Sashe 54
Sakar Makafi Part 2 Complete Hausa Novel · about 4 min read
a ɗakinba turaren ya ɗauka ya fesa tako wani sashi na jikinsa haka dan yake yi tun kafin ruwan wanka ya bushe a jikinsa yake feffesa turarukan haka shi yasa ko ya haɗa zufa sai kaji yana ƙamshi, kusan turare kala uku ya fesa sai kuma ya fesa a ƙalla biyu a kanshi, har yanzu tana tsaye a gaban Wordrobe ɗin ko kanta bata ɗagaba bare ta motsa daga wurin dan ji tayi kamar an dasata. Juyowa yayi ya nufi inda take, a bayanta ya tsa kib da kib, ido ya zuba wa fuskarta ta cikin madubin ganin yadda tayi ƙasa da kanta tana wasa da yatsun hannunta ne yasa ya ƙara matsota, a hankali ta ɗago kanta jin ya manna ƙirjinsa da bayanta. “Waya baki izinin shigo min ɗaki?”. Ya faɗa yana cusa kanshi tsakanin wuyanta da kafaɗarta. Ido ta ɗan ɗago ido huɗu sukayi dashi ta cikin madubi girarsa ɗaya ya naɗaga mata cikin shu'umin salon da yasata sauƙe ajiyar zuciya mai nauyi, towel ɗin hannunsa ya ɗan saƙala kafaɗarsa murya can ƙasan cikin salo mai narka zuciya yace. “Sata zakiyi min ko? Duk wanda kika yi basu isheki bane?”. A hankali ta jujjuya kanta alamun a'a. Ƙara matsowa jikin ta yayi har tana jin bugun zuciyarsa bakinshi ya sa kan kunneta iska ya ɗan hura mata tare da cewa. “To waya baki izinin shigo min ɗaki, me kika shigo nema”. Haka nan taji idonta na tsatstsafo hawaye masu sanyi da bata san dalilinsu ba murya a narke tace. "Ba kai bane”. Yana ƙara matsota yace. “Ni kuma to me nayi?”. Tana ɗan matsawa tace. “Kace inzo in karɓi wayata ai”. Hannunsa ɗaya ya ɗaura kan lafeffen cikinta haɗi da janta jikinsa a tare suka sauƙe numfashi. “Buɗe idonki”. Ya faɗa yana ɗan sunsunar wuyanta haɗi da manna mata kiss a fatar wuyanta. Kai ta jujjuya alamun a'a. Cikin raɗa ya kirata. “Farriyyha”. Tsikar jikinta daya tashi ne ya bawa hawayenta damar zubowa, ido ya zuba mata ta cikin madubin, sai kuma ya ɗan kamo hannunta ya juyota suna fuskantar juna a hankali yace. “Kuka kuma meya sameki”. Cikin rawan murya tace. "Ka sakeni”. Kai ya jujjuya murya a daƙile yace. "Kin san sharaɗin shiga ɗakina kuwa?”. Ƴan siraran hawaye na zuba ta girgiza masa kai. Ƙara matsota yayi suna fuskantar juna har ɗumin numfashisa na sauƙa kan goshinta fuska a tsuke yace. “Mata basa shiga min ɗaki, ko Maman Hafiz bata taɓa shigo min cikin ɗakiba”. A hankali tace. "Meyasa”. Yana tsare fuskantar da ido yace. "Saboda ɗakina bana mata bane, kuma bazan iya ganin mace a ɗakin nan ta shiga ta fita ban mallaketaba”. Cikin gaza gano manufarsa tace. “To meyasa kace inzo in karɓi wayata”. Ƙara matsaota yayi sosai murya can ƙasa yace. "Nace miki ki shigo ɗakine, ai da sai ki tsaya kiyi Knocking in buɗe in baki”. Tana matsawa gefe tace. "Ai nayi Knocking baka buɗeba, ni ka bani wayata in fitan ma a ɗaki”. Hannunsa yasa ya tare gefen, sunkuyowa tayi da nufin fita ta ƙasan hannun da sauri ya manna guiwarsa da Wordrobe ɗin ya toshe hanyar duka. Baki ta murguɗa tare da turo lip ɗinta na ƙasa ta fara tsotsar na sama, ta juya ɗaya gefen dama da sauri yasa hannunsa ya tare, ta sunkuyo kenan yasa guiwar ɗaya ƙafar ya tare nan ɗin ma, haka yasashi ƙara matseta a jikin Wordrobe ɗin a tsiwace tace. "Ni ka bani wayata in tafi gidanmu”. Yana kallon lip ɗinta na ƙasa yace. "Da izinin waye zaki tafi gidan naku? Wa kika tambaya?”. Baki ta tura tana neman ta inda zata zama tace. "Da izinin iyayena Abba da Baba Malam”. Ƙara matseta yayi da jikinsa har Saida numfashinta ya fara nauyin fita, haka yasa ta ɗago kanta tana jan numfashi kwaɓe fuska tace. "Nifa ba yar isaka bace irinsu Idaya ka matsa min in fita”. A hankali yace. “Ba kina da ƙarfiba”. Mutsutstsuka bayanta ta farayi a jikin Wordrobe ɗin haka yasa ƙirjinta gogar nasa breast ɗinta da suke tsaye ba bra suka manna da ƙirjinsa, ido ta ɗago jin ko motsi baiyiba da sauri ta kauda kanta so take tasa hannunta ta tureshi ta kuma rasa ta ina zata ɗaura hannunta a jikinsa dan ba riga. Ƙara matseta da yayine yasa tayi saurin ɗaura tafukan hannunta ƙirjinsa ta fara tureshi da iyakar ƙarfinta ko gezau baiyiba bare ta samu nasarar tureshi, haka yasa ta fara muntsilinsa da hannu ɗaya daya kuma tana ɗan dukan ƙirjinsa da hannunta ɗayan tana zubda siraran ƙollan haɗe da cewa. "Ni ka matsa min zan tafi, ni bana son wayar ma na bar maka ita”. Dan tuno yadda ya yi jiya ne yasa tsoronshi dawo mata. Ci gaba tayi da dukanshi tana tureshi, kwaffa yayi yana lasar lip ɗinshi yace. "Ai kuma sai kiyi ai tunda kika kawo kanki nan ɗakin wlh baki da maceci sai Allah”.