Sashe 72
Sakar Makafi Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read
A hankali suka shiga cikin ɗakin da Mahmoud yake, bisa jagoranci Sadiq. Kusan duk tsayuwa sukayi tamkar an dasasu saboda hagonshi zaune a tsakiyar ɗakin akan tattausan Turkish carpet yana jingine da kujera, Salim na kan kujerar Amina na gefenshi ido cike da kwalla. Hafiz da Huzaifa na gefe a hankali Sadiq yace. “Innalillah abin ya sake tashi ne kuma?”. Hafiz ne ya gyaɗa masa kai cikin raunin. A hankali Adda Nana Saddiqa da Khadija suka matso kusa haɗi da gaisawa da Amina da Salim suna kallon yadda ya sa hannunsa duka biyu ya damƙe mararsa dake barazanar darewa, wani irin masifeffen ƙarƙarwa jikinsa keyi har lips ɗinshi rawa suke yi duk jijiyoyin jikisa manya da kananan sunyi ruɗu-ruɗu More Especially na hannunsa da kanshi. A hankali Amina ta juyo ta inda Fariyda ke tsaye jin sassayan sautin numfarfashi mai tafe da bayyana tsorom da take dannewa. Sai kuma duk suka juyo kanshi saboda jin Salim na faɗin. "Innalillahi Aunty Amina aje a kira Doctor suzo kawai su mishi aikin nan kinga ya fara irin abin jiyan nanfa”. Da sauri ya fara jujjuya kai alamun a'a, haka yasa sukayi shiru suna kallon yadda ya naɗe wuyansa ya juya hagu da dama, hannunsa ya ɗago a hankali ta inda yake jin ƙamshin turarenta ya fara yafitowa yana mata alamun tazo, ido cike da rauni ta lumshe sai kuma ta buɗesu a hankali jin Amina na cewa. "Fariyda ke yake kira”. Adda Nana da Saddiqa na haɗa bakin cewa. "Kije ke yake kira”. A hankali ta rusuna gefenshi murya na rawa tace. "Appiyn ya jikink”. Sai kuma tayi shiru bata ƙara mgnarba jin yasa hannunsa ya kamo hannunta haɗi da fizgota jikinsa kan ƙirjinsa ya matseta yayi mata rungumar dake nuna azabar ciwon da yake ji. Da sauri su Adda Nana suka kalli juna. cikin sanyi ta fara kiciniyar kwace kanta amman ta kasa dan ba riƙon wasa yayi mataba. Dai-dai lokacin Dr da Jidda taje kira tun kan zuwan su Fariyda, suka shigo a tare da Nurses biyu, Dr ne suka ce su fita su basu wurin haka yasa su Adda Nana dasu Hafiz kab juyawa suka fita. Jidda tunda ta shigo ta sameshi rungume da Fariyda fuskanta ta koma tamkar zata yi aman jini. Dr ne ya kuma cewa a bashi wurin haka yasa Amina miƙewa tana faɗin. "Dan Allah Mahmoud ka bari ayi maka aikin nan na roƙeka da girman Allah ka rufa mana asiri rayuwarka fa nada mahimmanci a garemu dan Allah ko dan kwanciyar hankali su Ummi”. Salim ne ya watsawa Jidda harara yace. "Ke uwar me kike jira”. Cike da takaici tace. “To ai itama sai ta taso mu fita, me haɗinta dashi da zata maƙale mishi”. Hararan da Salim ɗin ke auna mata yasa ta juya zata fita juyowa tayi jin Dr na cewa. “Eh itama wannan ɗin ta fita, dan dole muyi mishi aikin nan yanzu Dr Sisila tana zuwa tayi masa aiki”. Da sauri Salim yace. “Wannan ɗin matarsa ce ai”. Ya ƙare maganar yana nuna Fariyda da watsa Jidda kallon da yasa dole ta fita taja ƙofar cike da takaici har tana jin zuciyarta na fara mata kokonto anya Salim yana sonta matsayin yar uwa kuwa. A cikin ɗakin kuwa cike da mmki Dr yake kallon Fariyda dake ta mutsu-mutsun ƙwace kanta a jikinsa, sai kuma ya kalli Salim yace. "Matarsa kuma?”. Cikin tabbatarwa ya gyaɗa masa kai Dr yace. “Dama yana da matane? To ina take? Ya akayi kuma ya kamu da wannan cutar me amfanin matar tasa?”. A hankali Fariyda ta fara magna cikin muryar kuka tace. “Ni ba matarsa bace”. Yadda tayi mgnar yana ƙwaƙume da ita yasa Dr baijita bama, dai-dai lokacin Dr Sisila ta shigo da Nurses ɗaya a bayanta rike da ɗan wani tray, juyawa Dr Haisam ɗin yayi ya fara mata bayanin ai wai yana da matama ga ma matar tasa. Shi kuwa Mahmoud a hankali cikin muryar ciwo yace. "Farriyyha Kuka kikeyi ne? Kina tsoron kar in mutu ne?”. A hankali tace. "Ni kam ka sakeni”. Cikin rawan murya yace. “Har abada Farriyyha bazan sakeki ba, kima dai na faɗa ko kina son Allah ya isan Mamy ya hau kanki ne”. Tana ɗan ture ƙirjinsa tace. "Ni a jikinka nake nufi ka sakeni. Ai wannan kam ka rigada ka sakeni”. Jiki da murya na rawa yace. “inji uban waye”. Jin yadda ya ƙara matseta ne tace. “Inji uban Zaid da Zaitoon mana”. Ta faɗa murya na rawa. A hankali yace. “Kina tsoron in mutu kin san duk duniya bazaki samu irina ba ko”. A hankali Salim ya miƙe jin Dr Haisam na faɗin. "Afwan Salim zaka bamu wuri zamu gana da matarsa dashi, ai ba bukatar wani aiki tunda yana da mata, munce a masa aikine dan Abbanku yace mana baida mata, wata ƙil lokacin yana kiɗimene shiyasa”. Juyawa yayi ya fita yana kara tabbatar musu ga matarsa nan. Yana fita Nurses ɗin duka na biye dashi a baya. Gyara zamanta tayi jin ya saketa saboda mararsa data sake murɗawar, da yatsa Dr Sisila ta nuna mata shi yadda yake riƙe da mararsa gyara tsayuwa tayi tana faɗin. "Kin san me yake damunsa kuwa?”. A hankali Fariyda ta jujjuya mata kai alamun a'a. Numfashi ta fesar cikin irin yar fusatar likitocin in sunga sakacin mutum akan ciwon ɗan uwansa tace. “Ok sai ciwon buƙatar kasancewa dake ya kashine zaki gane yana buƙatar ki kusa dashi, a inama kike da har mijinki zai shiga irin wannan halin ki kasa taimaka mishi da komai, duk da nasan ku musulmai in kuna period ko kun haihu haram ne mijinmu yayi sex daku, amman ai ance halal ne ku taimaka musu da bakinku da hannunku, gaki mace har mace ko mace yar uwarki in ta ganki tasan kin cika mace ta yaya bazai rinƙa azabtuwa da buƙatar kasancewa dake ba”. Tunda ta fara mgnar bata tsayaba bare ta bata damar ta faɗa mata itafa yanzu ba matarsa bane ya saketa, shi kuwa Mahmoud tunda Dr Sisila ta shigo bai kuma buɗe idonsa ba sai fuskarsa daya tsuke musamman yanzu da ta ɗaura da cewa. "Tunda aka kawoshi Papi ɗinsa bai barshi ya samu natsuwa ba ga azabar ciwon mara har suma yayi jiya iyayensa nata kuka, shi kuma yaƙi ya tsaya muyi masa aikin zuƙe sm ɗin da ya cika mararsa yace sai dai ya mutu wata mace bazata mishi wannan aikinba, har wasiyya ya barwa ɗan uwansa ko ya fita hayyacinsa kar a bari mu taɓa papi ɗinsa. Ke duk kina ina me amfaniki da bazaki zo ki masa abinda zai samu sauƙiba, da zaran ya samu ya zubda Spm ɗinsa shike nan ya zai samu sauƙi, in Kuma bai fitarba duk bayan auwa biyu sai ya murɗeshi, a ƙarshe komai zai iya faruwa dashi”. Tunda tayi ƙasa da kanta bata kuma ɗagowa ba bare ta kallesu badon riƙe hannunta da yayiba da tuni ta gudu ta bar wurin don ji take tamkar zata nitse cikin ƙasa, more Especially Dr Haisam abokin Yah Nasir ya santa farin sani. Jin Dr Sisila da a ƙalla zata kai sa'ar shekarun Goggo Dada shi yasa bai zagetaba dan da yarinyace ke magna kan wannan abun da tuni ya zagi kan uwarta. Cikin tausasa murya Dr tace. "Please Madam ki taimakawa mijinki in bakya son rasashi, in dai ba so kike ya mutuba to ki taimaka masa ya fidda abinda ke cin mararsa”. Ita dai ko ƙala bata ceba kanta dake sunkuye take ƙara sunkiyarwa har kamar zai taɓo ƙasa haɗi da rufe idonta. Har Saida suka ƙaraci baya nansu suka fita. Ido ya zuba mata murya na rawa yace. "Farriyyha zan mutufa! Wlh zan mutu in baki taimaka min ba Please My Angel help me”. Da sauri ta fizge hannunta daga nashi ta mara masu baya, narkakkun idonsa ya zuba mata har ta fita ko juyowa batayi ba. A nan waje kuwa Jidda tayi tsaki yafi dubu, haka yasa Khadijah yin dariya cike da manufa tace. “Adda Nana gwarafa mu tafi kwai kinga lamari da masoya an haɗu sun koro likitocinma sun barsu su kaɗai gwara mu tafi kawai mu barsu su yayyafawa fure ruwa da turare”. Salma da Salmanu ya kawota ita dasu Raihana ne tace. "Ni ma dai kam gwara in tafi dan kumatuna ya kusa fashewa da tsakin kishi”. Ta ƙare maganar tana hararan Jidda dan ta cika da tsanarta tun ranar da tayiwa Fariyda rashin mutunci ko gidan ma bata kuma zuwa ba. Zainab ne tace. "Au dama tana cikine Fariyda, aiko gwara mu tafi kunsan muna da abun yi tunda yau ɗin ranar muce sisters day fa”. Raihana tace. "To ai itama Fariyda ina sonta a kusa”. Khadijah tace. “Ke wa yake take mijinta ya ritsata zatayi jinyar miji ai yafi zuwa bikin yar uwa lada”. Dariya sukayi harda tafawa sai da Saddiqa da Adda Nana suka fara auna musu kallon gargaɗine sukayi shiru. Ita kuwa Jidda Amina dake can gefe tare da Salim da alamun magna mai mahimmanci Salim ke faɗa mata saboda ganin yadda fuskar Amina ya cika da farin ciki. Huzaifa da Hafiz da Sadiq kuwa suma suna can gefe. Harara Jidda ta auna musu haɗi da cewa. "Mata ko karuwa auren da babu ida a kanshi ai tun randa aka dannawa mayya saki uku magna ta ƙare dole a barmin ɗan uwana”. Salma ta yunƙuro da niyar magna kenan Fariyda ta iso wurin tana gyara mayafin jikinta. Adda Nana tayi saurin cewa. "Mu tafi to”. Haka yasa Salma yin kwaffa kawai ta juya suka tafi, bayan sunyi sallama da Amina. A yammacin ranar suka sha shagalin sisters day, washe gari laraba sukayi kamu, zuwa ranar kam kab yan uwa na nesa dana kusa duk an cika maƙil da ƴan uwa an fara biki gadan-gadan yan uwan angoma daga Taraba sun iso. Alhamdulillah sunyi kamu lfy lau, wuraren ƙarfe goma na dare suna cike a parlour Aunty Amarya dukansu cousins ɗinsu ba wanda bai isoba hira akeyi ana shan dariya. Mamy ne ta shigo parlour sannu da hidima tayi ta musu da jaddada musu akwai abinci fa. Mimy dake biye da ita a bayane tace. “Wannan ai duk taron yan kwalamane ba cin abinci zasuyiba tun ɗazu Amira da Sulaimi suna kitchen