Sashe 89
Sakar Makafi Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Baki ta tura ido cike da hawaye take watsa mishi harara cikin iyakar gaskyarta tace. "Ni bana sonka ai kasan bana sonka, kamar yadda nima nasan baka sona kaida kankama kacemin ai dai kin san bana sonki kuma bazan sokiba har gaban abadan. Nasan kuma haka ne kuma nima haka ne. Kasan bana sonka ko? Kuma bazan taɓa sonkaba har gaban abadan ka dai kasan bana sonka? Dan haka ni bazan rayu da kai ba yanzu sai ka yi min sakin kamar yadda su Abba sukace tunda ka san bana sonka ai ko?”. Ta ƙare maganar da alamar tambaya. Jajayen idanunsa ya zuba mata jiki na rawa yake gyaɗa mata kai alamar eh ido cike da wasu tsumammun hawayen da suka idanun sauya launi a take sukayi Nasir murya na rawa haɗi da cushewar numfashi da tunani yace. “Eh na sani ai tunda naji labarin ranar da aka ɗaura mana aure har suma kikayi nasan bakya sona tunda har suma kikayi kawai dan ance mini an aura min ke dan kin tsaneni kin maidani masifa da zama dani zai saki suma ai nasani nasan bakya son sumafa kikayi Fariyda kawai dan zaki rayu dani a matsayin miji kika suma”. Cikin galabaitar gajiya da yunwa ta zuba masa ido tana jin yadda yake ta mai-maita kalmar ta sumar nan sau ba adadi yana mgnarne daga can ƙasan zuciyarsa take fitowa da zafin, fuska a tsuƙe tace. "To ni dai har abadan bazan sokaba, ka rubutamin takardata kamar yadda iyayenmu suka baka umarni, ka barni in samu in auri wanda yake sona tun ina ƙarama. ba kai da nasan tun fil azal baka sonaba ka tsaneni kai da kanka ka bani damar kula maza da aurenka a kaina da na biye maka sai in kai kaima wuta”. Ta ƙare maganar tana zubda hawaye. Murya na rawa yace. "Please dan girman Allah ki daina tuna min wannan jahilci da rashin sanin ciwon kai da nayi, ni da kaina inajin tsanar kaina in na tuna wannan abu Please Farriyyhah ki yarda dani nasan tabbas na ƙiki ƙi mafi muni da tsauri, amman wlh a yanzu duk tsaurin kiyayyar ya zama so Please ki daina cemin zakije ki auri wani wlh zuciya zata iya bugawa Please My Angel”. Tureshi tayi tana faɗin. "Nifa Wlh sai ka rabu dani dole ka sak...” Sai kuma tayi shiru ganin yadda yayi da fuska murya a kufule yace. "Wato har kin mance sharaɗin Mamy har zaki cemin in sakeki ko? In kin mance na Mamy tunda Ita kin rainata ai bazaki mance na Allah ba da ya tsinewa duk matar da ta tambayi mijinta saki, wlh kika sake yimin mgnar saki ko mgnar waɗannan banzayen jahilan wlh yau wuni zanyi akanki har sai kin kasa magna bare ki yi min rashin kunya kin ganni nan sai in kwana ban gajiba tausayunki ne yasa na barki kuma duk abinda zan yi dake halal ne lada ma zan samu”. Ya ƙare maganar yana nuna mata papi ɗinsa, haɗi da miƙa hannunsa ya jawo goran Admiral ɗin. Ita kuwa tunda ya fara magna tayi shiru haɗi da tura baki ido na cikowa da sabbin hawaye ganin Papi ɗinsa kuma yasata rufe ido tana matsawa gefe, jin ya manna mata bakin gorar Admiral ɗin ne yasa ta buɗe idonta dake cike da hawaye, fuska a tsuƙe yace. "Buɗe baki ki shanye duka, bazaki cutar min da kanki da yunwaba”. A hankali ta fa Sipping Admiral ɗin tanayi tana zubda ƙwallan har saida tasha kusan rabi ta janye kai a hankali tace. "Ni na ƙoshi ka buɗe min zan tafi gidan Hajja Inna”. Maltina ya ɗauka ya ɓalle marfin yasa mata shi a baki, yadda ya tsareta ne da yadda ya kamo hannunta ya ɗaura kan abinda ke sa hanjin cikinta hautsinewa yasata sha fiye da rabi. Miƙewa yayi ya kamo hannunta ya miƙar da ita bakin gado ya kawota ya kwantar da ita haɗe da jan duvet ya rufeta. Guntun Admiral ɗin data bari yasha da ƙarin gora ɗaya. Kan gadon yazo ya kwanta haɗe da jawota jikinsa yana ɗaura kanta bisa ƙirjinsa yace. "Kiyi bacci in mun tashi zan kaiki, kinga har yanzu maganin murar nan bai gama sakeki ba”. Shiru tayi tana jin yadda yake shafa bayanta, a hankali kuma ya fara sauya fitar numfashi haɗe da fara jan jallabiyar, da sauri ta miƙe zaune ido na zubda wahaye murya na rawa cikin gajiya da tarin bacci tace da tsoron lamarinsa cikin rauni tace. "Please dan Allah kayi haƙuri ka barni inyi bacci wlh na gaji bazan iya bafa”. Kai ya fara jinjina mata kamar gadangare idanunsa da suka fara sauya launi ya zuba mata yana zare jallabiyar jikinsa ya cilla gefe, da sauri ta rufe idonta jiki na rawa ya rungumeta cikin sanyi yace. "Bazan miki komai ba, ina son samun ɗumin jikin kine My Angel zamuji sauƙin sanyi”. Ya ƙare maganar yana zare mata jallabiyarsa dake jikinta ya cillashi gefe. Hmmmmmm suka dauƙe numfashi da ajiyan zuciya a tare lokacin da tafarsu ta mannewa juna, wani irin masifeffen kunya ne mai haɗe da takaici ya rufeta jinta ba komai a jikinta shima ba komai a nasa jikin, wai yau itace da Mahmoud a wannan yanayin mafi ƙololuwar kusancin duniya suna gari ɗaya! ɗaki ɗaya! gado ɗaya! Duvet ɗaya! Pillow ɗaya! Fatarta manne da tasa fatar a yanayin da babu wani sutura a tsakaninsu sai duvet ɗin daya rufesu. Juya kanta tayi jin yana ƙara ƙwaƙwumeta a jikinsa kamar zai maida ita cikin cikinsa ya ilahi wai a raye take ko a mace ido biyu take ko a mafarki ne koko farke a haka yasata rufe ido kamar yadda shima ya rufe nasa idon a haka sukayi bacci. Ƙarfe tara dai-dai aka fara shirin fansar idon. Raihana da saida tayi wanka akazo aka ɗauki Humaira taje gidansu ta ɗanyi mata make-up acan sannan suka dawo, har lokacin dai ba Fariyda ba dalilinta sai ƙarfe goma dai-dai aka fara fansar. Alhamdulillah anyi fansar idon amarya lfy sha ɗaya dai-dai aka gama kamar yarda al'darsu take uwar ango ta fanshi ido amarya da saniya da shanu mafarin garke kenan sauran yan uwa duka kowa ya fanshi idon amarya kana aka fara na ango sai ƙarfe ɗaya dai-dai aka tashi daga fansar idon inda ango yasha ruwan kuɗi da kyautan shanaye Sulaiman kam ya zama abokin ango tuni komai dashi akeyi hakama Farooq ko ina yana maƙale da Zainab shi kuwa Sulaiman tarko nai ya kama kurciya shida Humaira sun fara zantawa bisa sahalewar Yah Farooq. A hankali take tafiya da ka gani kasan taji jiki a hannun maza, duk da ba ɗingishi take yi ba, amman da ka gani kasan ta gurzune iya kar gurzuwa abu ya haɗu da yongwali sarkin raki. Hand bang ɗinta dake hannunsa ya gyarawa riƙo haɗe da miƙa mata hannunsa ɗaya dan ganin kamar zata faɗi, da ɗan ƙarfi ta riƙeshi dan tabbas ta kusa faɗuwa sawunta sam ba ƙarfi sai rawa sukeyi. Ido Hajja inna ta zuba musu kamar ta samu TV har Saida suka iso tsakiyar parlour Arɗo Habu kakansu sannan tace. "To saketa mu ga uwar yauƙi ke ko yaushe aka ganki largi-largi kamar bulala sai raki yanzu haka zatace yunwa takeji ko shi yasata wannan narkewar”. Murmurshi Arɗo Habu yayi haɗi da nunawa Mahmoud wurin zama kusa dashi. Zama yayi tare da jawo hannunta ya zaunar da ita gefe yana kallonta yess tana da longomi kam dan yasan yayiwa idaya abinda yafi haka da yake ita jakace gar zaka ganta, baima yi zaton ritsawar da yayi matan nan zata iya tashi ta tafi da sawuntaba. Hannu ya bawa Ardo Habu suka gaisa sai kuma ya ɗan gyara zamansa ya matso kusa da ita sosai kanta ya jawo ya manna da kafaɗarsa a hankali yace. "Bacci ko yunwa”. Lip ɗinta na ƙasa ta tura murya na rawa tace. "Duka biyu”. Hajja inna ya zuba wa ido sai kuma ya kwaɓe fuska yace. "Tace bazataci komai ba sai abincinki zataci Bashir da kanshi ya kaimana abinci taƙi ci wai naki zataci”. Ya ƙare maganar yana ƙara sunkuyo da kanshi ya manna lips ɗinshi a goshinta. Worman dake jere gaban dattijon Hajja Inna ta jawo haɗe da fara zuba musu zazzafan dandarerun naman zabbi da tayi, ganin ta jawo wani bowl ɗin zata sane yace. "Bari haka wannan ya isa”. Tana kallonshi tace. "To kai ɗinfa”. Gyara zamansa yayi yana gyara mata jinginar, idonsa na kan ɗaya kular da Hajja inna ta buɗe wanda yake cike da chips soye plate ta jawo ta zuba mata kana ta gyara zamanta ta jawo mug ta fara haɗa mata tea. Fork ya ɗauka yana gyara zamansa ya soƙo tsakar dandarerun haɗe da chips ɗin ya kai mata baki yana faɗin. "Ha buɗe baki”. Cikin kasalar rashin bacci da uban gajiyar daya tara mata da sauran ɗan ragowar aikin maganin muran da rashin bacci hanata janye jukinta a hankali ta buɗe baki, cikin kulawa yasa mata. Murmurshi Arɗo Habu yayi haɗi da cewa. "Sannu tattabara uwar ƙoto dan sakalci sai ka bata a baki”. Idonshi na kanta yace. "Arɗo ta gajine shiyasa”. Baki Hajja inna ta taɓe haɗe da cewa. "Me tayi da zata gaji yarinya ko yaushe lagwai-lagwai kamar ganye ba auki sai raki yar tafiya daga Kano zuwa nan ai nima tsohuwa ina yinta kuma bana jemewa haka in narke kamar zan suma bare ita yarinya”. Girarsa ɗaya ya ɗan ɗaga mata yana kuma kai mata sokar naman, ko taunawar a kasalance take taunawa a hankali. Jin sallamar su Adda Nana ne yasa Hajja inna cewa. "Ai na zata bazaku isoni ba, tun jiya nake tsammanin nan zakuzo mu kwana nayi muku girki ba wanda yazo sai su Farooq da Sulaiman da Mujahid, sai yau da safe su Abu su kam duk sunzo tunda ni uwarsuce”. Kusan a tare suka shigo da sallama a bakinsu sai kuma duk suka ɗan kalli juna haɗi da zama kan kujerun. Saddiga ne ta kalli Mahmoud da yayi tamkar baishi shigowar suba, sai tea da ya fara bawa Fariyda dake kiciniyar tashi cikin raɗa yace. "Angel tsaya ki sha tea”. Tana kwaɓe fuska ta turo ɗan baki a hankali tace. "Appiyn Alhamdulillah I'm full.” Kai ya ɗan jujjuya mata, yana ƙara manna