← Book details Sakar Makafi Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 19 OF 95

Sashe 19

Sakar Makafi Part 2 Complete Hausa Novel · about 4 min read

da ɗan T-shirt maroon color ya wurga mata, ya juyawa ya fita gami da ja mata ƙofar ya rufe da ƙarfi. Cikin rawan jiki ta miƙe ta jawo rigar da sauri ta zira gyara wuyan rigar ta farayi dan rigar tayi masa soko-soko sosai, sai kuma ta ɗago wonɗo da yake da roba mai faɗi a ƙugunsa, zirawa tayi ta ɗaura robar wonɗo kan rigar. Ɗan sunkuyowa tayi ganin wondon yazo mata har kan ƙaurinta. A hankali ta koma ta kwanta bayan tayi addu'a ta shafa, cikin duvet ɗin ta duƙunƙune tana shaƙan ƙamshin turarensa da yasata lumshe idonta in 3 minute bacci mai daɗi ya figeta. Cikin baccin da ya ɗaukeshi tun da ya fito parlour ya kuma jiyo kukanta, cikin sauri da hatsala ya nufi bedroom ɗin zaune ya sameta tsakiyar gadon tana ƙarƙarwa tamkar mazari tana ganinsa ta yunƙura ta miƙe da sauri ta diro ƙasa ta koma bayansa da gudu, hannunsa yasa ya koma hannunta da ƙarfi ya jawota gabansa ganin duk abinda take yi idon ta a rufe bisa dukkan alamu mafarki tayi. Bakin gadon ya kwantar da ita, da ƙarfi ya danneta sabida ganin ta yunƙuro zata kuma tashi cikin kasalar bacci yace. “Ke nifa zanci uban aljanunki, in ma sune ke sakaki ihu buɗe idonki ki ganni bafa zaki hanani bacci ba”. Kai ta fara jujjuyawa tana ci gaba da karkarwa. “Ina zakije?”. Ya faɗa yana zama bakin gadon ya tare inda ya kwantar da itan ganin ƴunƙurin sauƙa da alamun gudu take son yi. “Appiy”. Ta faɗa ba tare da ta kuma cewa komai ba dan jin irin riƙon da yayi mata. Mitsssss ya ɗan ja tsaki gami da cewa. "Gani nan buɗe idonki kiyi addu'a ba kiran Appiy ba ki buɗe idan ki kinga ba ƙare anan”. A hankali ta buɗe idonta ganinsa zaune a wurin ne yasata sauƙe numfashi, sai kuma ta fara jujjuya ido ganin ba karen a ɗakin kuma kofar a rufe ne yasa ta meda kanta ta kwanta cikin sanyi tace. “Ayyah Appiy dan Allah karka fita, wlh zai sake shigowa”. Ba tare daya kuma kallontaba, ya miƙe ya shiga bathroom Jim kaɗan ya fito da alamun al'wala yayi, ganin ya fitone yasa ta koma ta kwanta tana mai rufe jikinta zuwa wuya ta bar kanta a waje sai raba ido take cikin tsoro. Ajiyan zuciya ta sauƙe ganin ya shimfiɗa sallaya a gaban gadon ta inda take fuskanta wayarsa da ta nuna masa time ƙarfe uku ne ya ajiye gefen sallayar. Ido ta lumshe jin sautin karatun suratul sajada da ya ɗaura kan suratul Fatiha da ya fara. Nafila yaci gaba dashi, ita kuwa Fariyda sai bacci ya fara ɗaukarta sai kuma ta buɗe ido ta ɗago kai ta kalleshi in ta ganshi zaune ko tsaye sai ta maida kai ta kuma fara baccin da bazai wuce 6 minute to 10 ba zata kuma buɗe ido, duk abinda takeyi yana ɗan lura da abinda takeyi musamman yanzu da yake zaune yanakaratun Alqur'ani. Ƙarfe biyar saura bacci mai nauyin yayi awon gaba da ita. Sai da ya idar da sallan asuba yayi Azkarul Sabah, kana ya miƙe daga kan sallayar yana ɗaukar wayarsa ƙarfe shida harda kwata. Ido ya ɗan zuba mata ganin yadda take kanainaye da duvet ɗin ta kwaɓe fuska ta turo lip ɗinta na ƙasa, ta kama lip ɗinta na sama kuma tana tsotsa ta ciki, tamkar yar yaye, a fili yace. "Ashe ita Zaitoon ta gada bacci da tsotsan lips kamar tsohuwar mayya”. Sai kuma ya shige bathroom wanka yayi. Yana fitowa ya sameta zaune fuska a kwaɓe cikin murya bacci da tsoro tace. "Zanyi salla”. Jin sautin muryar tamkar na yara yan yayine yasashi harararta tare da cewa. “Na rufe gabas ko”. Tura baki tayi ta wuce bathroom ɗin, shi kuwa Mahmoud kimtsawa yayi cikin shigar mutanen Istanbul ɗin da weather ɗin yanzu ya fito parlour. Bayan tayi wanka tayi alwane ta fito a hankali tana leƙowa ganin baya nan ne ta gyara zaman bathrobe ɗin jikinta bakin ƙofar ta matso ta buɗe a hankali ta fara kiransa. “Appiy! Appiy!! Appiy!!!”. Ta kuma kiransa na ukun da ƙarfi. Sai kuma ta ɗan ja da baya ganin yadda ya turo ƙofar yana mata kallon da yasa ta yi ƙasa da kanta cikin Muryar bacci yace. “Gani cinyeni ko hankalinki zai kwanta, waima dan Allah me ya kawoki nan ne? Ni na nemeki ne”. Da sauri taja da baya jin yadda ya daka mata tsawa. "Nace me ya kawoki nan? Waya nemeki da zakizo ki addabi rayuwata”. Tana murza yatsun hannunta ido cike da ƙwalla tace. "Yah Saleh ne fa yace inzo, kuma salla zanyi Appiy”. A kufule ya zaro mata ido tare da cewa. "Ke karki sake kirana Appiy ke ƴatace da zaki cemin Appiy”......
Chapter 19 · 0% Book details