Sashe 28
Sakar Makafi Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read
In one second Mahmoud ya kaucewa rungumar data kawo mishi, yana mai juya kansa zuwa kan Fariyda kamar yadda itama Fadila tayi mutuwar tsaye tare da zubawa Fariyda ido saboda jin sautin muryarta dake fidda harrufan karatun Ayar Suratul Al-Israa aya ta 32 *Wa laa taqarabuz zinaaa innahoo kaana faahishatanw wa saah'a saabeeyla* Idonshi ya tsaida cikin kwayar idanunta da yake tafe da wani saƙon dake tafe da tunasarwa haɗe da tsorotarwa. Ita kuwa Fadila a hankali ta sauƙe numfashi gami da yin ƙasa da kanta. Kai ya ɗan juyo kan Fadila, kallonta yayi na seconds yana mai kawo fassarar ayar da Fariyda ta karanta, sai kuma ya ɗan juyo kanshi kaɗan ta gefen ido yake kallonta lokacin da ta iso kusa dashi kib da kib tana mai tura akwatinta tsakaninsa da Fadilan. Kallonsa takeyi ido cike da takaici mai haɗe da gyama ta fara motsa lips ɗinta tana kawo aya ta gaba. Wa laa Taqtulun nafsal latee Harramal laahu illaa bilhaqq wa man qutila mazlooman faqad ja'qlnaa liwaliyyihee sultaanan falaa yusrif fil qatli innahoo kaana mansooraa Suratul Al-Israa Aya 33 A tare suka sauƙe numfashi mai nauyi shi da ita Fariydan. Fadila kuwa kai ta ɗago cike da kunya ta kalli Fariyda sai ta kuma kalli su Zaid dake jikin Mahmoud ɗan ƙara matsoshi Fadila tayi tana mashi kallon dake cike da so ta ɗaura hannunta kan su Zaitoon. Ita kuwa Fariyda ido ta zuba mishi cikin ƙallon dake nuna ƙyama, tsana, takaici takeyi masa tare da taune gefen lip ɗin na ƙasa. Da sauri Fadila ta matsa gefe, bayan ta shafa kan su Zaid tare da kissing Cheek dinsu, gaban Fariyda dake yi mata kallon ƙyama irin wanda duk tsabtarka in anama kallon mazinaci sai an ƙyamaceka da sauri Fariyda ta ɗan ja da baya ganin Fadila ta matsota da nufin runguma, a yatsine take ke kallon Fadila tana mai taɓe baki jin Fadila na faɗin. “Haƙiƙa Allah yayi miki babbar ni'imar da samun miji irin Mahmoud. Wanda nake fatan kin san hadisin nan da manzon Allah ke cewa ka sowa ɗan uwanka abinda ka sowa kanka kamar dai yadda kika san ayoyin dake hani da gargaɗi da tsoratarwa kan zina, dan naga alamu ke hafizace Allah yayi Mahmoud ni'mar samun mahaddaciya a matsayin matar aure wacce duk ni'imar duniya Allah ya gama mishi ya bashi kekkyawar mace mai haiba da kyan zubi da sura ga ilimi ga aji ga arziƙin haihuwa”. Bata ƙare jin abinda Fadila ke faɗiba ta juya ta fito tsakiyar harabar wurin. Ba tare da ta ɗauko akwatinta ba, fitarta da kamar 12 minute ya fito rungumeda su Zaid wuceta yayi kamar bai gantaba, motar da taga Ya shiga ta nufa, fuska a tsuke har lau baki a taɓe, baya ta shiga ta zauna tare da jan marfin ta rufe tunda tayi ƙasa da kanta bata sake ɗago kantaba duk da ba waya take dannawa ba. Jin anyi parking ne yasata ɗan ɗago kanta. Lagos Marriott hotel ikeja shine rubutun da tayi arba dashi a saman katafaren bene na alfarma da ƙawa da taga sunyi parking a ciki, a tare suka shiga Reception ɗin. Baki ta taɓa cike da tafasar zuciya ko uwar me kuma zasuyi a Lagos da zai kama hotel da taji suna faɗa masa price dinsa akwai na duk kwana ɗaya 400k akwai na 700k da kuma VIP 1m da wani irin harara ta rakashi lokacin da taji yana faɗin a basu key ɗin VIP ɗin. Murya ƙasa-ƙasa tace. “Ai wannan almobazzaramcine 1m a 1 day mutum bai iya tattalin kuɗiba kashesu kawai ya iya”. Ɗan juyowa yayi ya kalleta lokacin da suke gab da shiga corridorn zai sadasu da ɗakin yace. “In kuɗinki ne ki ƙwace, ki hananin yin abinda nake so”. Harara ta mannawa bayansa a ranta tace. “Ai ni dama na sani kullum in ina gayawa Yah Amin shi wannan bai san lallaɓa kuɗi ba sai kashesu kawai komai nashi yace iyakar ƙololuwar tsada zaiyi”. Ta ƙare maganar zuci da sauƙe numfashi lakacin da suka shiga ɗakin da ta gamsu tabbas eh lallai VIP yaci kuɗinsa. Tunda suka shigo ɗakin ta zauna kan kujera tayi ƙasa da kanta bayan ta mannawa ƙeyarsa harara, bata kuma sake ɗaga kantaba. Shi kuwa Mahmoud suna shiga briefcase ɗinsa ya buɗe ya zaro wasu tattausan riga da wandon 3 quarter da singlet and boxes, turarensa mai sanyin ƙamshi da sabulunsa da duk ƴan abubuwan buƙatarsa dake ciki ya ɗauka. bathroom ya wuce, sauri-sauri yayi wanka da alwala ya kimtsa fesa kana ya fito da jallabiyar a hannunsa bakin ƙofar ya nufa ya buɗe dan jin ana Knocking jallabiyar ya miƙawa ma'aikacin nasu tare da amsar tarkacen daya miƙa masa kan gadonsu alfarmar ya ajiye mai dasu sabulu da turaren da suka miƙa mishi. Turarensa ya ƙara fesawa a jikinsa tako wani sashin lokaci ɗaya ɗakin ya sake ɗibkewa da ni'imtaccen ƙamshin jikinsa dana ɗakin. Jin ana ƙara Knocking ne yasa ta ɗago kai da ido ta rakashi zuwa bakin ƙofar tana kallon shi sama da ƙasa, 3 quarter ɗin irin mai aljifayen nan ne sai yar T-shirt ɗin mai guntun hannu wacce tayi cib-cib da jikinsa ta kwanta ta lafe hakan ya bayyana ƙiran faffaɗan ƙirjinsa a fili wanda har kana iya ganin shatin singlet ɗinsa da kuma tudun ƙirjinsa more Especially kan ƙirjin, gashin ƙansa dake baza ƙyalli kamar wanda mai ya zube a kansa sai wurin ƙeyarsa da yake kwance sulup-sulup sai na sajensa da shima yake baza sheƙi da ƙelli, ta kuma mannawa harara da jan tsaki gami da meda idonta kan ƙugunsa zuwa ƙasa kan ƙwarinsa inda 3 quarter ya tsaya sharabarsa dake lulluɓe da tattausan gashin jiki wanda ke kwance sulup-sulup tayiwa kallo ɗaya ta kauda kanta takalmin snicker half cover ne a sawunsa Royal Blue kamar yadda rigar jikinsa take Royal Blue sai 3 quarter da yake fari. Kanta ta maida kan su Zaid da tunda suka shigo suke wasa da tab ɗinsu da har yanzu suna hannunsu. Tray da ya amsa ne ya ajiye kan ɗan table ɗin dake gefe wanda ke zagaye da yan madai-daitan kujeru guda huɗu. Tsaki taja tare da harararsa, sai kuma tayi saurin yin ƙasa da kanta ganin yadda ya tsura idonsa cikin nata. Bathroom ta wuce da hand bag ɗinta, wanka da alwala tayi sai kuma tayi shiru tana kallon kanta a mirror a fili tace. “Akwatina fa”. A hankali ta tsane ruwan jikinta da Women bathrobe ɗin da farkeshi daga ledarsa, mai ta ɗan shafa tare da murza turarukanta dole tasa ta maida Abayarta wacce take baza ni'imtaccen ƙamshi mai sanyaya zuciya. Zaune ta sameshi kan kujerar table ɗin, fruits ɗin da aka kawo mishi yake sha yanayi yana duba wayarsa alamar kallon lokacin da bisa dukkan alamu akwai abinda zai yi. “Akwatina fa”. Ta faɗa tana kallonshi. Shiru bai kulataba sai ma kallon Zaid da ya manna ƴan lips ɗinshi kan kumatunsa yayi masa kiss, murmushi yayi tare da shafa kan Zaid ɗin. “Ina akwatina yake?”. Ba tare da ya kalletaba yace. “Yana inda kika barshi mana, ko akwai bawanki da zai ɗauka miki shine”. Numfashi ta fesar tare da zama kan 3 seatter ɗin cikin tsuƙe fuska tace. “Nifa na gaji zan koma gida, dan ban san manufar sake kama wani hotel ɗin ba da zama a Lagos, ni wlh ina kewar iyayena da yan uwana ina son ganin Mamy na da Baba Malam, nayi kewar Ummi da Goggo Dada da Abba ina son ganin iyayena da ƴan uwana”. Ta ƙare maganar cikin iyakar gaskiyar ta da yasa idonta cikowa tib da kwalla da nuna tsananin kewar iyayenta da son ganinsu a fili wanda ke nuna gskyar abinda ta faɗa. A fakaice ya kalleta ganin hawayen dake silalo mata ne yasashi kauda kanshi gefe. Zaitoon dake kiciniyar hawa kan cinyarsa ya jawo yana mai tsinkar cherry yasa a bakinsa ido ya lumshe saboda sanyinsa daya ratsa mishi harce. Da sauri ya buɗe idonsa jin Zaitoon ta manna lips ɗin kan nashi lips ɗin tayi kissing nashi, murmushi mai sauti yayi ya manna mata kiss ɗin a goshinta. Sai kuma ya sauƙeta ganin tana kiciniyar sauƙa daga jikinsa inda Fariyda ke zaune ta nufa, haka yasashi ɗan kallon Fariyda da zuwa yanzu hawayenta sun zubo kan kuncinta ta matse lip dinta na sama tana tsotsa ta turo na ƙasan kuma tayi tamkar yar yayen da ke rigimar kukan yaye. Kamota Zaitoon ɗin tayi da kiciniya ta hau kan kujerar ta hanyar yin tsani da sawun Fariyda hannunta duka biyu tasa ta maƙale wuyan ta manna lips ɗinta kan na Fariyda data turoshi. Da sauri ta ture Zaitoon ɗin ta sauƙeta ƙasa tana mai turo harshenta waje cikin kwaɓe fuska take ɗan tofo yawun bakin Zaitoon ɗin da hurawa da iska fuska tsuke. Sai kuma ta tureta ganin ta ƙara dawowa kusa da ita mari mai cike da takaici tayi mata gami da tureta. Kusan a tare suka miƙe tsaye ita da Mahmoud ɗin da yake mata wani irin kallon mai tafe da fusata wanda ya hanashi tauna grapes ɗin da yake bakinsa, da sauri ya ɗauki Zaitoon ɗin data faɗi ƙasa ya rungumeta yana shafa kanta da jijjigata haɗe da matsowa gaban Fariyda cikin kafeta da ido yace. “Baki da hankali ko?”. Tana jawo bakin Veil ɗin da tayi Rollin kanta dashi ta fara goge bakinta cikin nuna kyama tace. “Ya zatayi min laifi kuma ace kar in hukuntata”. Yana mai ƙara shafa kan Zaitoon ɗin da jijjigata yace. “Akan me zaki mareta? Me tayi miki?”. Har lau goge lips ɗinta takeyi tace. "Akan me zata zo tayi min kiss, kiss din ma lips to lips”. Gyara riƙon Zaitoon ɗin da tuni tayi shiru yayi yana mai nunata da yatsa yace. “Dan kawai tayi kissing naki sai ki dakar min ƴa harda tureta ta faɗi kawai dan kin samu tana sonki tayi kissing naki zakiyi mata wannan marin dame lips ɗinki sukafi nata”. Cikin takaici tace. “Da tsabta akan me zatayi kissing lips dinka da ba wacce iriyar karuwar da ba'a sumbata da suba tazo a take ta manna min yawun ka data laso a lips dinta”. Tunda ta fara mgnar ya tsareta da ido tamkar zai mannasu kan lips ɗinta da take motsawa da turawa. Kan