Sashe 70
Sakar Makafi Part 2 Complete Hausa Novel · about 5 min read
and yellow sai ɗan purple jersey veil purple color tayi rolin kanta dashi fuskarta ta fito ras sai kamshi take bazawa tayi ras da ita, da sauri ta juyo ganin Mamy ta cikin madubi tana ɗan yin ƙasa da kanta tace. "Mamy ina kwana”. A takaice tace. “Alhamdulillah”. Shiru tayi kanta a ƙasa tana jiran me Mamy zatace. “Kin kira Mahmoud kinji ya jikinsa ne?”. Mamy ta katse shirun, kai ta jujjuya alamar a'a, fuska a haɗe tace. "Shima sai nace zan ja miki Allah ya isa ne in baki kira ɗinba kafin zaki kira!?”. Da sauri ta fara jujjuya kanta ido na cike da ƙwalla tace. “Kiyi haƙuri Mamy kar kim Allah ya isa, bani da number shi fa”. Harara ta danna mata tace. "Wayar Aminullah da take wurinsan zaki kira, tunda ke dai baki cika maceba, number mijinki ce baki da ita sabida isa ke sai dai a biki kikeso ba ke zaki bishiba tunda kece aljannarki ke ƙarƙashin digadiginsa ai dolene ma yasa Mahmoud ya sakeki to me ma zai yi da mace mai taurin kan tsiya, zaki kira ki tambayi ya jikinsa ki masa addu'a ko sai na saɓa miki tunda ke baki da kara ai ko dan su Zaid Mahmoud ya cancanci kulawa a wurinki mu samman irin halin da ya shiga jiyan nan”. A hankali tace. "Mamy zan kira”. Kwaffa tayi ta juya har taje bakin ƙofa tace. "Idan kin kirasa ki kira Abbansu da Umminsa ki tambayi ya jikinsa, har Amina ki kirata ki tambayi jikin ɗan uwanta”. Daga nan ta juya ta fita. A bakin gadon ta zauna ta jingine kanta da allon kan gadon tare da miƙar da sawunta ta jawo pillow ta ɗaura kan cinyarta haɗe da jawo wayar ta, a ƙalla 6 minute tana riƙe da wayar, jin kamar Muryar Mamy na tahowa inda take ne tayi saurin lallatsa numbersa ɗin Yah Amin ɗin tayi dailing tare da ƙara wayar a kunne. Shiru tayi tana jin yadda wayar ke bada sautin ɗut-ɗut numfashi ta fesar a hankali lokacin da taji an amsa kiran sai kuma taji shiru ba'ayi magna ba, haka yasa ta ɗan motsa lips ɗin ta a hankali tace. "Assalamu alaikum Appiy!”. Ta faɗa can ƙasan maƙoshinta, cikin wata iriyar galabaitacciyar murya mai sanyi yace. “Hmmmmm”. Shiru tayi tana jin sautin yadda yaja numfashi a kunnenta, murya can ƙasa ya kuma cewa. “Ke baki iya gaisuwa bako!?”. Baki ta ɗan tura like tana gabansa cikin sanyi tace. "To ba kai bane”. Murya cike da alamun ciwo yace. “Nine me? Me kuma nayi?”. Tana kwaɓe fuska tace. “Kayi shiru kaƙi mgna”. A taƙaice yace. "To ina jinki!”. Kamar cikin raɗa tace. “Ina kwana ya jikinka”. Cikin muryar raɗar da tasata lumshe idonta yace. “Kinyi farin ciki ai ko?”. A hankali tace. "Kamar yaya?”. Murya sarƙafe da sautin da ke bayyana raɗaɗin ciwon da yake ciki yace. "Wanda bakya so bashi da lfy, wanda kikeyiwa fatan mutuwa sauran ƙiris ya mutuwa”. Ido na cike da ƙwalla tab a hankali tace. "Ni wa nakeyiwa fatan mutuwa”. Ta ƙare maganar murya na rawa. Yana jan numfashi da rumtse idanunsa yace. "Wanda kikafi tsana fiye da komai na duniya, wanda da kikaji an aura mikishi kika Suma”. Dire mgnar murya can ƙasan maƙoshinsa yaja kalmar suman cikin ƙahon zuciyarsa. Murya a sanyaye tace. "Appiy ya jikinka da sauƙi ko? Tunda har ka fara neman faɗa da masifa”. Numfashi mai nauyi ya fesar cikin muryar raɗa yace. "Alhamdulillah da sauƙi ina su Zaid”. Tana ɗan kallon kofar shiga tace. "Suna wurin Raihana”. Hmmmm yace tare da yin shiru, itama shiru tayi tana sauraron sautin sauƙan numfashinda, a ƙalla 4 minutes baice komai ba wayar ta ɗan ɗago ta duba dan ta fara zaton ko kiran ya katse ne duk da tana jin alamun numfashinsa, ras bai katseba harara wayar tayi ta ɗaura da cewa. “Allah ya kara sauki sai anjima”. Da sauri yace. “Ke karki kuskura ki katse min kira”. Tana kallon Aunty Saddiqa data shigo tana cewa. "Fariyda har yanzu baki farkaba, Malam ya dawo munje mun gaisa yana tambayar ina kike ke bai ganki ba”. Da sauri ta nuna mata fuskar wayar alamun tana waya ne. “Wacece”. Ya tambaya a hankali. Tana kwaɓe fuska tace. “Aunty Saddiqa ce”. Ta bashi amsa. Murya na ƙarfi yace. “Bata waya”. Wayar ta miƙawa Aunty Saddiqa, a ƙalla 3 minute suna magna haka yasa Fariyda zuba mata ido ganin yadda take magna dashi da jera masa addu'a a ranta tace. Mutumin da ko an gaidashi an mishi addu'a baya cewa Amin. Bayan ta miƙawa Fariyda wayar ne ta juya ta fita tana faɗin in kin gama Malam na kira. Kai ta gyaɗa tana ce masa. “Sai anjima”. Shiru tayi jin yadda yake mgnar da kyar kamar a fizge yace. “Ke karki katse min kira fa”. Baki ta tura tace. “To katina zai ƙare ai”. A hankali yace. “Ni ba'a katse min kira”. Ya faɗa gami da yin shiru, a hankali tace. "Appiy Baba Malam yana kirana”. Murya na rawa alamun ciwon ya yunƙuro kishi a hankali yace. "Ba nace daina kirana Appiyn ba”. Baki ta ɗan turo a hankali tace. "Toh Moudy yayi ai”. Numfashi ta fesar jin ya katse kiran miƙewa tayi ta fito parlour a tare suka wuce parlour Baba Malam ita da Khadija suna zama gaban Baba Malam wayarta na ɗan yin ƙara alamun shigowar saƙo cikin mmki take kallon saƙon ganin ya yasa mata katin waya har na 100k cikin ranta tace. “in ance mai bai san zafin kuɗi ba yace an rainashi ko uwar me zanyi da wannan uban katin”. A fili kuwa Baba Malam ta gaida bayan sun gaisa ne ya kalli Sadiq dake gefensa wanda tare sukayi breakfast cikin bada umarni yace. “Fariyda tashi kuje asbitinsu Nasir ke da Saddiqa da Nana da Khadija kuje ku duba Mahmoud da jiki, dan ɗazuma ina can abin ya ƙara tashi, sai dai Alhamdulillah kafin in fito ya lafa tashi ka kaisu yanzu. Ya ƙare maganar yana kallon Adda Nana da Saddiqa da suka shigo cikin shirin fita.......