← Book details Sakar Makafi Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 24 OF 95

Sashe 24

Sakar Makafi Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read

“Gani cinyeni nima abincine ai tunda ke mayyace da kika san kina jin yunwa me ya hanaki amsar abinci a gidan Yah Saleh. Can ma Hanzade da mukaje me ya hanaki kici duk abinda kike so kikayi ta zuƙan ruwan zafi kamar mai cutar sanyi, sai yanzu da muka dawo zan kwanta inyi baccin da kika hananiyi jiya kice min zakici abinci yunwa kikeji cikinni na ciwo, to gani zo ki cinyeni.” ido cike da kwalla tace. "Masifa take min tana min gorin Yah Amin ya rasu, shiyasa bazan iya ci ba, a Hanzade Terrace kuma sanyine ya hanani ci.” a kufule yace. "Eh to yanzu ai gani ga zafi sai kizo ki cinyeni zaki fi samun kwanciyar hankali”. A hankali ta juya ta kwanta ta kife kanta a pillow gami da jawo duvet ta rufe jikinta tana mai sakin kukan cikin sanyin da yunwa a haka bacci ya ɗan saceta. A hankali ta yunƙuro daga kwanciyar tana rumtse idonta da ƙarfi gami da fara jan duvet ɗin jiki na rawa, ta farka a firgitacin daga bacci jin ana ajan duvet ɗin, Ɗan tsaki yaja ya sunkuyo hannunsa ɗaya dafe da kan gadon ɗaya hannun da ya kai yana jan duvet ɗin dan tada ita yaci gaba ja, Cikin sanyin bacci tasa ihun gami da faɗin. “Innalillahi wayyo Allah na Appiy Ketra Appiy ka taimakeni”. Tana magnar ne cikin magagin bacci da rawan jiki cike da ɗimuwa da tsoron karen da yasata gigicewa, shiru yayi cikin duhun da baya iya ganinta. tsaki yaja fahimtar a gigice take bata da niyar yin shiru ne yasa hannunsa ya fizgo duvet ɗin. “Yah salam”. Ya faɗa saboda jin yadda ta fara buge-bugen neman ma ɓoya da auna masa kira a jere a jere da magiyar neman taimako. “Wayyo Allah na Appiy Ketra ka taimakeni Appiy”. Zama yayi kan gadon ya miƙa hannunsa ya fara lolubo ta inda take, da ƙarfi ya fizgota kusa dashi kafaɗunta ya riƙe da hannunsa duka biyu yace. "Ke zan tsinka miki marifa in baki rufe min bakiba”. Ai bata ma jishi ba bare ta sahirta sai fizgewa take da yunƙurin ƙwace wa. “Da ƙarfi ya fizgota sabida juyawar da tayi tana tattaro duvet, kanshi ta faɗo da ƙarfi. “Ke nine karenne ko me kike nufi?”. Da ƙarfi ta rungumeshi ƙamƙam cikin haki da rawan jiki take ƙara ƙwaƙumeshi. Shiru yayi tamkar ba numfashi a jikinsa, yana jin yadda jikinta ke tsuma da bugun zuciyarta dake harbawa da ƙarfi-ƙarfi. Ita kuwa Fariyda har lau tana ƙwaƙume dashi gam, a hankali ya fara janye jinsa sai kuma ya miƙe tsaye ya ɗan matsa gefen gadon da ita a jikinsa jin yadda ta ƙara shaƙo wuyansa ta maƙaleshi, hannunsa yasa ya kunna wutan ɗakin fuskarta ya ɗan leƙa idonta dake rufe gam-gam ya ɗan kalla sai kuma ya fara magna cikin shakeƙƙiyar muryarsa da ta shaƙe ta maƙale wuyansa da tayi yace. “Ke zaki kashe ninfa ki sake min wuya, ki buɗe ido ki gani ba wani kare a nan sai dai ko in aljanu kike da”. Ya ƙare maganar da sauƙe numfashi mai nauyi saboda jin ta sakeshi, gefe ta tsaya tare da fara gyara rigarta daya tattare tayi ƙasa da kai kamar munafuka ta fara gyara Scarf ɗinsa dake wuyanta da hularsa. Harara ya auna mata ya tsuƙe fuska yace. "Ga nan abinci sai ki ɗauka kici”. Ya ƙare maganar yana komawa kan sallayar ya kwanta yana rufe idonsa da bakin Scarf ɗin wuyansa alamun baya son hasken. A hankali ya lumshe idanunsa yana faɗin. “Ya za'ayi bazakiyi ta ihuba kin kwanta ba al'wala ba addu'a sai charting da ƙattin banza, ni ki addabeni da ihun Ketra da baya nan yara ƙanana na bacci sai ke ki buwayeni”. Baki ta tura ba tare da ta kalleshi ba bare tace wani abu. Tray abinci da ya fita ya amso mata a kitchen ɗinsu ta kalla, sai kuma ta zauna a bakin gadon a ƙasa tana maida numfashi, tray ta ja ta fara cin abincin tana waige-waige tsoro, kusan rabi taci ta ɗaura da coffee sai kuma ta shiga bathroom ta wanke bakinta ta sabunta al'walan bacci ta fito ta kwanta bayan tayi addu'a. Duvet ɗin ta ƙara jawowa ta duƙunƙune a ciki har zuwa kanta a haka bacci ya ɗauketa. A ƙalla 43 minute da kwanciyarsa amman bacci ya ƙauracewa idonsa saboda hasken dake kunne a ɗakin tsaki ya ɗan ja ya miƙe tsaye dan kashe hasken da ya hanashi baccin. time ya kalla a wayarsa daya miƙe da ita. 1:00 Am. A fakaice ya ɗan kalleta, sai kuma ya ɗan tsaya a bakin gadon, ganin yadda take duƙunƙune cikin duvet da take rufe dashi har kanta duk da haka kuma rawan sanyi take yi, hannunsa ya miƙa da nufin kashe wutan sai kuma ya janye hannun gaban gadon su Zaid ya wuce gyara masu rufuwa yayi sannan ya juyo dan kashe wutan, karkarwa jikinta keyi bakin gadon ya ɗan zo ya tsaya a ƙalla 2 minute sannan ya sunkuyo ya ɗan ja duvet ɗin, shiru ko motsi batayi ba tabbacin bacci take yi sai karkarwar da jikinta ya ƙara kan lips ɗin ta tsaida idonsa, ta turo ɗan lip ɗinta na ƙasan kaɗan na saman kuma ta ritsashi da tsotso tamkar yar yayen data rasa nannan ɗinta, gashinta dake baje kan pillow har zuwa kan ƙirjinta saboda zamewa da hular tayi ne ya ɗan kalla a fizge. “Hmmmm”. Ya sauƙe numfashi, sunkuyowa yayi dan ganin rawan jikin yayi yawa ya wuce ace na sanyin Istanbul ne da alamun akwai zazzaɓi hannunsa ya ɗan matso dashi kan wuyanta zafi yaji rau har jikin Scarf din sa yaji ɗumin, matssss yaja tsaki. Briefcase nashi ya buɗe magungunansa dake ciki ya fara dubawa, kala biyu ya ɗauke daga cikinsu kan bedside drawer ya ajiye searched ɗin magungunan tare da goron bottle water ɗin daya ɗauka kan Tray abincin da ko rabinsa bata gama ciba. Bakin gadon ya zauna yana mai kallon tsanantan rawan jikinta kamar wacce zata sume sai tsotsar da takeyiwa lip dinta take tana sauƙe numfashi mai zafi. Hannu shi ya kai kan wuyanta ya fara jawo Scarf din dake zageye da wuyanta, da sauri ta buɗe idonta tana cewa. “innalillahi Appiy ketra”. Sai kuma tayi shiru ganinsa zaune a gabanta ya tsuƙe fuska tana ƙara jawo duvet ɗin tace. "Me nayi kuma?”. Lip ɗinta na saman da yayi jazir sai sheƙi yake yi sabida tsotsarsa da takeyi ya ɗan kalla a fakaice ya miƙo mata searched ɗin maganin. “Kisha”. Ya faɗa a sanyaye. Cikin tsanar shan maganin tace. “Ni lfyta ƙalau”. Juyowa yayi kan gadon da kyau yace. "Kisha”. Kai ta jujjya tana ƙanƙame jikinta, hannunsa ya kai da nufin jawo Scarf din da sauri ta matsa tare da cewa. "Ni ka barni inyi bacci”. Fuska a haɗe yace. "Bani abuna in ma bazaki sha mgni ba ya rage naki”. Cikin muryar bacci tace. "Wanne abun ka ni ba abunka da na ɗauka”. Yana kai hannunsa yace. “Ai bazaki iya daina min sata ba, sai ranar da na karya wuyan zanga a inda zaki ɗaura Scarf din harma da turarena kika ƙara fesawa ko”. Tana ƙara ja da baya tace. "Ni ba abinka da na ɗauka wannan cikin waɗanda aka bani a hotel ɗin nan ne, turarenka kuma ina zan ganshi ma”. Da ƙarfi ya fizgo Scarf din har saida ta matso kusa dashi sunsuna shi yayi yana mata kallon takaici yace. “Ke ƙanwar uwarsu ce ai yan hotel ɗin dole su baki kaya, ba ga turaren nawa ba”. Ya ƙare maganar yana ɓalle maganin ko wanne ɗaya ya cire. "Ni dai ba barauniya bace”. Ta faɗa tana turo lip ɗin ƙasa hannunta ya jawo da ƙarfi ta matso kusa dashi kan wuyanta ya manna hancinsa inda ƙamshin turaren jikin Scarf din ya mamaye. Da ƙarfi ta rumtse idonta saboda ɗumin numfashisa daya ratsa fatar wuyanta. Da ƙarfi ya juyota ta buɗe baki da nufin yin ƙara ya afa mata maganin a bakinta cikin zare mata ido yace. “Kina fiddashi sai na tsinka miki mari”. Yayi magnar da ɓalle marfin goron ruwan ya sa matashi a baki, ido ta rumtse da ƙarfi cikin tsananin sanar maganin ta fara kakarin amai, gefen tafin hannunsa ya manna kan bakin nata sai kuma yasa yatsarsa ma nuniya da babban ya matse hancinta yana zare mata ido yace. “Haɗiye”. Cikin rawan jiki da neman numfashi ta haɗiye. Miƙewa tsaye yayi yana goge hannunsa da Scarf ɗin ya wurga mata shi kanta, ya kashe wutan ɗakin ya kwanta. Ƙarfe biyar dai-dai ta farka daga baccin duvet ɗin da tun da zazzaɓin ta ya sauƙa ta farajin zafi ta ture gefe tayi saurin jawowa ganinsa tsaye kan sallaya yana Sallah, sai da ta gyara rigarta ta sauka ta ɗaya gefen ta wuce bathroom. Wanka ta farayi da ruwa mai zafin gaske duk da yau sanyin bai kai na jiyaba wanke bakinta taya tare da al'wala kana ta fito, ganin baya nan ne yasa ta sake tayi salla da azkar sannan ta kimtsa, bayan su Zaid sun farka tayi musu wanka suma ta kimtsasu cikin kayan sanyi. Jin ana buga mata ƙofane ta miƙe taje ta buɗe ɗaya daga cikin ma'aikatan hotel ɗin ne ya miƙo mata Tray ɗauke da abincinta da nasu Zaid sai flacks ɗin tea amsa tayi kana ta koma ciki. Sa'ad ne zaune gaban Mom ɗinsa da Uban riƙonsa gaba ɗaya baya cikin nitsuwarsa. “Kayi haƙuri Sa'ad yadda Mahmoud ɗin ya faɗa shine mafi dacewa sabida kaucewa saɓawa Allah, sannan tunda har ta tabbatar maka baya sonta kuma kaiman kaga tabbacin haka tunda har shi ke bada shawarar yadda zakuyi abin a sirri ta yadda ran iyayensa bazai ɓaci a kansa ba, to ka haƙura ni da ka gayamin zaka zoma da zan hanaka. Dan nima ina bincike kan ɗan uwansa da yace yana nan Gombe kuma akwai wanda yace min ya sanshi, ita kuma Fariyda ka dena damu da ƙinn baka number da tayi, ina da baccin taƙine dan kiyaye haƙƙin igiyar auran dake kanta kuma shiyasa bata amsa kiranka, take kuma katse kiran koda shi ya ɗauka ya bata wannan shine tabbacin tasan abin da takeyi yar gidan mutuncice.” cikin ɗimuwar rashin ɗaukar wayarsa da ciwo bai bar Mahmoud ɗin
Chapter 24 · 0% Book details