← Book details Sakar Makafi Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 40 OF 95

Sashe 40

Sakar Makafi Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Mallakin mijin da na aurana bayan rabuwata da Mahmoud dan bazan iya zama ba aureba, to kuma sakayyar abinda nayiwa Mahmoud kanta ya sauƙa last year mai gadinmu yayi mata fuaɗe, ba yadda banyi in rabata da shiba amman abun ya gagara a ƙarshe muka gane sihiri yayi mata, sanin haka yasa hankalin mijina tashi, haka yasa muka bar Lagos muka koma Ibadan wlh har can ya bimu yanzu haka cikine da ita a wannan shekarun nata, ni nasan al'haƙin Mahmoud ne ke bibiyata shiyasa nazo da ita dan Allah Mahmoud ka yafe min ko dan in samu tseratar da rayuwar yarinyata”. Kusan duk a tare suka sauƙe ajiya zuciya tsoron da suke ciki duk ya sake musu zuƙata jin cewa yarinyar ba yar Mahmoud bace basu da alaƙa da ita na nesa ko na kusa duk dama ba wata alama ta kama ko ta jini, jiki, fuska, da zata nuna yar Mahmoud ce. Cikin sanyi Abba yace. “Ni dai kam kin cutar dani cuta mafi muni dani da ɗana, amman na yafe miki domin Allah, saura in sunga zasu yafe su yafe in bazasu iya yafewaba, bazan tirsasamusu ba”. Cikin sanyi da zubda ƙwallan murya a sanyaye tace. “Ɗan Allah dan Annabi da tsarkin Alkur'ani mai girma ku yafemin, ba don halinaba sai dan Allah da yace yana son masu yafiya.” Cikin Sanyi Ummi tace. “Kije ko yanzu Allah ya saka min kinji yadda naji dan haka na yafe, Goggo Dada Sulaiman Salim ku yafe mata.” A tare sukace. "Allah ya yafe mana”. Amina ce ta miƙe tsaye tare da kallon Fariyda dake magna cikin rawan murya mai cike da rauni kuka na danne mgnar tata tace. “Abba Ina jin zuciyata kamar zata fashe zan tashi in kamin izini bana son kallonta”. Ta ƙare maganar tana kallon yadda Mahmoud ɗin ke kuka mai tsuma zuciyar duk mai imani. Da sauri Amina tace. "Ni dai bazan yafe ba, kuma Mahmoud kaima karka yafe mata”. Ta ƙare maganar dana jan hannun Fariyda tada ita tsaye. Jin Abba yace. “Ba komai Fariyda kuje kawai”. Da sauri Salim ya miƙe yana kallon Idaya jin Mahmoud ɗin yana magna cikin cushewar numfashi yace. "Abba bana son ganinta dan Allah Salim ka fitar da ita a gidan nan karka sake kawo min ita ko kusa da inda nake”. Ya ƙare maganar yana riƙe kansa da hannu bibbiyu sabida wani irin azabebben Headache da ya azzabeshi. Kukaka mai sauti ta saki tare da kallon Salim dake cewa. "Mu tafi Idaya in sha Allah zasu yafe miki suma shi da Amina yanzu dai mu tafi baya son ganinki, mu tafi idan ya mike zai miki abin baki zataba”. Daga nan suka fita, yayinda su Ummi duk suka rakashi da ido. Fariyda kuwa da Amina ɗakin Ummi suka wuce dan Hafiza da Samira na ɗakin Goggo Dada, Huzaifa kuma yana parlour yana game a wayarsa. Riƙe hannun Fariyda tayi tare da ci gaba da bata labarin yadda hankalin su ya tashi a wannan lokacin da yadda Yah Amin yayi ta bibiyar abin da irin addu'ar da Ummi tayi masa da azabar jinyar da yasha, da yadda yake gigicewa duk sanda ya kusanci wata wanda da nan suka gane yana wata rayuwar ta da ban, haka tai ta mata bayanan da Idaya bata san da su ba tunda a nan a gida akayi , ido cike da kwalla tace. “Tsinenniya ce har yanzu bata da kunya a gaban mahaifinsa da mahaifiyarsa take ta maimata mana sihiri tayi masa harda cewa duk mazan da ta sani babu kamarsa hakafa muka haɗu da ita a Mumbai tayi ta kuranta min yadda taji daɗin kasancewa dashi a lokacin nayi zaton ɗan iskane shima ashe sihiri tayi masa, ba kunya ba tsoron Allah a gaban Abba fa wai ai shi cikekken na mijine da ba'a samun irinsa da sauƙi ko tsoron Allah bataji bare kunyarmu”. Cikin zubda ƙwallan murya a sanyaye Amina tace. "Akwai fa ranar da wlh Yah Amin ya samesu a hotol su biyu suka ritsashi wallahi a ranar da Yah Amin ya ɗaukeshi suka dawo sai da mukayi ta kuka saboda yadda ya rinƙa soshe-soshen jikinsa duk yayi jazir yana kuka fa yake cewa, baya so har cewa yayi a kaishi shari'a Court a yanke mai hukuncin kisa kawai yafi masa da wannan ƙazamar rayuwar. Fariyda in Allah ya baki kekkyawan ɗa ko ƴa dole sai iyaye sun dage da addu'a da nema musu kariya wurin Allah ya tsare mana yaranmu da sharrin shaidan da shaiɗanu mutane”. Ranar dai haka suka wuni gidan babu walwala, har sai bayan sallan isha Hafiz ya maida Amina Sulaiman da Mahmoud kuwa tun safe suna Parlour Abba ko salla anan sukeyi tayin jam'i dasu da Abba da Hafiz da Huzaifa, abincin da Amina ta kawo musu kuwa shine har dare dan ba wanda ya wani kula abinci. Bayan sun raka Amina sun dawo a parlour Ummi suka zauna cikin sanyi Ummi tace. “Fariyda kinji irin ƙaddarar Mahmoud ko”. Kai ta sunkuyar ƙasa cike da nauyi da kunya. Ita kuwa Ummi a hankali tace. “Ba haushe yace gani ga wane ya ishi wane tsoron Allah, kinga ishara akan Mahmoud dan haka ki dagewa yaranki da addu'a dan kyau ma wani lokacin masifane musamman in ya haɗu da kwarjini ga kuɗi, kuma duk girman laifin da yaranki zasu miki kar ki musu mugun fata da addu'a cikin fushi kinga Zaid sak Mahmoud ne ba inda ya barshi dan haka dashi da Zaitoon duk ki dage musu da addu'a”. Kai take gyaɗa tare da cewa. “In sha Allah Ummi”. Goggo Dada ta ɗauki Zaid dake kwance inda Huzaifa ya kwantar dashi ta tafi ɗakintata kwantar dashi, saboda tuni Hafiza ta musu wanka ta musu shirin bacci. “Sai da safe ko jeki kwanta dare yayi naga har goma ta wuce”. Cikin sanyi tace to tare da miƙewa ta fita. Mahmoud kuwa a hankali yake tafiya riƙe da kanshi ya iso parlour kukan Zaitoon da Samira da Hafiza suka barta a bedroom ɗin Fariyda ne yayi welcoming nashi. Ido a rufe yake tafiya har lau hannunsa duka biyu na riƙe da kanshi dan zafin Headache ɗin ya ƙara ta'azzara ne saboda miƙewa tsaye da yayi da haure upstairs ɗin haka yasashi jin tamkar kan zai rabe gida biyu. Yana shiga cikin ɗakin ya faɗa kan gadon tare da riƙe kansa gam-gam dan masifar sarawar da yakeyi haka yasa ya kasa yiwa Zaitoon komai ita kuwa ganinsa bai kulataba yasata fasa wani ihun da yasashi ƙara rumtse idanunsa dan ihun ƙara hautsina masa kai yakeyi. Da saurinta nufi bedroom ɗin dan jiyo ihun Zaitoon ɗin ganin shi a ɗakin ne yasa ta zaro ido tare da ƙarasowa ciki ta sunkuyowa kansa ganin yadda yake wani irin jujjuya kansa da jijiyoyin sukayi ruɗu-ruɗu sai zufa da ya keto masa ya taune lip ɗinshi na ƙasa da ƙarfi. Cikin sauri ta juya da sassarfa ta koma parlour Ummi tana faɗin. “Ummi! Ummu!! Appiy fa ba lfy Ummi zo kiga yadda yake yi fa”. Kusan a tare Ummi da ke kitchen ita da Sulaiman suka fito, Goggo Dada data fito ɗakinta na biye dasu. Suna shiga Goggo Dada ta ɗauki Zaitoon dake watsa ihu, Sulaiman kuwa saurin tallabo Mahmoud ɗin yayi, sai kuma ya kwantar da shi da sauri saboda jin sautin da ya saki tare da cewa. "Kaina zai fashe”. Da sauri Ummi ta juya ta koma parlourn Abba dan gaya mishi. Jim kaɗan da fitarta suka dawo tare da Abba. Da Yah Nasir a bayansu yana cewa Abba. “Dama ina anan waje a pharmacy na, yau nazo na ɗan dudduba yanayin kayanmu kafin inzo kuma Malam ya bani zuma wai in kawowa su Zaid a rinƙa lasa musu da safe, to da naga kamar dare yayine nace bari dai in kira Fariyda inji in batayi bacci a tura ko Hafiz ya karɓa, dana kiran ne na jita a rikice tace min Mahmoud ba lfy kanshi na ciwo in zo da Allah inzo da First Aidbox.” Ya ƙare maganar da saurin ƙarasawa cikin ɗakin saboda ganin yadda Mahmoud ɗin ke riƙe da kansa da hannu duka biyu duk jijiyoyin kansa sun tashi sunyi ruɗu-ruɗu gwanin ban tsoro hakama na hannunsa daya damƙe kan dasu, da sauri ya zauna a gefensa tare da buɗe first Aid ɗin abin gwada Bp ya ɗauka ya jawo hannunsa da taimakon Sulaiman ya gwada jinin nasa, sai kuma yayi saurin ɓalle wani ɗan ƙaramin mgnin a bakinsa ya sama tare da cusashi kasan harcensa, ɗan ƙaramin ledan drip ɗin da ya ɗauko a pharmacy ɗin nasa yaja ya haɗa allurai, kana ya maƙala mishi ƙarin ruwan. Fariyda dake zaune gefe ta kife kanta jikin gadon, a hankali Sulaiman ya gyara masa kwanciya saboda ganin ya sake kan nashi ya fara sauƙe ajiyan zuciya. Goggo Dada dake goye da Zaitoon ta sauƙe numfashi cikin sanyi tace. “Alhamdulillah yayi bacci ko”. Kai Dr Nasir ya gyaɗa yana mai gyara zaman hannunsa ɗaya ɗaurawa karin ruwan yace. “Jininsa ne ya haufa Abba me ya tayar mai da hankali har haka? Dama yana da hawan jinine? Me ya ɓaya masa rai har haka?”. Kai Abba ya jinjina a hankali ya ce. "Eh to yana da hawan jini tun lokacin rasuwar Aminullah ya sameshi, Amman daga nan bai ƙara hawaba, sai kuma yau ɗin dai ya tashi, saboda matsalar yar damuwar da ya samu kansa a ciki”. Yana tattara kayan aikin nasa yace. "Gskya Abba a kula dashi sosai domin kare lfyarsa jininsa fa ya hau mataki mafi muni, dan Allah a kiyaye ɓacin ransa, Fariyda ki kula”. Ya faɗa yana kallon Fariyda da tayi zuru ta zuba mishi ido, gyara masa kwanciya Sulaiman yayi kana ya sauƙo yabi bayan Nasir da Abba dake fita, a hankali Ummi tace. “Allah ya sauƙa ya bashi lfy”. Cikin sanyi Fariyda tace. “Amin yah Allah”. Goggo Dada na gyara masa rufuwa ta juya ta jawo remote ɗin Ac gudun AC ta ƙara tare da cewa. “To saida safe ko Fariyda, su Zaid a barsu wurina nima in samu abokan kwana, kinga ke ga mara lfy”. Cikin sanyi ta gyaɗa mata kai tare da binsu da ido. Kan bedside drawer ta zauna bayan duk sun fita, yana kwance lup alamun baccin yayi masa nannauyan kamu sai
Chapter 40 · 0% Book details