Sashe 1
Sakar Makafi Part 2 Complete Hausa Novel · about 6 min read
*SAƘAR MAKAFI*
Page 44
Na
*Aysha Aliyu Garkuwa*
Sheshheƙan kuka ta saki ta zame a wurin ta zauna ta sakin kuka mai sanyin sauti cikin rawan muryar take faɗin.
“In banda mutuwa meke raba ɗa da uwa, ta yaya zakace ko inda nake bazasu jeba”. Sai ta kuma kife kanta ka kujerar tana rawan murya tace. “Yah Amin mutuwa ta rabani da kai, ɗan uwanka kuma zai rabani da su Zaid”. Jin numfashinta na cushewane yasa ta miƙe tsaye jiki na rawa ta ɗauko ruwa tasha.
Tana kallon ƙofar ɗakin ta koma bedroom ɗin.
Cikin mmki take kallon time ɗin wayarta ƙarfe ɗaya harda rabi na dare, a hankali ta miƙe parlour ta fito, shiru sai TV dake ta aiki, cikin sanyi taje bakin ƙofar parlour ta buɗe ya buɗu kuwa, leƙowa ta ɗan yi tare da waige-waige shiru sai haske da yayi kamar rana haka ne yasa ta sauri maida ƙofar ta rufe, ba tare da ta sa pin ɗin key ɗin ba.
A hankali ta kwanta jikinta ta rufe har zuwa kai tana maida numfashi sheshheƙan kuka da tayi.
Da safe cikin mmaki take tsaye a tsakiyar parlour wayar Yah Amin dake kan Centre table ɗin ta ɗauka. 9:00 Am, ɗan jujjuyawa tayi, can gefen kujerar one sitter akwatinsa yake ta kalla, wurin sab komai nasa na cikin akwatin.
Zaid da ta bawa maganin ta gyarawa riƙon da tayi masa, tana miƙawa Zaitoon ɗaya hannun Dinnin area ta wuce dasu dan yin breakfast.
Kano
Sosai shiryen-shiryen bikin Salim da Salma ya kankama tuni baki na kusama sun fara zuwa bare na nesa.
Anan gidansu Ummi kuwa, tuni Amina ma da yaranta sunzo a cewar ta sai biki ya ƙare zata koma ranar Monday mai zuwa kenan.
“Kuma sai ki bar mijin naki shi kaɗai saboda auren ƙaninki”. Ummi ta faɗa cikin tsare ta da ido, da sauri tace.
“Ummi ai Daddyn Hafiz yayi tafi Sudan tun jiya kuma kwana goma zai yi wata ƙilma yafi shiyasa nima nace mishi zanzo. Kuma ya yarda yce ba komai inzo asha biki, in bawa su Abba haƙuri bazai samu damar zuwa ɗaurin aure ba.”
Cikin gamsuwa Goggo Dada tace.
“Mu ai barkanmu zaku ɗebe mana kewar su Zaid da iyayensu”. Murmushin Amina tayi tare da cewa.
“Suma sun kusa dawowa ai Salim sai hali yake wai Mahmoud bazaiga bikinsa ba”. Ummi tace.
"Ɗazu ma kuwa mukayi waya da Fariyda tace jikin Zaid da sauƙi sosai ma, wata ƙil zasu dawo kafin a gama bikin”. Sulaiman da Salim dake shigowa da Dr Fadil a bayansu ne, Salim na faɗin.
“Ummi kin gane shi ko?”.
Ummi na murmushi tace.
“Sosai ma kuwa”.
Dr Fadil na zama gefen Ummi yace.
“A ina uwa zata manta ɗanta”. Da sauri Goggo Dada tace.
"Niko Fadil ina Fadilan Mahmoud”. Fuska ya ɗan kwaɓe yace.
“Goggo Dada har yanzu fa ita nake jira shi yasa banyi aureba, shi kuwa Mahmoud ba kun masa auren gataba, yanzu dai a dena cewa Fadilan Mahmoud ace Fadilan Fadil”. Dariya sukayi duka, suna kallon Amina da ta fara hirar tuna rayuwarsu ta baya tun a primary school.
Ahmedabad
Shiru tayi tana kallon kujerar da mafi yawancin lokacin yake zaune akai ko kwanciya, tun jiya daya fita har yanzu goma na daren bai shigoba. Akwatinsa ta zuba wa ido cike mmkin to me hakan ke nufi, sai kuma ta zauna kan 3 seatter ɗin tare da lumshe idonta, yanayin yadda ya zuba mata ido da yadda ya fitane ya gilmawa ganinta, da sauri ta buɗe idonta sabida ganin yadda idonsa ke zubda hawaye wani na korar wani ya gilmawa ganinta a fili tace.
“To dama yana da hawayene shima? To menene yasa baimin mahaifar daya saba ba, baice zai ɓalla min hannuba, bai min tsawa ba, bai harareni ba”. Numfashi mai sanyi ta fesar murya can ƙasa tace. “Ko ya gane ƙarfin zunubin raba uwa da yaranta ne, ko Yah Amin ya tunone shi yasashi kuka”. Ta ƙare maganar idonta na cika da ƙwallan da kawai taji suna zubo mata. Da sauri ta juyo kanta jin kamar mutum ya shigo, ba kowa haka yasa ta kuma tana jan numfashi ƙamshin turarensa ne dake cike a parlour ta shaƙa.
A hankali ta ɗan miƙe tsaye.
Zama tayi a bakin gadon tare da zubawa Zaid dake gefenta ido, ganin ya buɗe idonsa ya matso kusa da ita tare da cewa.
“Appiy Appiy pipiy”. Rungumeshi tayi irin rungumar da take ganin Mahmoud ɗin nayi musu, wanda duk rikicin da sukeyi in ya musu haka a take sukeyin bacci.
Kai ya ɗaga ya ɗan kalleta cikin maganin bacci ya kuma cewa.
“Appiy pippiy, Ammiy”. Cikin mmkin jin yau yadda ya kira Ammiy ya fita ras kamar yadda suke kiran Appiy ya fita ras. shafa kanshi ta farayi a haka ta samu ya maida bacci ta kwantar dashi.
Cikin sanyi ta kuma tashi ta fito parlour saboda tsoron da ya fara diro mata, ƙofar ta rufe ta sa pin ɗin.
Washe gari da rana waya take yi da Aunty Saddiqa.
“Yau ne za'ayi sisters day gashi Babu ke za'ayi”. Cikin sanyi tace.
"Wlh gaba ɗaya hankali na ya dawo gida, nasan yanzu duk kun haɗu ni kaɗaice bani”.
Zainab dake kusa da Aunty Saddiqa tace.
"To wai dan Allah sai yaushe zaku dawo”. Ɗan guntun tsaki taja cikin sanyi tace.
“Nima ban saniba”. Saddiqa tayi saurin cewa. “To ki tambayeshi mana kiji wata kil dai zaku dawo kafin auren Raihana kam dai ko?”. Da sauri Tace.
“Auren Raihana ansa rana ne”. Zainab tace.
“Eh jiya Hajja Inna tazo da Kawu Kabiru da Bashir ɗinta da iyayensa da kayan aure da sadaki ke harda kayan rufi duk sun kawo”. Da sauri tace.
"Yaushe ne akasa”. Saddiqa tace.
“Ba nisa dan nima bazan koma Adamawa ba, sai anyi bikin in mun maida Amarya taraba daga nan sai in wuce Yola wata ƙil ma mu dawo tare idan oga ya yarda”. Cikin sanyi tace.
“Dan Allah Yaushe ne bikin?”. Salma da yanzu ta shigo ne ta matso kusa da wayar da suka ajiye a gabansu tace.
“22 December”. Da sauri ta fara lissafi cikin gyaɗa kai tace.
"A in sha Allah kafin nan kam mun dawo, amman Aunty Saddiqa wannan karon zaki daɗe sosai kenan naga fa yanzu auren ya kai 40 days ya rage”. Tana kallon Zaitoon da ta leƙo tace.
"Ai da yake Daddy Aslam ya tafi wani cous Pakistan zaiyi wata uku shinefa nima zan sake, yara kuma na barsu wurin mamanshi”. Cikin jin dadi tace.
“Nima Allah yasa mu dawo da wuri”. Salma tace.
"To ki tambayesa mana”. Tana kallon Zaitoon dake ta ɗan kamo hannunta tana jan tana faɗin Ammiy Appiy! Appiyyyyy”. Ta ƙare kiran sunan da kuka har lau kuma tana jan hannunta da nuna mata hanyar fita parlour da yake ƙofar a rufe cikin jawo hannun Zaitoon tace.
“In na ganshi ko, yau kwana biyu kenan ban ganshi ba”. Da sauri Aunty Saddiqa tace. “Kamar ya baki ganshi ba”. Kai ta ɗan jujjuya kana tace.
“Aunty Saddiqa zamuyi waya anjima, bari in bawa Zaid maganinsa”. Bata jira cewarta ba ta katse kiran, ido ta zuba musu ganin shi Zaid yana tsaye bakin ƙofar bedroom ɗin yana kiran Appiy. Ita kuwa Zaitoon hannunta take taja tana ta kiran Appiy a jere a jere, cikin sanyin murya tace. “Zaitoon nima ban san inda Appiynku ya shigaba”. Sai kuma ta miƙe tsaye ƙofar ta buɗe suka fito parlour da ɗan gudunsu na yara suka nufi kan 3 seatter ɗin, sai kuma duk suka juyo suna ce mata Appiy, fuska a kwaɓe tace.
"Kai wai uwar me zai baku da zaku addabeni”.
Tab ɗinsu ta miƙa musu ta zauna kusa dasu, ganin sun ɗan fara wasa.
Kiran Sa'ad da ya shigo wayar Yah Amin ɗin da ya bari kan Centre table ɗin ta zuba wa ido, har ya katse bata ɗauka ba, numfashi mai sanyi ta fesar ganin su Zaid ɗin sunyi bacci a wurin.