Sashe 18
Sakar Makafi Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Da sauri ya ɗan kalli ƙofar bedroom ɗin nasa sai kuma ya rumtse idanunsa saboda gigitaccen ihun Fariyda da yaji ya ratsa masa kunne. Towel ɗin dake ƙugunsa ya ɗan gyara ɗaurawa bisa alamu yanzu ya fito wanka. Ɗan ƙaramin towel dake hannunsa ya ɗaura kan sumar kansa yana gogewa a hankali cikin rashin kuzari. Ido ya zuba wa ƙofar ɗakin jin yadda take ihun babu ƙaƙƙautawa ihun neman maceci takeyin tamkar zata ari baki. Tanayi tana zagaya parlour da iyakar karfin gudunta da yarfa hannunta ganin yadda karen ke binta duk inda tayi yanayi haushi mai tsinka zuciya. cikin tsananin kiɗima tashin hankali da firgici take ihu da gudun da sai yanzu ta samu ta shiga corridorn. Hannunsa yasa ya dafe kansa da karfi saboda ihunta da haushin karen sun haɗe sun cika ko ina a gidan, kamar an jefota haka ta shigo cikin ɗakin cikin gudun ceton rai ta nufeshi da neman ceto. "Wayyo Allah na, wayyo Appiy ka taimakeni zai kasheni”. Ta ƙare maganar da ƙarfi ta koma bayansa ta abka jikinsa ta rungumeshi cikin firgicin neman ceto. Bayanshi karen ya koma yana haushi da tsalle. Karƙarwa yaji jikinta nayi wanda har hakan yasa nashi jikin tsuma, bugun zuciyarta na bada sautin da har a bayansa yakeji, da sauri ya juyo haka yasa karen ya zama a gabansa ita a baya tana maƙale dashi. Cikin rawan jiki ta diro daga bayansa data maƙale ta nufi ƙofar bathroom dake can gefenta, da ƙarfi ta tura ƙofar ta kutsa kai ciki ganin karen ya kuma biyota ne yasa tayi saurin kutsawa ciki da gudu. Suuuuu santsi ruwa ya kwasheta ya watsata cikin bath ɗin da ruwan wankan da yayi yanzu yake cike dan wanda ya tsiyaye bai kai rabi ba. Ƙofar da ƙafarta ya meda ya rufe ne ya hana karen samun damar binta sai haushin da ya tsaya yanayi a bakin ƙofar tare da yagushin ƙofar, saboda bai santaba gashi dare ne gani yake kamar mugun nufine ya kawota. A hankali ya zauna a bakin gadon ya fara kiran karen wanda haka yasa ya dawo gabansa hannunsa yasa kanshi yana ɗan shafawa da ɗan bubbugawa bayansa kaɗan kana ya nuna masa hanyar fita. Ba ɓata lokaci ya juya ya fita yana kaɗa bindi. Ido ya zubawa ƙofar bathroom ɗin yana jin sautin kukanta tamkar ranta zai fice ya bar gangar jikinta. Cikin tsuƙe fuska ya tura ƙofar bedroom ɗin da sauri ta miƙe tsaye daga cikin bath ɗin shar-shar haka ruwa ke tsiyaya daga jikinta ba inda ya rage a jikinta da bai jiƙeba. Cikin rawan jiki ta fito daga cikin bath ɗin sai kuma tayi saurin zamewa ta zauna a ƙasa ta jingina da jikin bath ɗin saboda rawa da sawunta sukeyi bazasu iya ɗaukarta ba, ga wani irin zogi zut-zut da singalalin ƙafarta keyi wacce ta buge da bakin bath ɗin. Ido ya zuba mata cikin mmki ganin yadda jikinta yake ƙarƙarwa tamkar mazari. Sunkuyowa yayi kanta tare da sa hannunsa ya kamota ya miƙar da ita tsaye ido ta buɗe cikin rawan azabebben sanyin garin da sanyin jiƙeƙƙen kayan ruwan da tafaɗa da kuma rawan tsoro da firgita ga zafi buguwa ƙafarta da tayi a bakin bath ɗin haka yasa hatta lips ɗinta rawa sukeyi. Cikin firgitaccen yanayi ta kalli ƙofar bathroom da ya bari a buɗe ganin karen na kuma shigowa cikine ta saki ihu tare da faɗawa jikinsa tace. “Appiy ka taimakaneeeyyy”. Taja ƙarshen mgnar can ƙasan maƙoshinta cikin sasssyan sautin sumewa lip tayi a jikinsa, yadda tayi tsit a jikinsa haka shima yayi tsit a tsaye tamkar wanda aka dasa, a hankali yake fesar da numfashi sauraron bugun zuciyarta da duk da sumewar da tayi yake harbawa da ƙarfi cikin sauri-sauri, kanshi ya ɗan sunkuyar yana leka fuskantar idonta dake lumshe kamar mai bacci ya kalla yana mai ƙara tabbatar da suman da tayi, numfashi ya fesar saboda sanyin jikinta daya fara ratsa mishi jiki har zuwa ƙashi, towel ɗin dake ƙugunsa ya kama da hannunsa ɗaya ya ƙara gyara ɗaurin tamau, yana jin sanyin towel ɗin da ya jiƙe da ruwan jikinta dake ɗiga, a hankali ya ɗan tallabo haɓarta ya fara ɗan marinta kaɗan kaɗan gami da cewa. “Ke! Ke!!! Ke!!! Ki tashi”. Shiru ba motsi bare ta amsa, karen da yake haushin ya hamɓare da ƙafarsa ɗaya, gami da tattaro kuzarinsa yayi masa tsawa da masa nuni da waje, a guje ya juya ya fita ya bar corridor baki ɗaya ya koma parlour yana haki. Tallaɓeta yayi da kyau ya matso kusa da wurin alwala ruya ya tare a bakin tab ɗin ya watsa mata afuskarta da ƙarfi, shirun da ya ganine Yasashi ƙara yarfa mata ruwan kan fuskarta har lau shiru, a karo na uku ya kuma ciki hannunsa ya yarfamata kan fuskarta zuwa wuyanta har lau dai dib ba motsi, numfashi ya fesar saboda rawan sanyi da jikinsa ya fara, ganin kamar ta danskarene ya sashi kallon yadda kayan jikinta ke jiƙe jagab. Shiru yayi yana mai nazarin abin yi kusan 4 minute yayi a tsaye da ita a haka. Numfashi ya fesar cikin sanyi ya rumtse idanunsa da ƙarfi, hannunsa ya ɗaura kanta jersey veil ɗin da tayi Rollin kanta dashi wanda shi bai jiƙa sosaiba ya fara warwarewa, tare da cillashi gefe, sai kuma ya ɗaura hannunsa kan wuyanta Scarf din da ta naɗe a wuyanta ya fara ƙwancewa a hankali ya ɗan naɗe yatsunsa uku da iya babbar yatsarsa da manuniyarsa ya kwance shi, har lau kuma idansa na rufe kib kamar yadda ya taune lip ɗinshi na ƙasa da ƙarfi haka idonsa yake duk abinda yake yi da hannu ɗaya ne ɗaya hannun kuma shike tallaɓe da ita ya hanata faɗuwa da kuma rabata da jikinsa. Cikin sanyin daya fara tasiri a jikinsa ya fara ɓalle boturdin long coat ɗin dake saman riga da wandon jikinta, a hankali ya zareshi daga jikinta ya wur gashi kan washing machine dake gefensa, hannunta ya kamo ya matse da lafaɗarsa gloves ɗin da suke ta ɗiga da ruwan da tuni yayi sanyi ya zaresu duka biyu, sai kuma ya ɗanyi shiru har lau idonsa a rufe, jin yadda tayi nauyi tayi baya ne saboda wuyanta daya koma baya yashi gyara tsayuwar da kyau yadda bazata rinjaye shi ba. A hankali yasa yatsunsa ya fara ɓalle botur ɗin Sweater, yana mai ƙara rumtse idansa ya zare rigar ya cilla kan sauran kayan nata, numfashi mai nauyi ya fesar haɗe da tsuƙe fuska da jan dogon tsaki yana ƙara tallabota jikinsa yayi dan yadda take sake yasa tana gab da jawoshi suyi ƙasa ga ƙarfin alluran da har yanzu basu sake shi ba, sai kuma ya ƙara rumtse idonsa da ƙarfi jin yadda sanyin fatar jikinta ya manne da fatar jikinsa, ƙasa yayi da hannunsa tare da zuge zip ɗin ƙugun wondon ya fara ƙasa dashi duk idonsa a rufe ya zareshi har ƙasa hannunsa ya miƙo ya jawo towel ɗin dake saƙale a gefe, da sauri ya ɗaura matashi kan bra and pants wanda yake har guiwarta, a hankali ya tallabota ya ɗagata cak ya fito ido a rufe yake tafiya cikin rashin kuzari yace. “Metsss mutum kamar tsinken sakace sai rashin kunyar ƙarya da tsoro kamar farar kura”. Kan gadonsa ya direta tare da jawo duvet ɗin ya rufeta kirib sannan ya miƙe tsaye ya juya ya fuskanci wardrobe ɗinsa kafin ya buɗe idonsa . Cikin sauri-sauri ya kimatsa jikinsa, room heater ya kunna yana ɗan kallonta ya taɓe baki ya fito. Parlour ya dawo cikin shigar pajamas milk color masu kauri da taushi. Ledan da Yah Saleh ya ajiye a kan Dinnin table ya kalla a fakaice sai kuma ya wuce kan 3 seatter ya zauna yana kunna TV yana ɗaura ƙafarsa kan Centre table ɗin gabansa, boxing akayi shiyasa hankalinsa duk ya tafi kan TV. A hankali ta fara jujjuya kanta da ƙara jan numfashinta da ƙarfi take jin wani irin sassayan ƙamshi da shine ya farfaɗo da ita daga suman, a gigice ta yunƙura da sauri ta rufe idon tana ƙara jan duvet ɗin haɗe da sakin ihu da disashesshiyar muryarta tana jujjuya kai. Tsaki mai tafe da gajia kasala da bacci yayi yana kallon karen da ke kwance a gefensa tuni yayi bacci, ihunta da ya kuma jine yasashi nufar bedroom ɗin. Ido a rufe take ihun tana yarfa hannunta da ƙarfi tare da mummurza ƙafafu. "Ke! da Allah me haka?”. Yayi mata magna cikin tsawar da tasa tayi saurin rufe bakinta a hankali ta fara buɗe idanta cikin rawan murya take faɗin. “Kare! Kare!! Kare!!! Wayyo wayyo Allah na Appiy kareeeee!!!!!”. A kufule yace. “Ke baki da hankali ne zaki addabi mutanen anguwa da ihu, yanzu ina kika ga karen da zaki toshe min kunne”. Cikin tsoro ta ƙara buɗe idanta tare da sauƙe numfashi tsoro, ganinta ba karen ne yasa ta kwaɓe fuska ta tura baki sabida ganin kallon takaici da yake danna mata. Cikin rauni tayi ƙasa da kanta, sai lokacin ta lura daga ita sai bra and pants wani ihun ta kuma sawa ta kife ƙirjinta kan guiwowinta tana jawo duvet ɗin. “Ke zan ɓallaki fa, nine karen da zaki kalleni kisa ihu”. Cikin rumtse idonta da ƙarfi take magna haɗe da kuka. "Kayana ina kayana waya cire min kayana”. Harara ya watsa mata yana taɓe baki ya juya ya fita yana faɗin. “Shirmen banza da na barki da su ai da tuni sanyi ya kasheki kija ace ni na kasheki”. Sai kuma ya dawo da baya jin taci ga da kukan da yarfa hannu da cekiyar kayanta a hatsale yace. “Kin san Allah in kin ƙara min ihu zan turo miki Karen nan ki kwana dashi kan gadon nan”. Da sauri tasa hannunta ta rufe bakinta tana mai girgiza kai gami da mishi alama da hannu ɗaya alamun tayi shiru. Kwaffa yayi kana ya juya zai kuma fita yana kallon time ƙarfe ɗaya harda minti arba'in na dare da sauri tace. “Ina kayana”. Sai kuma kawai ta fashe da kuka mai cike da takaici murya na rawa tace. "Tsinennen kare ya yaga min kayana.” ta gefen ido yake kallon yadda take kukan da rufe baki, Wordrobe ɗinsa ya buɗe, wasu tattausan riga da wanɗo 3 quarter fari