← Book details Sakar Makafi Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 8 OF 95

Sashe 8

Sakar Makafi Part 2 Complete Hausa Novel · about 5 min read

samu sauƙin wucewa a Airport. Washe gari da safe. Zaune yake a parlour video call yake yi da Abbansa. “Eh Abba na biya komai duka lissafi har ma da kuɗin dawowarmu”. Ɗan juyowa yayi saboda jin muryar Zaid na faɗin. “Appey”. Numfashi ya fesar yana shaƙan wani a hankali sabida ƙamshin dayayyi parlour mamaya. Ita kuwa Fariyda hannun Zaid da take son bawa maganin yana ƙine ta miƙo mishi dan yaƙi nitsuwa ya karba daga ƙasa yake kallonta ta gefen ido cikin tattausan riga da wondo Turkish take purple color mai masifar kyau da sulɓi mai taushi tayi Rollin kanta da Jersey veil sai takalmin snicker Black color dake ƙafarta, hannun Zaid ɗin ya kamo yana kallon Abba dake cewa. “Yau ɗin ƙarfe nawa zaku tashi”. Cikin girmamawa yace. “10:00 AM flight ɗinmu zai tashi daga Ahmedabad zuwa New Delhi, a can kuma ƙarfe biyu dai-dai zamu tashi zuwa Istanbul.” cikin mmki take kallonsa kenan ma yau zasu koma, amman bai gaya mataba bare ta shirya da bataji yana mgna da Abba ba to tafiya zai yi ya barta kenan”. Time ta duba ganin ƙarfe 8:46 Am cikin mmki tayi sassayan numfashi saboda jin sauƙin shirin. Da sauri ta kalli inda travelling box ɗinsa yake to dama kullum a kimtse yake system nashi ta kalla ganin komai nashi ya tattare ya haɗa kib da kib. Da sauri ta juya tayi bedroom sauri-sauri ta fara haɗa kayanta dana yaran, samun ƙarin kayyakin da ya sayawa yaran yasa dole sai da ta ɓata lokacin wurin kimtsasu yadda zasu zauna, ajiyan zuciya ta sauke tace. “Shiyasa jiya da na fita yasa aka tattere duk kayansu aka wanke da dare aka dawo dasu a goge. Knocking ɗin da taji anayi Babu ƙaƙƙautawa, ne yasa ta fito parlour da sauri saboda jin ba'a denaba wayam parlour ba kowa, ba komai nashi da sauri ta buɗe ƙofar driver sune ya ɗan kalleta cikin ɗan rusunar da kai ya gaidata yace, tayi sauri ta fito kada suyi missing flight. Da sauri tace ya shigo ya ɗauka mata akwatin haka kuwa ya shigo shi ya taimaka ya rufe mata akwatin kana suka fito. Alhamdulillah sun bar Ahmedabad lfy sun isa New Delhi cikin Aminci. Ƙarfe biyu saura kwata suka shiga cikin babban jirgin Indian Airlines. Ƙarfe biyu dai-dai jirginsu ya ɗaga ya ɓar ƙasar India zuwa Turkish. Numfashi mai sanyi ta fesar lokacin da taji sun gama dai-dai a sararin subahana, jirgi ya na keta hazo a matakin gudu na musamman. Ido ta ɗan jujjuya tana ɗan ƙarewa first class ɗinsu kallo wanda ya tsaru iya tsaruwa, tsaida idonta tayi a kanshi saboda ganin yadda yake datse lip ɗinshi na ƙasa da sauri-sauri ya manna kanshi jikin seat ɗin yayi lip sai numfashi yake fesarwa a hankali, su Zaid dake kwance a jikinsa tuni suke bacci cikin aminci. Kai ta jingina ta lumshe idonta dan baccin safe da batayi ba na dawo mata. Kai ya fara jujjuyawa a hankali dan wani irin birkitaccen yanayi da yakeji a jikinsa, da sauri ya meda idonsa ya rufe saboda jirin da yake fizgarsa in ya buɗe idonsa gani yake komai na jujjuyawa. Cikin baccin da ta fara taji muryarsa can ƙasa. “Ke! Ke!! ɗagasu kwantar dasu”. Buɗe ido tayi tana gyara zamanta ganin ɗaya daga cikin flight Attendance ya ware seat ɗin su Zaid ya sa musu blanket ɗin yara, kanshi ta sunkuyo ta ɗauki Zaitoon ta fara kwantar wa, ita kuma ma'aikaciyar jirgin ganin yadda goshin Mahmoud ke tsatstsafo zufa ne yasa ta ƙara masa gudun AC, tare da tambayarsa me yake buƙata kai ya jujjuya mata alamar a'a dan baya jin zai iya magna, Fariyda dake kwantar da Zaid ta kuma tambaya take buƙatar, tana gyara zamanta tace sai anjima dan ɗan abin da sukaci a flight ɗin Ahmedabad to New Delhi ya wadaceta ita da yaran duka shiyasa sukayi baccinsu. a hankali ta juyo ta inda yake jin kamar ana mgna, baki ta taɓe ganin idonsa a rufe zufa na ɗan tsatstsafo mishi kaɗan Sai kuma lips ɗinshi da yake motsawa wanda sai duk da kasa kunne bataji me yake faɗa a sambatun da yakeyi. Meda kai ta jingine taci gaba da baccinta da bata samu tayi na safeba, hannunsa duka biyu yasa ya tallaɓe cikinsa da yake masifar murɗawa wanda hakan ke jawo masa jin zafi duk da sanyin AC, bayan 30 minute cikin na murɗawa sai kuma yaja numfashi mai sanyi Saboda jin ya lafa, haka ya rinƙa yi masa ya murɗa 30 minute Ya lafa 30 minute. Buɗe ido tayi tana mai kallonshi zaune riƙe da wayarsa yana danne danne kamar ba shiba wayarta ta duba ƙarfe 6:00 Pm sunyi awa huɗu kenan a sama saura musu 2 hours and 40 minutes su isa, su Zaid dake wasa akan seat ɗin su ta ɗan kalla sai kuma ta meda hankalinta kan Flight Attendance ɗin da suka fara raba musu abinci for dinner. Sosai taji daɗin abincin nasu haka yasa ta ɗanci abinda zata iya ci. Daga nan suka zo suka tattare komai, ganin ya gyara zama ya kabbarta sallah ne yasata fahimtar magrib tayi kenan, lavatory ta nufa dan sabunta alwalarta tunda tayi dogon bacci mai nauyi. Salla tayi kamar yadda taga yayi. Tana cikin sallan taji ya fara sammatu fiye da na ɗazu ma, har yanzu bata iya jin me yake faɗi, bayan ta idar ne ta ɗan kalleshi ta gefe, kar-kar jikinsa ke rawa kuma ga zufa, hannunta ta ɗaga don yin addu'a har ta shafa bata daina jinsaba, a hankali ta ɗan juyo kansa tana tuno ɗan taimakon da yayi mata ranar da mararta ta kusan hallakata, a hankali tace. “Baka da lfy ne”. Shiru ba magna sai numfarfashi da yake ja da ƙarfi, ɗan ɗaga murya tayi tace. “Baka da lfy ne? Meke damunka?”. Baki ta ɗan tura sai kuma tace. “Ina ma magna ka shareni”. A hankali ya buɗe idonsa da sukayi masifar ja tamkar zasuyi aman wuta da sauri ta janye idonta tana faɗin.....
Chapter 8 · 0% Book details