Sashe 16
Sakar Makafi Part 2 Complete Hausa Novel · about 3 min read
“Farriyyah zafeeh ina su Zaid”.
Da sauri Yah Saleh ya kashe room heater ɗin, sai kuma ya dawo bakin gadon yana cewa.
“Abba Alhamdulillah ya farka”. Miƙa masa wayar yayi, murya a sanyaye yace.
“Abba na warke fa, bari inyi salla zan kiraka”. Miƙawa Yah Saleh wayar yayi yana mai jan tsaki ya miƙe zauna yana faɗin.
“Zan ƙwaƙule idon mutun in ba'a dena min kallon maitaba”. Da sauri Amira tayi ƙasa da kanta ta juyawa ta koma bayan Maryam.
Ita kuwa Fariyda ido ta ɗan zuba mishi cikin sanyi tace.
“Yah jikin da sauƙi ko”. Fuska ya tsuƙe cikin yi mata wani irin kallon yace.
“Ina kika baro min su Zaid”. Da sauri Sajida ta matso tana cewa.
"Yah Mahmoud gasu”.
Zuro sawunsa yayi ƙasa ya shafa kansu haɗi da yin kissing Cheek dinsu da sauri suka abka jikinsa, cikin rashin kuzari ya rungumesu yana mai sunsunar ƙamshi jikinsu da yaji ba irin na kullum bane amman dai ba laifi yana da ƙamshi, turaren waye kika sa musu?”. Ya tambaya, Imran ne ya matso kusa dashi yace.
“Uncle Mahmoud ya jiki turarena ne na saka mata”. Shafa kansa yayi yana kallon Iman dake riƙe da hannun Zaitoon ta gefensa.
Kansu ya shafa da hannu ɗaya, ɗaya kuma na tallaɓe dasu Zaid sai kuma ya kalli Fariyda cikin sauran mayen allurar yace.
“Farriyyha ɗaukesu”. Da sauri ta ɗaukesu tana kallon yadda yake lumshe ido, ganin Yah Saleh zai tallabeshi ne yace. A'a a barshi zai iya.
Haka kuwa ya shiga bathroom yana shiga
Yah Saleh ya kalli Fariyda yace.
"Fariyda kije Arda ya kaiki gida ki samu kiyi wanka ki ɗan huta sai ki dawo”.
Sai kuma ya kalli Arda cikin bada umarni yace kuje ko?”.
Kai ta gyaɗa kana suka fita. Su kuwa su Sajida
duk suka fito parlour
Sai Yah Saleh kawai.
Bayan ya idar da salla, a hankali ya zauna kan gadon saboda shigowar Doctors ruwa aka kuma ƙara masa da sa mishi allurai a ciki da dai sauran kulawa. Bayan sun fitane.
“Mahmoud asa maka abinci ko”. Aunty Maryam ta faɗa tana kallon Amira data shigo da basken ɗin foodflacks a ciki sai ɗan flacks ɗin tea da cup, plate, spoon, fork. Kai ya jujjuya cikin lumshewar Ido hannu ya miƙawa Sajida.
Da sauri ta miƙa masa Zaid kontar dashi yayi bisa kirjinsa sai kuma ya jawo Zaitoon ɗaya gefen itama ta.
Lumshe idanunsa yayi ba tare da ya kuma cewa komai ba.
Ganin haka ne yasa sukayi zaton bacci yake yi shi yasa Yah Saleh amsar car key ya tafi gidan dan ya samu yayi wanka ya ɗanci abinci.
Parlour suka dawo suka zauna.
Sajida na gefe tana waya da Ummi ta wayar Hafiz da ya kirata cikin alamun shaƙuwa sosai tsakaninta da yayar mahaifiyar tata Ummi kenan take jaddada mata jikinsa da sauƙi sosai.
Amira kuwa ƙusƙus sukeyi da Aunty Maryam akan burinta na mallakar Mahmoud.
Da sauri suka juyo saboda jin ni'imtaccen sassayan ƙamshi mai daɗin shaƙa daya ziyarcesu.
Cikin takaici Amira tayi ƙasa da kanta ganin Fariyda ne ta shigo Arda na biye da ita a baya da ɗan babybag a hannunsa. Aunty Maryam kuwa cikin zafin kishi wa ƙanwarta da hasada take kallon Fariyda sama da ƙasa sanye take da wonɗo royal blue jeans sai sweater shima blue mai kyan gaske sai white Scarf data naɗe a wuyanta da ɗan farin jersey veil datayi rolin kanta da babban long coat mai ɗan girma dan ya wuce guiwarta shima irin ɓaki mai sheƙin nan, ido ta tsaida kan takalmata da sanin kuɗinsu yasata jin malolon hasada ya shaƙeta coat ɗin da yake wani irin sheƙi ta harara sai kuma ta maida ido ta kan fuskarta da tayi masifar kyau duk da idanunta na kumbure.