← Book details Sakar Makafi Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 14 OF 95

Sashe 14

Sakar Makafi Part 2 Complete Hausa Novel · about 6 min read

Dogon tsakin da Aunty Maryam taja ne yasa Amira yin kwaffa tare da kallon Sajida data shigo riƙe da waya.
"Eh Aunty Amina ga Aunty Fariyda”. Amsar wayar tayi tana sharce hawayenta da wani ke korar wani cikin son danne kukan da yaƙi barinta tace.
“Aunty Amina ya bani tsoro fa, amman Dr sunce ba matsala”.
Cikin ɗan samun sauƙin firgici Amina tace.
"To ki daina kuka ya isa haka, su Abba ma jibi zasu zo, wata ƙil nima zanmuzo da Daddyn Hafiz da Sulaiman”. Tana amsar Zaid da yake miƙo mata hannu ta rungumeshi tace.
“Allah ya kawoku lfy.” daga nan ta miƙawa Sajida wayar. Su Zaid ɗin ta zuba wa ido wasu hawayen na taruwa.
“Shine mafi ƙololuwar gatansu a duniya, shine wanda sukafi so fiye da kowa kamar yadda shima yake sonsu fiye da kowa, tabbas shine Garkuwarsu ya hanasu jin maraici ta ko wanne sashi ta ko wacce siga ya hanata jin cewa su marayune, ya riƙe matsayin uba har ya haɗa dana uwa ya riƙe tunda har abinda uwa keyiwa yara yanayi musu ji yakeyi shi kaɗai ya ishesu a rayuwa baya barinsu a kullum sai sunji ɗumin jikinsa ko ƙaiƙayi da fatarsa keyi in fatar wani ya taɓashi su fatarsu bata mishi komai ji yakeyi ya ishesu komai baya son taunakon kowa a kansu kuma bata taɓa ganin gazawarsa ba. Wannan shine nazarin da yake mata yawo cikin kanta da zuciyarta.
“Ƙarfe 10:17. kuje Arda ya me daku Maryam, kun bar su Imran sun kaɗai a gida”. Yah Saleh ya faɗa yana kallon matar tasa.
“Cikin haɗe fuska tace.
“To kai kwana zakayi a nan kenan”. Yana kallon Mahmoud ɗin da ya fara sake rawan sanyi yace.
“Eh. Da sauri Arda yace.
“A'a kai kaje gida zan kwana dashi”. A hankali ta miƙe tsaye Socks ɗin ƙafarta ta cire, kana ta dawo ta wurin sawunsa, inda Amira take tsaye, blanket ɗin da ya ɗan zame daga kan sawunsa ta ɗan ture ta fidda sawun nasan duka waje, tafin hannunta da ta dake da ɗumi saboda cire gloves da tayi yanzu, numfashi mai sanyi ya fesar lokacin da ta manna hannunta a sassayan kafafun nasa,
Socks ɗinta ta saka kishi tana kallon zara-zaran yatsunsa. Tsaki Amira taja tana mai shaƙar ni'imtaccen ƙamshin jikin Fariyda wanda ya hanata matsawa.
Ita kam Fariyda batama san tanayi ba. Wurin zamanta ta koma ta zana tare da
fara zura mishi gloves ɗin hannunta, a tafin hannnunsa ido ya ɗan buɗe cike da mayen allaurar ya kalleta sai kuma ya lumshesu yana kamo hannunta yace.
“Zaid”. Sai kuma yayi shiru alamun bacci ya kuma ɗaukarsa sai dai hannunsa dake damƙe da nata gam.
“To ai sai kace mata ta tashi mu tafi Yah Saleh ta barshi ka kula dashi”. Amira ta faɗa tana bin bayan Aunty Maryam suka fita.
Suna fita Sajida ta fito riƙe dasu Zaid.
“Ina Fariyda kuma”. Amira ta tambaya a yatsine.
Sajida na miƙawa Arda Zaid tare da gyara riƙon Zaitoon tace.
“Ita anan zata kwana zan koma dasu Zaid mu kwana a gida”. Cikin tsuƙe fuska Aunty Maryam tace.
“Akan me zata kwana a nan tunda ga ɗan uwansa zai kwana tare dashi”. Tana ɗan tura baki tace.
“To mijinta ya riƙe hannunta gam taja-taja bai sakeba, shine Yah Saleh yace ta zauna su kwana tare shi zai fito parlour su suna ciki”. Cikin faɗa tace.
“Ta tabbata anan in taga dama, da zaki wani cemin mijinta kin fini sanin mijinta ne, tunda ta auri wa ya mutu ta kuma dawo kan ƙani shima zata kalallameshi kamar yadda ta kanainaye zuciyar Aminullah”. Da sauri Amira tace.
“In sha Allah wannan dai nan gani nan bari awarar mayya ga yaji ga albasa ba damar ci, in ma ita mayyace wlh Mahmoud yafi ƙarfinta in sha Allah sai mun haifi kyawawan yaranmu”. Ido da baki Sajida ta zuba musu sai kuma kawai tabi bayan Arda a ranta take faɗin.
“Da yake nice mareniyar wayonku ba, ni zaku gayawa yo wargi ma ai wuri ya samu duk haukar nacin son da Amira keyiwa Yah Mahmoud ko kallo bata ishesaba ta isa nema in yana wuri ta tsaya a wurin in dai Yah Saleh baya wurin duk wannan kallon maitar da tayi masa ai dan yana cikin ciwo da mayen allurane da tuni yace zai ƙwaƙule mata ido,”. Sai kuma ta lumshe idanta lokacin da suka shiga mota tana gaba su suna baya, ƙara rungume yaran tayi tana mai hasaso kyan sura da haibar Fariyda a hankali tace.
“Kamar ita tayi kanta in kuka take yi ma kyau takeyin in dariya takeyin' ma kyau takeyin in kuma tana mgna da raunin kamar shogobar furen da ya ɗanji ɗumin rana yadda yake yaushewa haka muryarta keyi”. Aunty Maryam tace. “Ke me kike cewa”. Cikin tura baki tace.
"Addu'a nakeyiwa su Zaid”. Amira tayi saurin cewa. “Wlh ni dai yara bazasu hanani bacci ba, yadda kika kwasosu ke ɗaya ke kaɗai zakiji dasu”. Da sauri Sajida tace. “Sosai ma kuwa zanji dasu kuma nasan ko kowa bai tayani riƙonsu ba Imran da Iman zasu tayani tunda su dai kam jininsu ne ƴaƴan Yah Amin sun cencenci muyi musu komai Yah Saleh da yana gida komai tare zamuyi tunda jininmune su muna son abunmu”. Ta ƙare maganar cikin alamun rashin tsoron su da tsiwa. Aunty Maryam tace. “Ke bafa na son rashin kunya”. Tana shafa kan Zaid tace. "Ni bada ke nayi ba da Amira nakeyi”. A fusace tace.
"Ita ɗin sa'arki ce dan inskanci waccar yarinyar Aunty naji kike kiranta Amira da a ƙalla ta baki shekara goma baki ce mata Aunty sai wacce ko ta fiki bazai wuce da shekara uku ba”. Ɗan tura baki tayi tace.
"Itafa matar yayana ne Amira kuma me haɗina da ita”. Tsawar da Maryam ɗin tayi matane yasata murguɗa musu baki tayi cib har suka isa gida.
Yara kuwa tunda tayi musu wanka ta basu Custard ko motsi basuyi ba sai da safe.
Kitchen ta shiga dan sama musu abinda zasuci, Imran da Iman kuwa na zaune dasu a parlour suna wasa dasu.
Baki ta taɓe ganin yau Aunty Maryam ɗin da kanta ita da Amira suke kitchen ɗin sai Khyri dake tayasu aikin.
Amira dake soya chips ne ta kalla a fakaice a ranta tace.
“Hmmm Yah Mahmoud ɗin ne zaici”.
Acan Hospital ɗin kuwa tun bayan sallan asuba Arda yazo.
Zaune ya sameta yana riƙe da hannunta har yanzu da alamun haka suka kwana, idanunta dake lumshe alamun bata dade da samun bacci bane yasata makara shi kuwa Mahmoud allaurar bata gama sakinsa ba, da hannu Yah Saleh yayi masa alamun su fita.
Chapter 14 · 0% Book details