← Book details Sakar Makafi Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 21 OF 95

Sashe 21

Sakar Makafi Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Daga kan sawunsa take kallonsa har zuwa sama murya a sarƙafe da rawan sanyi tace. “To me zan kiraka?”. Yana gyara jacket ɗin sa yace. “Baki san sunan da ubana ya raɗa min bane da zaki tambayeni me zaki kiraki, ko Mahmoud ɗin sunanki ne? Ba nawa ba”. Yayi magnar yana kallon gashin kanta dake zube kan kafaɗunta, kai ta sunkuyar ta tura baki tace. "Salla zan yi kuma ba hijabi”. Ko ta inda take bai kalla ba ya juya ya fita. Cikin sanyi ta koma bakin gadon, 3 quarter T-shirt ɗin da ya bata, ta zura, gaban dressing mirror shi ta tsaya tana mai sauƙe numfashi saboda sassayan kanshi da kekkyawan ɗakin nasa keyi wanda sai yanzu ma take iya fahimtar tsarin ɗakin dan yadda ta shigo a gigice jiya bata fahimci komai ba, ɗan roban da taga set ɗin kum da mayykan gashisa ta jawo, taje kan tayi ta shafa manshi ta fesa turaren gashinsa sannan ta tubƙe gashin ta kitse jelarba ta naɗe. Manshi ta ɗan shafa dan rage sanyi sai kuma turarensa data fesa. Wordrobe ta buɗe a hankali tanayi tana kallon ƙofar shigowa, hmmmm ta faɗa a fili tana mai kallon tsarin kimtsa kayan sa dake cike cib kai kace a ƙasar yake da zama din-din-dim ba zuwa yake yi ba, komai yana gefensa ido ta tsaida kan step ɗin da Socks, gloves, Scarf, caps ne kawai zalla a wurin kala da ban da ban, hulunan saƙar ulun dake wurin ta fara ɗagawa a hankali ta dauke maroom mai ɗan tambarin M a sama goshin, kai ta jinjina ganin yadda hular ta zauna cib a kanta ta ɓoye duk himilin gashin kanta da kunnenta, Scarf ta ɗauka mai ɗan girma shima maroon color ta naɗe wuyanta cib, sai kuma ta zaro Socks inrin dogayen nan farare ta saka, tsawonsu yasa suka rufe duk Gwari ta gloves ta saka a hannunta, sai kuma ta kalli kanta a jikin madumin jikin Wordrobe ɗin duk jikinta a suturce yake, sai dai 3 quarter ɗin da ya ɗan kamata sosai musamman cinyanta da mazaunenen ta. A hankali ta dawo kan salla cikin rashin gamsuwa da suturar a dole ta kabbarta sallah. Koda ta idar zama tayi a wurin tayi Azkarul Sabah, kusan ƙarfe 8 ta koma kan gadon ta kwanta tana mai lumshe idanta lokacin ɗaya baccin da firgici da tsoro ya hanatayi a daren jiyan ya kwasheta. Ƙarfe biyu dai-dai ya farka dan kiran Salim daya addabeshi. “Bacci kake yi ne”. Yana zuge zip ɗin jacket ɗinsa yace. “Ban sani ba”. Yayi magnar yana kallon ƙirjinsa tabbas fatar jikinta ya ɗan manne da nashi cikin sauke numfashi yake shafawa cikin son tabbatarwa jin ba komai. Numfashi ya ɗan sauƙe dan sanin yadda fatar jikinsa keyi in dai fatar wani ya taɓashi jin ba ƙaiƙayin ba kuma ƙarajen kuma baiyi jaba ne yasashi janye idonsa yana tuna wannan shine karo na biyu kenan jin Salim na faɗin. “To ga Abba in ma ni bazakayi magna ba”. Gyara zamansa yayi yace. “Abba Barka da safiya”. Abba yace. “Barka da rana dai ko Mahmoudu ya jikin naka da sauƙi sosai ko”. Cikin tabbatarwa yace. “Alhamdulillah da sauƙi sosai Abba kar kace zaka zofa”. Cikin gamsuwa yace. “To Alhamdulillah haka dai Saleh yace min ɗazu da safe yaje kun koma kunga Doctor yace ba komai sun ƙarasa ma alluranka. Ina iyalintaka da yaranku”. Yana meda zip ɗinsa yace. "Suna gidan Yah Saleh wurin Sajida”. Bayan sunyi sallama ne yayi al'wala ya fito yayi salla a parlour. Kan sallayar ya jawo system nashi ya fara ɗan aikin da ba'a rasa ba, kai ya jinjina cikin gamsuwa ganin tuni kamfanonin da ya bawa aikin kayansu sun gama komai har wasu sun fara loda kayan cikin tirelolin dan kai kayan bakin teku yanayi yana ɗan shafa. kekkyawan farin karensa da ke gefen yana kaɗan jela. A hankali ta miƙe tsaye bayan ta idar da sallan la'asar da ta haɗa da azahar data wuceta tayi ƙasarunta, cikinta ta ɗan shafa dan yunwar da taji na murɗarta rabonta da abinci tun jiya da safe a hotel. Ta buɗe ƙofar ɗakin ta ɗan leƙo kai corridorn da yake cike da haske da sheƙin gyara sai kamshi da sanyin da yafi na jiya dake busowa, cikin ɗan ƙara leƙowa saboda tsoron cin karo da karen tace. “Appiy! Appiy”. Kanshi ya ɗago yana mai rufe system nashi da tattara wayarsa da ta Yah Amin da tata wayar data wurgar garin gudu ya zurasu cikin briefcase ɗinsa. Igiyar jikin Chain ɗin dake wuyan karen ya riƙe ya rataya briefcase ɗin ya nufi hanyar fita yana faɗin. “Ke ki fitomin a ɗaki, kizo ki koma inda kika fito ɗakina ba mazauninki bane”. Da sauri tace. “Ina tsoron karenka”. Da sauri ta fito jin yadda ya mata magna a faɗace. “Yana hannuna in baki fitoba zan sako miki shi ya fito min dake waje, ance miki ɗakina matattaran aljanune”. Cikin taka tsantsan da ware ido take taku har ta fito parlour, ganin baya cikine yasa tayi saurin fitowa waje. Da sauri ta koma da baya ganinsa tsaye shida Arda da Yah Saleh Mahmoud ɗin na riƙe da Ketra yana ta zirga-zirga a tsakaninsu, ganin yana riƙe da shine yasa tayi saurin raɓawa gefe can ta wuce da sassarfa ta nufi gidan Yah Saleh. A parlour ta samesu kasan cewar yau ba makaranta su Imran na gida, Zaid da Zaitoon sai wasansu sukeyi a tsakanin su Sajida da su Iman. Numfashi ta fesar a hankali saboda ɗumin parlour ya fara kore mata sanyin waje data ɗebo, Sajida ne ta matso kusa da ita tana jawo hannun su Zaid tace. "Zaid ga Amminku”. ko kallonta basuyi ba gwara Zaitoon ta ɗanyi dariya ta rufe ido. Aunty Maryam da Iman taje ta kirane ta fito Amira na biye da ita a baya. Dai-dai lokacin Yah Saleh ya shigo Mahmoud na biye dashi a baya da Ketra, da gudu Imran ya rungumo karen ya fara shafa shi, ita kuwa Fariyda cikin rawan jiki ta koma can bayan kujerar Aunty Maryam tana karya kai murya a sanyaye tace. "Appiy kallona yake yi fa”. Igiyar ya miƙawa Imran sai kuma ya kalli Zaid dake ta shafa karen Zaitoon kuwa da gudu ta maƙale Sajida tana nuna Ketra ganin haka ne yace. "Imran maidashi wurin Arda”. Cikin jin dadi kuwa ya nufi waje riƙe da igiyar yana kuma kiran Zaid. suna fita ta dawo tsakiyar parlour ta gaida Yah Saleh dake murmushi da faɗin. “Har yanzu baki dena tsoron Ketra ba”. Mahmoud na ɗan kallonta ta gefen ido a ranshi yace. "Hmmm yarinyar da harda suma dan tsoron tsiya”. Maryam ne ta ɓe baki tana kallon Mahmoud ɗin da ko inda take bai kalla ba bare ya gaisheta, sai Sajida daya miƙawa hannu alamun ta miƙo mashi Zaitoon, yana amsarta yace. "Kin basu abinci”. Da sauri tace. “Eh Yah Mahmoud sunci sun ƙoshi”. A daƙile Aunty Maryam tace. “Ni na ɗauka ai suma bazasuci abincin gidanmu ba”. Da sauri Sajida tace. “Ai su da guzurinsu suka zo ko ruwan gidana ban musu amfani da shiba ba abinda babu a babybag ɗinsu”. Fariyda dake gaidata a karo na biyu ta kalla a yatsine tace. “lau”. Yana kallon Yah Saleh yace. “Bari muje”. Cikin kulawa yace. “Bakuyi breakfast ba gashi har lokacin yin lunch ma ya wuce. Maryam ki kawo musu abinci”. Baki ya taɓe tare da jujjuya kai yace. “Bazan ciba”. Da sauri Yah Saleh yace. “Ki kawowa Fariyda ita ai zataci”. A faɗace tace. “Ita ba mace bace ba daga gidan mijinta ta fitoba, nifa na gayama ba abinda zan basu, ta iya aure wa in ya mutu ta aure ƙani, amman bazata iya bashi abinda zaiciba da wanda zataci, ni ba su Ummi bane da zan ƙare a kanta kamar yadda Ummi da Abba suka ga zasu iya su ƴaƴansu duk ita suka haifawa”. Wani kallon da yayi matane yasa ta haɗiye rogowar maganar. “Mu tafi”. Ya faɗa yana kallon Fariyda da idanta ya cika da ƙwalla. “Mu tafi”. Ya kuma faɗa yana kallonta, a hankali ta miƙe tsaye ta bi bayansa. Binsu Yah Saleh da Sajida sukayi har waje, motarsa suka samu a waje Arda ya fito da ita, key ɗin ya karɓa ya kwantar da Zaitoon a baya inda Sajida ta ajiye bag dinsu, Zaid dake ta wasa da Ketra Fariyda tace Arda ya miƙo mata, a baya ta sashi bayan Imran da Iman sun rungumeshi Iman tace. “Aunty yaushe zaku dawo”. Tana ɗan shafa kanta tace. “Anjima kaɗan zamu dawo”. Sai kuma ta ɗan rungume Sajida tace. "Goggo Sajida mun gode babys naki zasuyi missing dinki”. Tana murmushi tace. “Nima na kusa zuwa Nigeria in sha Allah”. Hannu Yah Saleh ya miƙa masa yace. “Sai ka juyo”. Kai ya jinjina mishi kana ya shiga. Ganin ya shiga motane, itama ta shiga gaba. Tuƙi yakeyi cikin nitsuwa da sanin kan garin, tunda ta shigo bai kalli ko ta inda takeba, itama gefe ta rakuɓe ta haɗe jikinta wurin ɗaya saboda jarabebben sanyin garin da ya buwaye ta, ta mirror ya kalli su Zaid da suke wasa. gaban motar kawai take kallo yadda garin yayi luf alamun ana iya fara Snow ako wanne lokacin. Kusan tafiyar 38 minutes sukayi, sannan yayi parking a wani kekkyawan eatiry na alfarma, Hanzade Terrace. daga motocin dake parking space ɗin nasu kasan wurine na hamshaƙan mutane. Su Zaid ya ɗauka ba tare da yace mata ko ƙala ba, ya juya ya nufi ciki, murɗawar da cikinta yayi shi ya sata yi masa biyayyar dole ta fito tabi bayansa tana ƙanƙame jikinta. A hankali suke taka upstairs ɗin. Hammm taja numfashi mai tafe da rawan lips sabida sanyin garin Wurine na alfarma dake bakin teku daga sama kana hango tekun dake shimfiɗe a ƙasa, wanda glass ne yayi musu Garkuwa tsakaninsu da ruwan sai flowers masu kyau da aka zageye wurin dasu sai yan tables masu kyau wasu da kujeru huɗu wasu biyu, inda ya zauna ta ƙaraso ta zauna tana gyara Scarf dinta tare da haɗe hannunta duka a ƙirji manu ɗinsu ya jawo yana dubawa, ɗaya daga cikin ma'aikatansu da yazone ya faɗawa abinda yakeso da abinda su Zaid zasuci. Tambayar ta abinda take buƙatane yasa tayi saurin cewa. “Coffee”. Duk
Chapter 21 · 0% Book details