← Book details Sakar Makafi Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 5 OF 95

Sashe 5

Sakar Makafi Part 2 Complete Hausa Novel · about 9 min read

Lokacin da taji ya sake rigar tare da tureta can gefe da sauri ya sunkuyowa jin Zaid na riƙo ƙafarsa tare da faɗin.
“Owo Appiy”. Yana faɗin haka Zaitoon na buɗe ido, kusan a tare ya rungumesu dan tana buɗe ido tayi kashi, wuyansa suka maƙale a tare da fara yin dariyar farin cikin daya cire kasalar bacci daga jikinsu. Kissing nasu ya farayi tako ina, yanayi yana sunsunar ƙamshi jikinsu gami da faɗin.
“Yah Salam my Happiness kunyi missing Appiy ko”. Sake rungumesu yayi tare da matsesu a jikinsa ganin yadda suke ta maƙalƙale wuyansa.
“In sha Allah zamu raye tare, babu abinda zai rabamu, bazan ƙara yin nesa da kuba”. Yayi magnar yana kallonsu
Ganinsu fes-fes gwanin burgewane ya sauƙe numfashi saboda babu wani alamun tawaya ko yunwa ko datti.
Ita kam Fariyda tuni ta shige bedroom, jiki na karkarwa ta zauna bakin gado bugun zuciyarta dake bugawa da sauri da sauri take saurara tare da jin zufa duk da sanyin AC.
“Lallai ma na yarda wannan baida farillan mutunci bare sunoninsa kenan nufinsa tsirara zai min kawai dan nasa kayansa.” a fili tayi magnar yayinda zuciyarta ke duka tara-tara, kayan ta kalla cike da jin dadinsu a jikinta, idon cike da hawaye tace.
“Allah sarki Yah Amin shi in yaga nasa abinsa ma daɗi yakeji wannan mai fuskar Migambon kuma tsirara zai min dan tsabar rashin mutunci. Shine abinda take faɗi a zuciyarta.
Shi kuwa Mahmoud tuni ya fita dasu Zaid.
Zaune yake a office ɗin Dr Imran Patel, a bisa manyan sofa dake tsakiyar office ɗin. Cikin mmki yake kallon Mahmud ɗin bayan ya tambayeshi me ya hanasu zuwa da safe, yace masa ai baya gari yaje Kerala ne ɗazu ya dawo, tambayarsa me yaje yi a Kerala yasashi ce mai Dr yaje gani. Yana ɗan kamo Zaid tare da fara cire masa pampers yake tambayarsa wanne Dr yaje gani. “Dr Avinash”. Mahmoud ya bashi amsa a taƙaice. Da sauran Dr Imran Patel ɗin ya bar abinda yake yi tare da maida kallonsa kan Mahmoud gami da tambayarsa kanshi ya kaine? Ko wani yaje dubawa? Meke damunsa? Tun yaushe yake ganin Dr Avinash ɗin. A taƙaice yace masa shekaru goma kenan yanzu, yana kafeshi da ido ya nuna Zaid da Zaitoon yace.
“Yaranka ne?”. Kai ya gyaɗa masa cikin ƙosawa.
Da sauran Dr Imran Patel yace.
"Biological kids?”. Banza yayi masa, cikin sauƙe numfashi ya kuma tambayarsa a hankali yace masa yaran yayansa ne. Sai kuma ya kalli Dr Imran ɗin da ya jawo wayarsa ɗan lallatsa wayar yayi tare da kaita kunnensa alamar kira sai kuma ya kalli Mahmoud ɗin yace.
“Dr Avinash ubane a gareni babban ɗansa Aryan abokina ne, tare mukayi karatu, wasu lokuta kuma mamata ita ke tai maka masa da magungunansu na Chaina wurin warkar da masu irin larurar da take kaisu wurinsa, zan tambaye shi matsalarka da sunanka zai min bayani, tunda har kace 10 years kana ganinsa inaga matsalar babbace in ka yarda zan haɗaka da Dr Sarala”. Cikin sauƙe numfashi ganin ya kuma kiran dan na farkon ya tsike ba'a ɗaga bane yasa Mahmoud ɗin lumshe idanunsa a hankali yace.
"Waye Dr Sarala?”. Yana ɗan gyara zama yace.
"My Mom ita asalimta yar Chaina ce, babbanta babban mai bada maganin gargajiya ne da Chaina ke alfahari dashi, ta gaji babanta fiya da duk sauran yaransa, suna bada mgnanin ko wanne irin ciwo amman ita tafi ƙarfi wurin bada na maza yara da manya masu irin matsalar dake kaisu irin wurarenmu da wurin Dr Avinash”. Jin anyi picking call ɗin nasa ne yasa ya maida hankalinsa kan Dr Avinash ɗin dake masa magna. Sunan Mahmoud ya faɗa masa wanda yana faɗa Dr Avinash ɗin ya ganesa sabida tsawon shekaru goma suna tare yasa yayi masa farin sani, tambayarsa yayi me matsalar Mahmoud, amman sai yace dole sai Mahmoud ɗin ya amince kafin ya faɗa masa sirrinsa haka yasa ya bawa Mahmoud ɗin waya yana ƙara ce masa. "Ina so zan taimaka maka kaga Dr Sarala in sha Allah in dai ta baka mgni kayi amfani dashi to komai zai wuce in kuwa bai wuceba to kawai sai dai ince maka ka haƙura da neman mgnani kawai a rayuwarka”. Amsar wayar yayi sukayi magna kusan 6 minute to 23 seconds kana ya miƙawa Dr Imran Patel ɗin wayar.
Cikin sauƙe numfashi Dr Imran ɗin yayi shiru yana sauraron bayanin da Dr Avinash ɗin ke masa, kusan 18 minutes sukayi kana ya katse wayar tare da cewa, juyowa yayi yana kallon Mahmoud ɗin yace masa Dr Avinash ɗin zai turo mashi dukkan bayanan lafiyar Mahmoud ɗin dama iya adadin nakasarsa duk ya gani a system nashi.
Ido Mahmoud ɗin ya zuba masa jin yana faɗin. Zai duba duk files ɗinsa zai nazarcesa kuma zai haɗa mamansa da Dr Avinash ɗin ya mata duk bayani, in sun gama zai zo ya ɗaukeshi suje har gida wurinta. Miƙewa Mahmoud ɗin yayi yana mai jawo hannun Zaitoon ya nuna masa Zaid alamun ya dubasa, kan gadon dake gefen wurin ya kwantar dashi gami da fara yi masa gwaje-gwaje da latse-latse da dube-duben da ya tabbatar mai da lfyar Zaid ɗari bisa ɗari. Mahmoud dake gefensa ya nunawa ɗan kaciyar Zaid ɗin da ya tashi tsaye cir yana ɗan harbawa irin ta lafiyayyun yara.
Hamdala yayi tare da tabbatar masa Zaid bashi da wata sauran matsala da zatayiwa mazantakansa barazana ya samu lfy dari bisa dari. Magunguna ya rubuta musu a take ya tura pharmacy ɗinsu ta system, jim kaɗan da turawa sai ga wata Nurses da ta shigo musu da ladar magunguna, amsa yayi ya yi masa bayanin yadda za'a bashi, cikin jin daɗin warakar Zaid ɗin ya rungume Dr Imran Patel ɗin kamar yadda shima ya rungumeshi, kafaɗarsa ya ɗan buga yace.
"Na gama da matsalar ɗa, sauran ta uba itama in sha Allah Dr Sarala zata medashi garay fiye da 10 years back”. Ɗan lumshe idonsa yayi tare da jin wani tsammani na musamman a cikin rayuwarsa ya ɗan motsa lips ɗinshi a hankali yace.
“Issue nafa is very very Dangerous”. Cikin jinnina kai gami da tuno ɗan bayanin da Dr Avinash yayi masa na sanadin samun matsalar tasa yace. "In sha Allah zamu gwada”.
Washe gari da safe bayan ta tafi Restaurant ɗin hotel ɗin dasu Zaid, Video call yake yi da Sulaiman Salim da Dr Fadil da Usman da dai sauran abokansu dan yau ne za'ayi dinner ɗin Salim da Salma duk parlour cike yake da abokansu wasu tun na primary school wasu na Secondary school wasu wanda sukayi karatu dasu a Texas ne. Yahaya ne ya leƙo fuskarsa cikin tsareshi da ido yace.
“Kawai ina shiga Airport a Lagos sai ga Idaya”. Da sauri ya rumtse idanunsa sai kuma ya buɗesu jin Yahaya nace masa.
“Tunda ta ganni ta tsareni da tambaya dole na faɗa mata auren Salim zanzo.”
Da sauri Hadi yace.
“To kenan tana cikin Kano dan tabbas naga wata a hotel ɗinmu da muka fara sauƙa kamar ita”. Yahaya ne yace. "Eh tana nan da zata zo auren ma jin Mahmoud baya nanne yasa tace bazata zoba, amman ta matsa min wai in kaita gidanku”. Da sauri Sulaiman yace.
"In kana yiwa Allah da Manzonsa da darajar iyayenmu kada ka kai mana idaya gaban iyayenmu, duk zuriyarmu bama fata da burin ƙara ganin fuskantar ko jin sunanta bama so, ita da Sara, wlh zuciyar Abba dasu Ummi zasu iya bugawa in sun ganta”. Da sauri Yahaya yace.
"Wlh bazan kaita ba, dan nasan irin illar da tayiwa Mahmoud a school”. Numfashi mai nauyi Mahmoud ya fesar cikin yiwa Salim kallon takaici kana ya kauda mgnar da cewa a bawa Hadi waya, nanfa suka ɗan gaisa dasu ɗaya bayan ɗaya”.
Yana katse kiran ya ɗauki wayar Yah Amin da Sa'ad keta kira ba ƙaƙƙautawa ba yabo ba fallasa ya amsawa Sa'ad ɗin sai kuma ya ɗanyi shiru yana sauraron duk ƙorafinshi da magiyarsa cewa Fariyda fa bata bashi number taba kuma bata yin mgna ko an bata waya in ya kira, gyara riƙon wayar yayi jin Sa'ad ɗin ya gama mgnarsa yana lumshe ido cikin yaƙinin sanin abinda ya gayawa Abba dole ne zai datse igiyar auren da suka ƙaƙaba mishi da kansu.
“Sa'ad nifa ba sonta nakeyi ba, amman kuma ina gudun saɓawa iyayena akanta, shiyasa nake tunani kafin yanke shawarar komai. Alhamdulillah yanzu inada tabbacin iyayenmu da kansu zasu raba auren kamar yadda suka haɗa bamu saniba haka zasu raba aure. Dan haka kayi haƙuri ka daina damuwa da kiranka da bata ɗagawa, da rashin yin waya da ita, next week zamu koma. Kuma muna komawa zasu bani umarnin sakinta kamar yadda na tsara, ina sakinta da kaina zan gaya maka, sai kazo da iyayenka a nemi auren a gaban iyayenta dan haka kada ka damu, ka daina takurawa rayuwata da kira ni zan nemeka in lokacin yazo”.
Cikin tsananin jin dadi Sa'ad ɗin yace.
"Ngd amman zan rinƙa kiranka muna gaisawa”. A daƙile yace.
“Ba buƙatar haka”. Daga nan ya katse kiran yana mai jaddadawa kansa ana bashi umarnin sakinta yana bata takardar zai gayawa Sa'ad ɗin.
Bayan kwana biyu zaune suke a cikin garding ɗin gidansu Dr Imran Patel, wanda garding ɗin bawai na kayan marmari bane da ƴaƴan itatuwa ba, zalla tsirraine na magungunan gargajiya da jijiyoyin da gadalulluka irin na ƙasar Chaina da wasu nan na. India wasu ma na Afirca ne wasu nada ya'yan itace wasu babu,
Miƙewa tsaye tsohuwar bachainiyar mahaifiyar Dr Imran da ta gama jin dukkan bayanan da ɗan nata yayi mata da ƙarin bayanin da Mahmoud ɗin ya ɗanyi mata, yan ƙananan idanunta da suke kamar babu ta ɗan fidda tare da kallon Mahmoud ɗin sama da ƙasa, hannunta tasa jikin wata yar guntuwar bishiya ganyeta ta tsinko a ƙalla goma, Dr Imran ta miƙawa su tap ɗin dake wurin ya buɗe ya wonkesu fes tare da sasu cikin plate.
Amsa tayi ta miƙawa Mahmoud ɗin tace ya cisu haka, da mmki yake kallonta, a ranshi yake mgnar zuci, Sufa waɗannan illarsu kenan su cin komai, Allah yasa ma kada ta kwaso wani ƙwaron tace inci”
Jin tana jaddada masa yacine yasa ya ɗan kalli ganyen irin masu laushin nanne kuma sun wonku fes sai sheƙi suke yi, a hankali ya sunkuya ya ƙara wankesu kana ya ɗauki tsilli ɗaya ya ɗan datsi gefensa ƙara kallon ganyen yayi sabida jin yadda ɗanɗanonsu da garɗi-garɗi gami da ɗan gafi-gafi kaɗan ya fara bin jijiyoyin harshesa da gudu suna gilanwa cikin duk jijiyoyin jikisa manya da ƙanana. Sunkuyawa tayi ƙasa wani yaɗon ganyen me haɗe da jijiya jijiya ta ɓallo da ƙarfi, ta bawa Dr Imran amsa yayi ya wanke da sauri ya miƙawa Mahmoud tare da cewa ya manna bakin jijiyar a harshensa. Ganin yadda ya wankeshi ne da yadda wani farin nono ke tsatstsafowa bakin jijiyar ne da sani likitane na musamman yasa ya amsa tare da mannawa kan harcensa, da ƙarfi ya rumtse idanunsa tare da damƙe hannunsa saboda jin yadda jijiyoyin hannunsa suke mimmiƙewa.
Ita ko Dr Sarala kai ta jujjuya cikin taraddadi da rashin yaƙini samun lfyarsa sabida ganin abinda take son ganin ya miƙe bai miƙeba, a hankali taci gaba
zagayawa dashi cikin ɗan labun gonar maganin tana tsinkan ganyayyakin da jijiyoyin tana bashi wasu yaci tace ya haɗiye wasu tace ya manna a harshe wasu tace ya tauna ya tsotsi ruwan kamar jikin asuwaki ya tofar da diddiga. A hankali ya zauna kan kujerar bayansa yana mai jin cikinsa na hautsinewa saboda ciye-ciyen ganye.
Wasu data wanke ta fara yankawa siri-siri ta wankesu fes ta sasu a wani ɗan roba mai kyau ta rufe ta miƙa mishi tana faɗin duk abinda zaici ya rinƙa daurawa a kai. Gobe da yamma su dawo kamar yanzu.......
Chapter 5 · 0% Book details