Knocking ɗin da ake yi ne yashi juyawa dan zuwa buɗe ƙofar. "To Yah Mujahid karka manta fa”. Ta faɗa cikin muryar dake nuna jin dadi. Ko ta inda take bai kuma kai idonsa ba, tray abincin da aka kawo musu ya amsa. Kan table ɗin dake gaban kujera ya ajiye tare da miƙawa su Zaid hannu da gudu suka zo. Su ya fara bawa saida sukaci ya goge musu baki sannan ya jawo plate ɗin fruits, ya fara sha. Ita kuwa Fariyda a hankali ta juya ɗaya gefen taci gaba da wayarta. Bayan kamar 46 minute ta juyo da kanta tsaye ta hangoshi rungume dasu a bakin ƙofar, baki ta ɗan taɓe bayan ya fita, plate ɗin fruits da ya rage ta jawo ta fara shan strawberry and Apple da ya rage, tana cikin sha ne taji ana Knocking tasan ba shi bane dan in shine sai dai ya shigo kawai dan shima da card a hannunsa cikin mamaki ta zuba mishi ido tare da cewa. “A...........