Sashe 66
Sakar Makafi Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Yan latse-latse yayi na kusan 13 minutes sai kuma ya kife wayar dan ciwon marar da ya murɗa masa, a ƙalla 6 minute kafin ya kuma ɗagowa daga kafuwar da yayi cup ɗin lemon tea dake kan bedside drawer wanda ya sha tun ɗazu haka kuma bai hana shi ƙara jin ciwon bane yasashi yin kwaffa yana yakice abin a ransa ya kuma ɗaukan wayarsa ya shiga WhatsApp abinda bai wani damu da shiba, hotuna da videos sabbin kayansu da ya saro a Istanbul da suka iso a satin nan Hafiz yayi masu tallarsa kamar yadda da Mahmoud ɗin keyi, duba hotunan da videos ɗin yake yi ɗaya bayan ɗaya sosai aikin Hafiz yake kyau musamman abinda ya shafi hoto da ado da kwalliyar tallafa musu kaya dan shi ya iya maɗe kamar mace, ido ya lumshe cikin gajiya da farajin bacci ya juya wayar da nufin ajiyewa sai kuma ya juyota ganin kamar Hafiz ɗin yasa abu status nashi dannawa yayi ya fara kallo. Da sauri ya miƙe zaune yaci gaba da kallon duk abubuwan dake kan status nashi. Miƙewa yayi ya nufi ƙasa, a parlour ya samesu harda Aunty Amina da tazo da yamma sai Hafiz dake tsaye da key a hannunsa alamun zai maida maman nashi. Da sauri ya dafe kuncinsa yana mai ja da baya saboda bahagon marin da Mahmoud ɗin ya watsa mishi, da sauri Ummi da Goggo Dada sukayi kansa suna faɗin. "Ha'a Mahmoud lfy kuwa? me ya faru? Me yayi?”. Rai a ɓace ya fara nunashi da yatsa cikin tsawa yace. “Baka da hankali ko? Wai kai Hafiz sai yaushe zaka san banbancin haram da halal ne”. Da sauri ya fara jujjuya kai yana faɗin. "Uncle kayi haƙuri wlh ban san me nayi ba”. Amina ta watsa mishi harara tace. "Ta yaya zakace baka san me kayi ba”. Huzaifa kuwa gefe ya koma ya tsaya, Hafiza da Samira kuwa ɗakin Goggo Dada suka koma. Wayarsa ya nuna masa a hatsale yace. “Har sai yaushe zaka san ba komai ake sawa a status ba ka tallatashi a banzace ko wani jaki da doki ya gani kai baka san haramcin bane”. Da sauri Amina ta jawo wayarta ta shiga WhatsApp status ɗin Hafiz ta shiga. Hoton Fariyda ta fara cikin karo dashi wanda Hafiz yayi mata ranar da zasuje gidan Bappa Lawan a ƙasa ya rubuta irin yadda sukayi missing nata ita dasu Zaid ya ƙara da cewa tunda suka tafi gidan ba daɗi shima zai koma gidansu, sai kuma screenshot na comments ɗin mutane akan kyanta harda masu cewa suna sonta duk ya ɗaura yana cewa. Our Aunty kina wutafa”. Cikin tsoron ko wani mugun abu Hafiz ɗin keyi a social media Ummi tace. “Kallon banza yake yi ko”. Rai a haɗe Amina tace. “Bashi da hankali ne ya ɗauki hotunan Fariyda ya saka a status nasa, bayan ya sani ko nashi danasu Hafiza da Huzaifa ina hanashi sawa sabida gudun bakin jama'a ta yaya zai sa na Fariyda in banda rashin hankali da sakarci”. Ta ƙare maganar tana fizge wayar Hafiz ɗin ta fara Delete ɗin hotunan baki ɗaya, tana kallon Mahmoud tace. "Na gogesu”. Ajiyan zuciya mai nauyi ya sauƙe kana ya juya ya fita ba tare da yace komai ba, Ummi kuwa da harara ta rakashi Goggo Dada kuwa murmushi tayi tana kallon Amina da itama Murmushi takeyi harda jijjiga kai da ɗaga gira, shiko Hafiz da yasha mari da faɗa a hankali yace. “Mom muje in maidaku”. Daga nan suka fita. Numfashi ya rinƙa sauƙewa wani na korar wani yana kallon kiran Sa'ad da Faisal da suke ta jerenge in wannan ya kira yana katsewa kiran wannan zai shigo. A kufule yace. “Zanci uban ubanku yan iska mayun mata da shegun fuskoki kamar na birurruka ina nan tafe gareku ƙananan yan iska. Washe gari da safe. Ido Ummi ta zuba mishi ganin yadda ya shigo riƙe da ɗan ƙaramin hand lounge sai briefcase nashi. “Sai ina”. Goggo Dada ta tambaya tana kallonshi sama da ƙasa da fuskarsa data nuna babu wata matsala ko damuwa tare dashi. "Gombe zanje”. Ummi tace. “Gombe kumwa”. Yana kallon Huzaifa dake gaidashi ya amsa sannan yacewa Ummi. "Eh”. Goggo Dada tace. "Lfy dai kam ko?”. Kai ya gyaɗa mata ya ɗaura da cewa. "Eh wani ɗan aiki zan taya Sulaiman kwana biyu zanyi zan dawo”. Kusan a tare sukace. "Allah ya kiyaye hanya ya kaika lfy ya dawo da kai lfy”. Amin Ya Allah yace ya juya ya bar gidan kai tsaye gidan Baba Malam ya wuce. Cikin kulawa Malam yake kallon yadda yake ta sunsunar su Zaid yana kissing nasu, sai kuma ya ɗan kalli Zaitoon a hankali yace. "Ina Ammey”. Dariya tayi tare da jujjuya mishi kai tana ƙara kwanciya a jikinsa, shafa kan Zaid yayi haɗi da cewa. "Zaid ina Mamanku”. Ido Baba Malam ya zuba mishi yana karantar yanayinsa da yadda ya zama a kwanakin nan. Kanshi ya ɗan ɗago ya kalli Malam ɗin yana mai kuma kiran layin Fariyda da rashin ɗaukar wayarsa yasa shi fara jin fusata kan su Sa'ad. "Kamar tafiya zakayi ko”. Malam ya tambaya, kanshi a sunkuye yace. "Eh zan ɗanyi tafiyar kwana biyu ne”. Yana miƙa masa hannu yace. "Kawosu to kada lokacin ya ƙure maka”. Miƙa mishi yana ɗan yin ƙasa da kanshi a hankali yace. "Malam mamansu fa?”. Cikin kauda kai Baba Malam yace. "Sun ɗan fita ita da Saddiqa”. Fuska tamkar zai yi kuka yace. "Malam ina suka je”. Kai ya ɗan jujjuya cikin bada umarni yace. "Mahmoud tashi kaje. Allah ya kiyaye hanya”. Mamy da tun da suka gaisa bata kuma cewa komai ba ne tayi ƙasa da kanta cikin sanyi yace. “Mamy zan tafi”. Cikin sonshi tamkar ɗa na cikinta da jin ciwon rabuwarsa da Fariydan tace. "To Mahmoud Allah ya kaika lfy ya bada sa'a”. Yana miƙewa yace. “Amin ya Allah Mamy ngd”. Daga nan ya juya fita. Jirgin ƙarefe takwas yabi zuwa Abuja yana isa ya sake bin jirgin Abuja to Gombe kafin sha ɗaya dai tayi masa cikin Gombe. Washe gari da yamma. Mama da Jidda ne zaune da Yah Ahmad da Salim lissafa musu abubuwan da jidda ke buƙata takeyi sai kuma suka kalli Jidda dake miƙawa Yah Ahmad ɗin takardar data gama rubuta duk irin kaya da collors da takeso. Taɓe baki kawai Salim yayi Yah Ahmad kuwa sarkin sauki kai nan take ya fara tura kuɗin wasu ababe. Salim yayi kwaffa yace. "Kunje kunyi gwajin ne? Waima tukun Mahmoud yasan da mgnar nan”. A kufuli Mama tace. “Ras ma kuwa ya san da ita ubansa ya gaya mishi, gwajin kuma Abba da kansa ya gayawa Babanku Mahmoud zaiyi tafiya jiyan”. A gidan Malam kuwa Yah Mujahid ne zaune a parlour Mamy shi da Fariyda dake ta mishi sannu duk da hannun ya saɓe ba kumburin amman baya iya komai dashi, baki kuwa har yanzu ba haƙorin. "Sai yaushe zakaje a sama haƙori Yah Muhajid”. Yana murmushin da yasa giɓinsa bayyana yace. “In sha Allah na kusa sawa naje asibiti sunce sai wurin ya ƙara warkewa”. A sanyaye tace. "Allah ya ƙara sauƙi”. Amin Ya Allah Ya faɗa yana ɗan dawowa kusa da inda take tafiyarsa take kallo ganin yadda yake ɗan ɗinƙisa kafa kaɗan da sauri ta matsa can gefe tana gyara rufe jikinta kab da ƙaton hijabin da ta rufu dashi. Dai-dai lokacin Aunty Aisha ta shigo tana ganinsa cikin wasan yar kawu tace. "Kai Mujahid wai karo kayi da tifa ne ko tirelane ya bangajeka”. Harara ya watsa mata yace. “Ban sani ba”. Dariya tayi tana kallon Fariyda dake mata sannu da zuwa. Aisha na wucewa ɗakin Mamy yace. “Zuwa nayi muyi magna my dear ni so nake a ɗaura aurenmu rana ɗaya dana Raihana in yaso sai na ƙara sauƙi sai muyi namu bikin”. Fariyda tace. "To Yah Mujahid ai wannan da mgnar Malam ce, kuma ya yanke hukuncin sai ka warke, Please kayi haƙuri ka bar min wannan maganar har sai ka samu lfy kaza zamuje bikin Raihana ma shine a gaba”. Yana murmushin yace. “Sosai ma kuwa, in na ƙara sauƙima ni zan kaiki da kaina”. Cikin jin takaicin dabaibayin da Mahmoud ya mata da gujewa shiga fushin Allah da iya kallonsa a matsayin ɗan uwanta tace. "Yau saura kwana tara in sha Allah kafin nan ka ƙara samun sauƙi”. Shigowar Hafiz da Huzaifa ne yasa Mujahid ɗin haɗe fuska kana yace mata in sun tafi yana jiranta a BQ dinsu. Kayyakin da Mahmoud ya haɗa a turawa su Zaid ne da duk wani abun da zasu buƙata su Huzaifa suka shigo dashi nan sukayi ta hira har sai gab magrib suka tafi. Bayan sun idar sallan ishane suna zaune sun sa kayyakin a gaba, wasu irin datsatstsun Abaya na alfarma ne a ƙalla guda bakwai ko wanne da kalarsa da takalminsa da yar jakarsa sai turaruka masu mafar sanyin ƙamshi sai hijabai manya-manyan har bakwai suma irin masu har ƙasan nan sai laffaya suma bakwai Aunty Saddiqa tace. “Hmmm wannan salo naku dai kam ana cin uwar kuɗi ana kuma ƙonawa juna zuciya ranar da zaku gane ɗaya bazai rayuba saida ɗaya dole mu ja gefe mu zama yan kallo Mahmoud kuwa Allah yasa kada kishi ya kashe mana shi wannan matakan tsaro duk na menene bayan anyi saki kalli fa ashe harda niƙab”. Kwaffa tayi tana amsa kiran. Aunty Khadijah. Su kuma sukaci gaba da kallon kayyakin su Zaid Adda Nana na leka fuskar Fariyda tace. “hmmmm nifa abun sun yana ɗaure min kaifa”. Wuraren ƙarfe goma na dare. Adda Nana da tun jiya itama tazo da shirin sai bayan bikin ta koma. Ta shigo ɗakin Aunty Saddiqa ta samu zaune tasa Farriyyha a gaba da dahuwar kaza mai kyau sai turiri takeyi. "Ki cinye shi fa Fariyda abu tun safe kin kasa cimyewa Raihana ma tuni ta cinye tata amman ke sai gardama kuma dai kinsan dole ne”. Gyatsa tayi a hankali tace. "Aunty Saddiqa ni ba son abubuwan nanfa nakeba. naji kuna cewa wai yana cike mace”. Da sauri Aunty Saddiqa tace. "A'a ai nasan yadda kike ke haɗin dahuwar na ni'ima akayi miki ai nasan matsalarki duk abubuwan da zai taimaka miki nasa akayi miki”. Tana rufe bowl ɗin tace. "To ni daba aure