← Book details Sakar Makafi Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 69 OF 95

Sashe 69

Sakar Makafi Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read

“Salma jikin nasa har haka yayi tsananin da Abba da Ummi ma suke kuka, to yaushe ya fara mishi?”. Sai kuma ta ɗanyi jim tana sauraronta fuska cike da kaɗuwa tace. "To Allah ya kawoki lfy, Salman ɗin ya isone ko dai in turi Sadiq yazo ya ɗaukeki tunda kince Salim ɗin ne tare dashi, ba yadda za'ayi ya bar wurin”. Sai kuma ta ɗanyi shiru na seconds kana tace. “To Allah ya kawoku lfy”. Daga nan ta katse kiran. Fariyda da har lau idanta ke kafe a kanta tace. “Meke faruwa meya sameshi?”. Juyawa tayi tana kallon Saddiqa dake cewa. “Yanzu fa kafin inzo Aunty ta dawo daga parlour Malam tace wai baya nan akwai mara lfy da aka gaya masa jikin yayi tsananin a rikice ya tafi baima gaya mata wayeba to ko dai Mahmoud ɗin ne”. Adda Nana tace. “Shine ma dan Salma tace min ga Malam ya iso tun ɗazu jikin fa yayi tsanani sosai tace har Umminsa da Goggo kuka suke yi, Abba ma yana zubda ƙwalla”. Ido ta juyo tana kallon Raihana dake cewa, ai ɗazu da na fita na samu Mamy ma sun fita da Sadiq da Aunty Amarya. Irin abinda zuciyarta yayi mata ranar da akace Yah Amin yayi acsident shine taji sak irinsa ya rufe mata zuciya da jiki, haka yasa ta kasa ƙara cewa komai sai tsuma da jikinta keyi ta ciki, idonta kuma har lau ta kasa koda ƙebtasu. Saddiqa tace. "Adda ko zamu jene”. Cikin sanyi Adda Nana tace. "To ai su Salma ma da suke can. tace Malam yace duk mata sun tafi, yanzu itama dasu Mamy Salmanu na dawo dasu gida, su Ummi ma Malam yasa Hafiz ya medasu gida dan kukan da suke yi sun rikita ko ina.” Zuru sukayi cikin sanyin jiki, ita kuwa Fariyda a hankali take motsa lips ɗinta bayan taja numfashi mai ƙarfi sai kuma tayi shiru bata ce komai. Dai-dai lokacin sukaji shigowar su Mamy, da sauri duk suka nufi parlour banda ita da ƙafafunta suka kasa miƙewa. Adda Nana ta kalli Mamy dake zaune kan kujera tallaɓe da kuncinta. Aunty Amarya na gefe zaune a hannun kujerar Mamy Salma kuwa na zaune a ƙasa Salmanu ƙaninta aune a gefenta. "Mamy ashe Mahmoud ne ba lfy ya jikin nasa”. Ido na cikowa da ƙwalla Mamy tace. "Nana Mahmoud najin jiki, yaron nan ya bamu tsoro”. Da sauri Aunty Saddiqa tace. "Mamy meke damushi? Yanzu ya jikin nasa” Ta ƙare tambayar tana kallon Aunty Amarya dake cewa. "Wlh har yanzu jikina rawa yake yi, Mahmoud yana cikin wani yanayi, Amman yanzu kam da sauƙi Sadik yace dan na kirashi kafin mu shigo”. Raihana tace. "Mamy Accident yayi ne?”. Tana sharce hawayenta tace. "Ba Accident bane, ciwon cikine ya murɗesa lokaci ɗaya ya galabaitar da shi tamkar zai ɗauke rayuwarsa, wlh Hajia Fatima ta bani tausayi ta kiɗime sosai sai kuka takeyi Goggonsu har suma tayi lokacin da cikin yayi masa murɗar da tasa maza zubda ƙwallan”. Ido na cikowa da hawaye Salma tace. "Ni tunda naga Yah Salim na kuka nasan abin nan babbane.” kiran Salim ɗin da ya shiga wayarta ne yasa ta sauri amsawa, yadda taji muryasa ne yasa ta sauƙe numfashi da sauri tace. "Babe ya jikin Appiyn Zaid”. Sai kuma duk suka kalleta jin tana hamdala tare da addu'ar Allah ya ƙara masa sauƙi ta ɗaura da cewa, “Babe ina gidan Baba Malam mun dawo dasu Mamy”. Bayan ta katse kiran ne tana kallonsu tace. "Alhamdulillah Yah Salim yace yanzu jikin da sauƙi har sun samu yayi bacci”. A tare sukayi ta hamdala, Mamy ne ta mike ta nufi bedroom ɗin Fariyda yadda su Raihana suka barta haka Mamy ta sameta kamar mutum mutumi, sai dai yanzu numfashinta ya dai-dai tun da ta jiyo duk abinda suke tattaunawa a parlour har da abinda Salma ta faɗa. Haka yasa ta rungume su Zaid a jikinta irin yadda Mahmoud ke rungumesu kansu take shafawa kanta na sunye a kansu. Fuska a haɗe Mamy tace. "Ke baki ji Mahmoud ba lfy bane”. A hankali a ɗago kanta sai kuma tayi ƙasa da kanta a hankali ganin kallon da Mamy ke watsa mata, ita kuwa Mamy cikin takaici tace. "Koma baki masa fatan samun lfy a kan komai ba a duniya kyayi masa fatan samun lfy ko saboda yaranki da in babu shi a duniya sun tabbata marayu, amman da yake zuciyar dutse gareki kin ɗaurawa kanki tsanar mutumin da yake son yaranki tamkar ranshi kowa ya fito amman banda ke wato ke farin cikima kikeyi ko?”. A hankali ta fara jujjuya kai alamun a'a. Saddiqa da Adda Nana ne suka shigo Salma na bayansu Mamy taci gaba da cewa. "A'a wlh farin ciki kikeyi tunda ko ki fito ki jajanta kiji me ya sameshi kin gaza, bare aje ga babin kiyi masa addu'ar samun lfy”. A hankali tace. "Allah Ubangijin talikai ya bashi lfy dashi da dukkan ƴan uwa musulmai baki ɗaya”. A faɗace Mamy tace. "Amin Yah Allah in ma da gatse kikayi masa uwarsa kam da ubansa suna can sunayi masa addu'a suna kai kukansu wurin Allah kuma zai amsasu, muma kuma da duk masoyansa muna masa addu'a”. Daga nan ta juya ta fita Aunty Amarya dake bakin ƙofa nace mata. "Yi haƙuri dare yayi fa ana jinki har waje”. Gefenta Salma ta zauna tana amsar Zaitoon tace. "Wlh naji tsoro sosai shiyasa na kiraki, Fariyda naga su Ummi ma sai kuka suke Abba ma da kansa da Bappa Lawan hawaye suke yi, Yah Salim kamar macefa yake kuka yana rungume da Appiy Zaid. Amman Alhamdulillah yanzu kam yace da sauƙi sosai har yana min tsiya wai na gudu na barshi yau da wa zai kwana kinga kenan ai jikin Appiyn Zaid da sauƙi kenan”. Kai ta jinjina tare da cewa. "Allah ya ƙara sauƙi”. Amin sukace a tare. Daga nan kuma suka ɗan fara hira, Raihana ta shimfiɗa katifa a can gefe ita da Adda Nana da Salma suka kwanta a kan katifan Anuty Saddiqa da Fariyda dasu Zaid suna kan gadon hira suke yi sosai Raihana da Bashir ɗinta ya turo mata videos ɗin gidansu dasu Aunty Jamila da matar kawunsu da ƙawar Mamynsu sukaje suka yi jeren yau ɗin ne ta kalla tare da miƙawa Aunty Saddiqa wayar. “Wow”. Tace lokacin da ta fara kallon tsarin farfajiyar gidan har zuwa cikin parlour bedroom kitchen da ko wani saƙo na gidan. Salma da Adda Nana suka amsa suma suka gani, sosai kyau da tsarin gidan yayi kyau duk da gidan ba irin ƙato ɗin nan bane. Ido Adda Nana ta zuba wa Fariyda dake zaune jingine da kan gadon idonta a buɗe Amman kamar bata ɗakin duk abinda suke faɗa shiru. Salma tace. "Dama fa nima gobe talata zanzo tunda goben za'ayi sisters day, jibi laraba kamu ko, ranar Alhamis kuma wali jumma'a ɗaurin aure asabar zamu tafi taraba ko”. Saddiqa tace. "Wai kin tambaya an barkin ne”. Da sauri tace. "Wallahi ya barni da kanshima fa ya tayani shirya akwati da zanzo dashi ɗazu muna cikin shiryawan ne aka kirashi Appiyn Zaid ba lfy”. Kai Adda Nana ta jinjina tana kallon Fariyda data zame ta kwanta ta rungume su Zaid haɗi da lumshe idonta tayi shiru. Da ido Adda Nana ta nunawa su Saddiqa ita, a hankali Raihana tace. "Mamy ta mata faɗa ta ɓata mata farin cikinta”. A hankali Salma tace. "Ko dai ciwon mijinta ba”. Tsaki ta ɗan ja tare da taɓe baki tana hararan Salma tace. “Bani da mijinma bare yayi ciwo bare ciwonsa ya tsaya min a rai”. Ta ƙare maganar tana jan wayar taci gaba da karatun littafin Garkuwa, 2 minute tayi da farawa sai kuma ta juya ɗaya gefen tare da kifi wayar bayan kamar 10 minute ta kuma jawo wayar ta ci gaba da karatun tsaki ta ɗan ja ta kuma kife wayar. Su kuwa sai hira suke tayi Ameera ne ta shigo da trayn a hannnuta ta dafa musu indomie sai tururi yake yi yaji kifi da albasa taruhu. Salma tace. "Kai yar ƙanwata Allah yayi miki al'barka dama yunwa nakeji”. Aunty Saddiqa tace. “Ai mu mun saba cimar tsakiyar dare, don bama bacci da wuri shiyasa in gari ya waye yara sun tafi school mu biya bashin baccin itama Amiran da yake zuwan rana takeyi”. A hankali Fariyda ta juyo tare da jawo wayarta tana duba Time ƙarfe biyu saura, bathroom ta wuce alwala ta fito. Saddiqa na kallonta tace. "Kizo muci yayi yaji sosai yadda kikeso”. Kai ta jujjuyawa a hankali tace. "Bana jin yunwa”. Ta ƙare maganar tana shimfiɗa darduma ta kabbarta sallah, kusan duk a tare suka ɗaga gira kana sukaci gaba da hira da cin indomie, nafila tayi tayi daga bisani ta fara karatun Alqur'ani. Ƙarfe huɗu baccin shaiɗan ya kwashe su, har lau tana kan sallaya Saida tayi sallan asuba ta tashesu, kana ta koma ta kwanta tana cewa Raihana. "Dan Allah in su Zaid sun farka ki tafi dasu part ɗin Aunty Amarya ki musu wanka acan ki basu abinci kar su hanani bacci”. Kai Raihana ta gyaɗa mata. A tare suka shiga parlour Baba Malam dan gaisheshi. Aunty Amarya suka samu a parlour nashi tana shirya masa kayan tea, bayan sun gaisa ne Adda Nana tace. “Aunty Malam fa”. Tana ninke dardumarsa tace. “Tunda ya fita masallaci bai dawoba dama yace zasu wuce asibiti shida Safiq zasuje su duba Mahmoud da jini”. A tare sukace. Ayyah to Allah dai ya bashi lfy. Amin tace tana kallon Salma dake cewa. "Nayi magna da Yah Salim dai yace, har yanzu yana bacci”. Aunty Amarya tace. "Bacci ai alamun lfy ne”. Sai ta kuma kalli Saddiqa da Adda Nana tace. "Zakuje kitchen kunsan sai an sawa Lami hannu a aikin, yanzu Kahdija ma ke cemin anjima kaɗan zata iso”. To sukace, ina Fariyda ta tambaya, Raihana tace. “Tana bacci”. Daga nan suka fito suka nufi kitchen ɗin tsakar gida inda ake aikin biki. Ƙarfe tara da rabi Mamy dake tare da Khadija da bata daɗe da isaba, ta miƙe ta nufi daƙin Fariyda zaune ta sameta gaban dressing mirror, tana fesa turare da alamun ta ɗan jima da tashi tayi wankanta tayi kimtsa cikin doguwar rigar material mai taushin gaske milk color
Chapter 69 · 0% Book details