Sashe 60
Sakar Makafi Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Kan cikinta, murya a sanyaye yace. “Farriyyha kina jin nakeji”. Ƙarfin Alluran da akayi mata da gajir da ya tara mata ga kukan da ya galabaitar ne suka haɗe suka diro mata mutuwar jiki da kasala haka nan taji idonta na lumshewa. “Farriyyha Mamy da Malam suna fushi da ni ko?”. Ya faɗa yana ɓalle marfin goron Admiral ɗin ya kai matashi bakinta. Kai ta jujjuya mishi ido na zubda wahaye sake kai matashi bakinta yayi haɗi da cewa. "Please dan Allah kiyi haƙuri kisha kar yunwa ta cutar min dake”. Ture hannunsa tayi tana yunƙurin tashi haɗe da mishi kallon dake nuna tsanar zama kusa dashi. Ajiye goran yayi haɗi da jawota ya manna bayanta da ƙirjinsa ya riƙeta gam a sanyaye yace. "Mamy na fushi da niko”. Tana janye hannunsa ta gyaɗa masa kai alamun eh. Cikin yace “Dan Allah in kin je ki basu haƙuri kice su yafe min kada suyi fushi dani”. Ya ƙare maganar yana manna lips ɗinsa kan wuyanta Ummi tacewa Amina. “Me ya tsaidaku ne haka bayan naga tunda Dr Fadil ɗin sun tafi, kuma tun safe su Hafiz sun gama sauƙar da kayanta har Hafiz ya kaisu ya dawo,Ina Fariyda Abbanku na jiranta fito da nace masa sunyi baƙine yace to a barsu gashi yanzu kuma har azabar tayi”. Cikin rashin sanin abin faɗi tunda Mahmoud ɗin ya gargaɗeta karta faɗa musu komai yasa a hankali tace. “Tana zuwa”. Goggo Dada tace. “Ko karyawa batayi bafa”. Kije kice mata tayi sauri ta fito”. Tana jawo jakarta jin wayarta na ringing tace. "Toh”. Tattaro dukkan ragowar ƙarfinta tayi ta fizge jikinka daga gareshi, jiki na rawa ta sauƙa daga kan gadon fuska a tsuke har lau ido na zubda ƙwallan murya a dishe tace. “Ka bani wayata ni zan tafi gidanmu”. Shi kuwa Mahmoud wayar da kiran Muhajid ya shigo yake yiwa wani irin kallon zuciya a tafashe ya cilla mata wayar yana miƙewa tsaye yace. "Kifi ruwa tafiya duk dai inda zakije da igiyar aurena a kanki, in kinje gidan nakuma kada Allah yasa ki tsaya ki wuce gidansu jakin da yake kiran naki nan zan san baki da hankali shi kuma duk abinda nayi masa shi ya jawa kansa wlh duk motsinki idona na kanki in ya kuskura ya zo inda kike sai na hanashi ganin hasken rana ma bare ya ƙara kallon matar wani ma bare tawa”. Ya ƙare maganar yana nuna mata hanyar fita, tsaki taja tare da murguɗa baki ta juya ta fita tana taune lips ɗinta, idonta na kan wayar kallon text ɗin da yayi mata ta wayar Yah Amin bata buɗe ba taci gaba da tafiyar tana jin sukan zazzaɓi na ɗan sauƙa dan allurar da akayi mata dana kashe zogin sun taimaka mata sosai. Tare da Amina suka shiga parlour Abba bayan Ummi tasa sun ci abinci gaidashi sukayi kana suka bi bayansa. Ganin ya miƙe ya fita, rungumeta Ummi tayi ido cike da ƙwalla tace. “ina sonki Fariyda bakuma zan daina sonki ba har gaban abadan, amman ƙaddara ta rabamu”. Itama hawayen na zuba ta rungume Ummi haka dai suka rabu kamar yadda suka rabu lokacin rasuwar Aminullah. A gidan Baba Malam Mamy da Aunty Amarya da Abba da Uncle Sani bappansu Fariyda ne zaune a parlour Malam ɗin Abba yana tausarsu da shaida musu Babu laifin Fariyda a mutuwar aurenta. A can cikin gida kuwa. Fariyda ne dasu Zainab Raihana da Humaira sai matar Yah Nasir duk jugun sukayi ba wata wal-walar tare dasu tun da Hafiz ya dawo da kayanta, tana zama ta zame ta kwanta tayi pillow da sawun Aunty Saddiqa sai kuma ta kamo hannun Aunty Saddiqa tace. “Ya jikin Yah Mujahid yana asbiti ko? Muje mu dubashi da jiki Aunty Saddiqa”. Mamy dake shigowa ne ta danna mata harara cikin takaicin mutuwar auren da har ranta take son Mahmoud ɗin a matsayin surkinta rai a ɓace tace. “Ki nitsu ki gama iddar kafin ki fara batun yawon dubiya ki sani yanzu ba inda zakije har sai kin sami sahalewa da yardar Mahmoud”. Kai ta longwaɓar cikin sanyi murya a dishe tace. "Mamy ya sakeni ma sai na nemi izininsa”. Kwaffa Mamy tayi tace. "Tabbas kuwa dole har sai kin gama iddarsa”. Ta ƙare maganar tana shigewa bedroom ɗinta rungume dasu Zaid da Abba ya batasu da kanshi. Ita kuwa Fariyda da sauri ta kalli Saddiqa dake cewa. "Mu fa yau gidan nan ba wani farin ciki tare damu Fariyda mutuwar aurefa ba wasa bane, naga kamar farin ciki kikeyi har kina mgnar zuwa duba wanda yayi miki sanadin mutuwar aurenki”. Fuska ta kwaɓe cikin son fahimtar dasu tace. "Aunty Saddiqa nifa ba wani bani da sauran matsala tunda ya sakeni ai shike nan ya kema kina mgna kamar baki san komai ba, Yah Mujahid kuwa wlh ba shi yayi sanadin mutuwar aurena ba, dama can yana da niyar saki nima kuma ba son zama dashi nakeyi ba”. Shiru tayi jin Mamy na cewa. “Ci gaba da rashin kunyar ai dama ni na sani ruwa baya tsami banza”. Shiru tayi tana yin ƙasa da kanta saboda ganin kallon da Mamy keyi mata, Aunty Sadiya matar Dr Nasir ta ɗan numfasa tace. "Wallahi ni duk jikina yayi la'asar nama rasa abin faɗi”. Humaira na kallon Fariyda tace. “Ni wlh su Zaid ne suke bani tausayi a rabuwar auren nan”. Raihana da tuni ido ta ya tara ruwa tace. "Wallahi nima abinda nake tunawa kenan, nasan tabbas watan wata rana Yah Mahmoud zaisa a karɓesu.” tana yin ƙasa da murya yadda Mamy bazata jitaba tace. “Ai kuwa dole ya bar min su tunda bashi ya haifa min suba, kuma su Abba da Ummi ma sun yarda a barmin su ni dashi kuma haihata-haihata”. Kwaffa Saddiqa tayi ta miƙe ta shiga bathroom ɗin su Raihana inda suka jera kayan Fariyda da yaranta. Washe gari da yamma Dr Nasir ne zaune bakin gadon Mamy gefen Mamy Fariyda na zaune a ƙasa. “Mamy muyita addu'a kawai Allah yasa hakan shi yafi alkhairi, Amman batun daɗi kam ai abin bai mana daɗi ba, ni nasan waye Mahmoud wlh yana da nagartar da ita kanta Fariyda bata saniba sai yanzu da suka rabu zata gane, shine Garkuwarsu ita da yaranta, a cikin ƴan uwa dubu kaɗan ake samu irin Mahmoud masu nagartar kula da tarbiya da rayuwar ƴaƴan yan uwansu bayan ransu”. Cikin ɓacin ran da har yanzu bai bar zuciyar Mamy ba tace. "Ai ita da yake bata san abinda ake duba mata ba, har farin ciki takeyi da sakin mutumin da yake son ƴaƴanta fiye da kowa a duniya, tana farin cikin zata auri Muhajid, hmmmm ba komai Allah ya tabbatar da alkhairi”. Amin yace yana kallon Fariyda a tausashe yace. "Wai Sadiya tace min baki da idarsa?". Da sauri ta gyaɗa kanta tace. “Eh kuma su Abba ma sun sani Malam yasani”. Cikin sanyin jiki yace. "Shike nan ai, Allah ya bawa Mujahid ɗin lfy, in hannun ya ƙara sauƙi sosai dai sai a ɗaura muku auren tunda dama shi yana sonki kema kuma yanzu kin amince dashi nima kuma na gamsu zai riƙe miki yaranki bisa amana dan nasan son gsky Mujahid keyi miki, yanzu ma muka gama magnar da Malam yace ba don karayar da Mujahid ɗin ya samu da jinyar haƙora biyu da Mahmoud ya zubar masa ba, da rana ɗaya za'a ɗaura aurenku da na Raihana”. Numfashi mai nauyi Mamy ta sauƙe tana kallon Fariyda da tayi ƙasa da kanta cikin yanayi farin ciki a can ƙasan zuciyarta kuwa abinda ya faru ke mata yawo a zuciya tsoron duba text ɗin da ya mata takeji ta kuma kasa tuna menene abinyi akan abinda yayi mata bata jin kuma zata iya gayawa kowa wannan abun lallai wannan shine SAƘAR MAKAFI yees SAƘAR MAKAFI mana to ita kanta bata san menene mafitaba a kanta dan ya rigada ya gama mata dabaibayi abu ɗaya dai da tasani duk rintsi bazata koma gareshiba dole sai ya tabbatar da sakin nan a karan kanshi. Salim ya zubawa Salma ido ban ya faɗa mata abinda ya faru na mutuwar auren Fariyda sai kuma ya gyara zamansa jin tana cewa. "Innalillahi ta ya su Abba zasuyi haka yah Salim meyasa baku hanasu raba auren nan ba ko dan su Zaitoon”. Kiran Sulaiman da ya shigo wayarsa ne yasa bai amsa mataba. “Ato Alhamdulillah Barka da isa lfy, ya Gombe da mutanen Gombe duk ka samesu lfy ko”. Salim ɗin ya faɗa bayan ya amsa kiran Sulaiman da ya koma Gombe yau. Jim kaɗan yayi kana yace. “To a huta gajiya”. Yayi magnar yana kallon Salma data kira Fariyda suna magna daga bisani tace in sha Allah gobe zanzo in yah Salim ya barni. Bayan kwana uku tun ranar da abun nan ya faru bai sake shigowa parlour Ummi ba, iya karsa parlour Abba in sun dawo sallan asuba anan yake gaida Ummi da Goggo Dada. “Har yau fa baya cin abinci, yadda Hafiz ke kai masa haka ya ɗaukowa da alamun ko taɓawa bayayi”. Goggo Dada ta faɗa tana amsar Tray da Hafiz ɗin ke miƙa mata. Ummi tace. "Ni ai cewa nayi ki fita harkarsa, ki daina mishi girki ba dai yayi yadda yake soba ya samu nasarar sawa a bashi izinin sakin Fariyda, ni bazan ƙara shiga kitchen dan yi masa girki ba, in ya damu ya nemi mata yayi aure ta rinƙa mishi girki”. Hafiz ya ɗan juya ya kalli bayansa a hankali yace. "Ai Mom na turo masa abinci, kullum in Huzy zai zo yana zuwa masa da abinci”. Kwaffa tayi tace. "Ai wato Amina ko ya zanyi sai ta nuna min sunfi kusa, na lura ita tausayinsa takeji bayan koma menene shi haka yakeso kuma tsarinsa ne”. Goggo Dada tace. “Naji ai Abba na cewa zasu tada mgnar aurensa da Jidda”. Rufe ƙofar bedroom ɗin tayi tana jujju kanta dan ta tabbatar ba kowa a ɗakin. Kiran da a ƙalla shine na 23 da yayi mata tunda jiya zuwa yau amsa kiran tayi tana faɗin. "Nifa ka daina kirana bana so, ka rubuta min shaidar sakin da kayi min ka bawa Hafiz ya kawo min shine yasa na amsa kiranka”. Ɗan guntun Murmurshi gefen baki yayi haɗi da cewa. “Hafiz zaizo ya