← Book details Sakar Makafi Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 22 OF 95

Sashe 22

Sakar Makafi Part 2 Complete Hausa Novel · about 4 min read

da azabar yunwar da takeji ta zaɓi coffee ne saboda sanyin daya gigitata ya fara sata ƙarƙarwa, baki ya taɓe yana dannan wayarsa. Su Zaid ya fara bawa abinci saida suka ƙoshi ya goge musu baki sannan ya gyara zamansa ya fara cin abinda suka kawo mishi. Flacks ɗin coffee ta buɗe a karo na uku ta sa a ɗan ƙaramin mug ɗin da baya wuce kurɓa biyar, zuƙeshi tayi tana mai ɗan jin rawan sanyin da lips ɗin ta keyi na raguwa, sau huɗu tasha kana ta gyara zamanta tana mai longwaɓar da kai tace. “Ayyah zan tafi cikin mota sanyi kamar zai kasheni”. Tayi mgnar tana ɗaukan Zaid da shima yake takure duk da Sweater dake cikinsa. Zaitoon kuwa yar son sanyi harkokinta takeyi daga nan zuwa can. Car key ɗin ya ajiye a kan table ɗin ta ɗauka da sauri ta juya ta fita. Kusan 42 minute tayi a zaune kafin ya fito tuni magrib ta ƙarato, daga nan Homey Airport hotel ɗin suka wuce tafiyar 26 minute suka isa. Suna shiga ta sauƙe Zaid kan babban gadon, shi kuma bathroom ya wuce al'wala yayi yana fita ya nufi ƙofar ɗakin a hankali tace. “Tafiya zakayi ne?”. Tsayawa yayi ba tare da ya fitaba kuma bai tankanata ba tana ɗan kallonsa tace. “Ina zaka je?”. Tayi tambayar dan son cemasan ta manta wayarta a gidansa. “inda kika aikeni”. Ya bata amsa tare da fita. A hankali ta sauƙe numfashi tana mai jin sauƙin sanyin saboda ɗumin ɗakin. Wanka tayi da ruwa mai ɗan karen zafi haɗi da al'wala tana fitowa ta kimtsa cikin tattausar Turkish jallabiya mai sulɓi da ɗumin gaske, turarenta mai sanyin ƙamshin ta fesa, tana zura ɗan hijjab ɗin jallabiyar ya shigo riƙe da sallaya da briefcase ɗinsa. Yana shimfiɗa sallaya ya kabbarta sallan magrib da tuni ana ta kiran salla, Itama gefenshi ta koma ta kabbarta sallah. Bayan sun idar ne, ta miƙe ta gyarawa su Zaid kwanciya dan tuni sunyi bacci. Shi kuwa waya yake yi da Sulaiman dake tambayarsa ya jiki da kuma abinda ya shafi kasuwancinsu. Koda suka gama waya isha tayi. Bayan ya idar ne ya jawo pillow yasa akan tattausan sallayarsa daya shimfiɗa kan Turkesh carpert ɗinsu mai masifar laushi gaske, ɗan kishin giɗa yayi ta sa system nashi a gaba yana aiki da Yah Ahmad ya tura masa. A hankali tace. "Appiy wayata na bari a”. Cikin tsareta da ido da takaicin umarnin da Abba ya bashi na cewa kar ya sake kwana shi kaɗai saboda jikinsa ya kwana da ita, ganin yadda ta addabi rayuwarsa daren jiya akan kare harda suma ta kwana iface-iface ta hanasa bacci ne yasa dole ya taho nan ɗin da shirin kwana. “Appiy”. Ta kuma kiransa cikin sanyi. A daƙile yace. "Kika sake cemin Appiy sai na baki marin da zai makantaki”. A hankali tace. “To ince ma Mudy”. Wani irin kallon takaici ya watsa mata a kufule yace. “Nine ma Mudy, Mudy to ma a gidan uwar wa kika samo wannan sunan zaki labta min shi Mudy me Mudy”. Cikin sanyi tace. "To incema Papi?”. Wani irin juyowa yayi ya mata kallon da bata taɓa ganin makamancinsa ba a rayuwarta, rawa lips ɗinshi suka farayi kamar maijin sanyi yana nunata da yatsarsan ido cike da yanayin da yafi kama da nadama sai kuma kawai yayi ƙasa da kanshi “Ina son magna da Mamy nane kuma wayata na can”. Wayarta ya zato ya cilla mata kan gadon. Ya maida kanshi yaci gaba da abinda yake yi. Da sauri ta ɗaga kanta ganin ya kashe wutan ɗakin duhu ya mamaye ɗakin. Kwanciya yayi kan sallayar ya lumshe idanunsa saboda baccin da ya fara fizgarsa. Voice ɗin da Mami tayi mata ta bata amsa kana ta ji na Aunty Saddiqa sai na Amina sai Zainab, ɗan gajeren tsaki taja ta juyawa gefen hagu sai ta kuma juyowa dama, hannunta ta ɗaura kan cikinta da yake ɗakale kamar ba hanji ɗan coffee ɗin da tasha fitsari ɗaya da tayi ya tafi. Zama tayi a tsakiyar gadon tana ɗan tunanin cikin ɗakin ba wani abu na ci haka ne yasa ta ɗan kwaɓe fuska, sai kuma ta kwanta 2 minute tsakani ta tashi zaune, saboda murɗar yunwa tun jiya da safe. Cikin rawan murya tace. “Appiy”.. Shiru bai amsa ba baiyi masifa ba shi yasa ta ƙara cewa. “Appiy!”. Cikin baccin yaji muryarta dan ta sunkuyo ta inda yake kwance a ƙasan. “Appiy yunwa nakeji cikina ciwo”. Da sauri ta dawo tsakiyar gadon jin ya buge hannunta da ta kai da niyar tadashi hasken wayarsa ya kunna tare da cewa.......
Chapter 22 · 0% Book details