Sashe 17
Sakar Makafi Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Da sauri Sajida ta miƙe tare da isa inda take a hankali tace.
“Wow Aunty Farriyyha kinga yadda kikayi kyau kuwa, wlh sak Azra ɗin Rayuwata ko kalar fatarki irin ta mutanen Istanbul ne kinyi kyau sosai”. tana ɗan lumshe idanta da takejin sun mata nauyi dan sun ɗan kumbura sabida kukan da tayi cikin jin sanyin garin tace.
“Ngd Yah jikin Appiy”. Ta tambaya tana wucewa ciki. Numfashi ta ɗan fesar tana zama kan kujera. Su Aunty Maryam da Amira na shigowa. Sajida kuwa babybag ɗin ta amsa a hannun Arda.
Amira ta matso bakin gadon. Cikin yauƙi da ƙarfin guiwar da Aunty Maryam ta bata na cire tsoronsa a ranta ta daina shayinsa ta zama jajirtacciya ne yasa ta ɗan kalli lips ɗinshi da yake motsawa yana magna da Abba dasu Ummi. “Ummi nifa ba abinda nakeji, Abba ba sai kun zobafa na warke bana jin komai”. Sai kuma ya ɗanyi shiru yana ɗan kallon Fariyda da gefen ido yace.
“Gata nan”. Shiru ya ɗanyi jin Abba na cewa.
“Yanzu dai tayi shiru ko? Bata kukanko? ta samu tayi bacci”. Idanunta da suke kumbure da bada wani launi na da ban ya kalla a fakaice sai kuma ya miƙa mata wayar jin Ummi na cewa.
“Bata waya”.
A hankali tace.
“Hello Ummi Alhamdulillah jiki da sauƙi bai sake yin amai ba ma”. Cikin yauƙi da ƙwarƙwasa Amira tace.
“Baby insa maka abinci”. Shiru yayi kamar bai jitaba sai kauda kansa da yayi gefe.
“Baby bana son ka zauna da yunwa dan Allah ka daure kaci wani abu”.
Ido Fariyda data gama waya ta zuba mata, sai kuma tayi murmurshi mai cike da sanin waye Mahmoud ɗin.
“Please Baby ka tashi”. Wani irin kallon daya hautsina mata hanjin cikinta ya watsa mata sai kuma ya ɗan nunata da yatsa yana kallon Aunty Maryam yace.
“Nifa zan zagi uwarta in bata daina matsa min ba ki gaya mata ko a mafarki in ta sake cemin Baby wlh in ta farka tayi sadaka, bana son in zagi kan uwar tane dan kar kiji ba daɗi, dan haka ki gaya mata kar ta sake zuwa inda nake in ba haka ba zanci uwarta”. Murmurshi gefen baki Fariyda tayi a ranta tace.
“To kuma zagi na nawa ka zageta kace wai bazakayi zagi bane sabida kar taji ba daɗi, ba lfyar ma ba sauƙin masifa mutum kamar wuta.
Aunty Maryam kuwa Fariyda take dannawa harara.
“To me haka ke nufi ganin Fariyda a wurin ne yasa ya gigice da masifa, tunda bai taɓa zaginta hakaba sai yau sai dai yaja tsaki ko yace zai ƙwaƙule mata ido, ke nan ma shi yakeyiwa Fariyda kishin kansa da kansa ko yaya, me haka ke nufi”. Ita kam Amira tuni ta fice tana zubda ƙwalla.
Sajida ku fita tayi can waje dariya harda riƙe ciki a fili tace.
"Dadina da Yah Mahmoud kenan ai shi wutane maganin zuma, munafukai kun mallake Yah Saleh da yake shi mai sauƙin kaine ai Yah Mahmoud kam bazai samu da sauƙi ba, dan shi ba irin su Yah Saleh da Yah Ahmad da Yah Amin bane, su waɗannan team ɗinsu Yah Mahmoud da Yah Salim basu ɗaukar raini gwarama Yah Sulaiman shi ne ma mai ɗan sauƙin kai”.
Wuraren magrib Dr yazo ya dubashi tare da sallamarsa dan Alhamdulillah jiki da sauki bai ƙara aman ba, sai dai ɗan rashin kuzari da jirin da yake ɗan ji kaɗan.
Saida sukayi sallan magrib da isha kafin suka koma.
Yah Saleh ya kalli Fariyda data fito bayan motarsa tare da Sajida dan su Aunty Maryam tun da yamma suka dawo.
“Zo muje ciki ki ɗauko muku abinci Fariyda”. Ya faɗa cikin kulawa da sanyin hali irin na Yah Amin, Sajida na gyara riƙon Zaitoon ta yi gaba, shi kuwa Yah Saleh Fariyda ya kuma nunawa hanya yace.
“Muje ko, kinga tun jiya baici komai ba, gwara da muna asibiti drip zai riƙe masa ciki”. A hankali ta gyara riƙon Zaid daya fara bacci tabi bayan Sajida cikin rasa ta ina zata ce masa shifa Mahmoud ba abincin kowa yake ciba, gate ɗin gidan nasu ta kalla cikin mmkin sauyin tsari da gyara da akayi masa duk ta irin gate ɗin nan mai raga-raga da kana iya hango harabar gidan motarsa da ke parking lot ya tabbatar mata yana cikin gidan kenan dan shi tare da Arda suka dawo dasu Imran, sanyin da ake busawane yasa tayi saurin yin cikin gidan Yah Saleh.
A parlour suka samu Aunty Marym da Imran yana ganinsu yayi saurin zuwa ya rungume babansa sai kuma ya rungume Fariyda tare da miƙa mata hannun ya amshi Zaid.
Sajida dake ce masa.
“Yauwa Imran kawoshi in musu wanka kafin suyi bacci.
Ita kuwa Fariyda numfashi jin daɗin ɗumin dake cikin parlour ne yasata lumshe idonta.
“Maryam kawo abincin Mahmoud ta kai mishi”. Tana yiwa Fariyda wani mugun kallo tace.
“Banyi dashi ba”. Cike da mmki yace.
“A'a kamar ya zakice bakiyi da shiba”. Cikin takaici da baƙin ciki ta kalli Amira data fito ido a kumbure dan kuka kwaffa tayi kana tace.
“Sabida ban shiryawa karɓar zagin iyayena ba”. Kai Fariyda ta sunkuyar cikin taɓe baki. Yah Saleh yace.
“Kamar ya zagin iyaye daga nace ki kawo abincin Mahmoud sai kice baki shiryawa zagin iyaye ba”. Cikin fusata tace.
“Eh saboda zagemin iyaye da yayi na safema ya isheni dan kawai yaga Allah ya jarabci Amira da sonshi, tun asuba da wannan uban sanyin Istanbul ɗin ta fita sayo wani abun ma da ta samu ya ƙare, tazo dani da ita duk bamu hutaba muka shiga kitchen mukayi masa girki, muka kai masa kawai dan ta nuna kulawarta ya tashi ya fesa mana rashin mutunci ka sanshi dama ya iya ya saba ya ƙware a tijara haka a gabana ya zage mana iyaye fes daga taimako, wai kawai dan Amira tace masa ya tashi ta zuba mai abinci yaci, harda cewa zaici kan uwarta”. Ta ƙare maganar cikin jin takaici.
Ita kuwa Fariyda Amira take kallo cikin taɓe baki.
Mace kamar ba maceba ta yaya ma akan na miji zata zubda kunyarta da kimarta har ya wani rainata madallah gobema ta ƙara in dai wannan ɗan bala'inne abinda yafi haka ma zai mata, mutumin da ba'a masa gwaninta shi da kansama yake faɗa shifa ba'a masa gwamnatin sai kace abun kirki, dama ta nemi masu mutunci tace tanaso da yafi mata dan shi dai wannan bashi da farillan mutunci bare sunoninsa.
Masifar da Aunty Maryam keyi ne ya dawo da ita daga mgnar zuci da take yi.
“Wallahi bazan sake bashi ko ruwan gidana ba, in kaga dama ka kaimishi in ma girki zakayi ga kitchen ga komai ka shiga kayi masa, ni dai Maryam bandani, to ma wai ba ga matarsa ba ita yar idoce da bazatayi masa girki ba”.
A hankali ta maida kallonta kan Amira dake cewa.
"Please Aunty Maryam ni zan mishi, tunda ya nema”. Ido Fariyda ta ɗan jujjuya jin wai a zatonsu shi ya nema.
Yah Saleh ne yace.
“Fariyda muje Restaurant in sama muku abinda zakuci ki kawo muku ko”.
Cikin sanyi ta jujjuya kanta tare da cewa
“Ba komai Yah Saleh zai yi wuyama yaci wani abu yanzu sai dai zuwa safe”.
sai kuma kawai ta jujjuya tare da cewa.
“Sajida kawo su Zaid mu tafi”.
Cikin bada umarni Yah Saleh yace.
“A'a barsu zasu kwana nan wurinmu Sajida zata kula dasu, ke kije ki kula da Mahmoud ɗin kar a barshi shi kaɗai dan har yanzu bai gama warwarewaba kar abun ya tabashi bama fata”.
Jim ta ɗanyi sai kuma dai ta juya a hankali tace
"Aunty Maryam saida safe”. A kufule tace.
“Umma ta gaida ashsha”.
Yah Saleh ya bi bayanta yana faɗin.
“Kiyi haƙuri Fariyda Muje in sama muku abinda zakuci ko”.
Tana kallon gate ɗin gidansu Mahmoud ɗin tare da ƙara rufe jikinta da kyau da azabebben sanyin da yayi mata rumfa lips na fara rawan sanyi tace.
"Alhamdulillah yah Saleh wlh ka bari”. Cikin sanyinsa ya tura mata ƙofar ta shiga yana mai kallonta yace.
“Shiga ke kam ina zuwa zan kawo muku abincin”. daga nan ya juya ya shiga motarsa
Cikin rawan sanyi ta fara taka steps ɗin gaban parlour da sauri ta ɗan matsa ganin an buɗe ƙofar Arda ne ya fito cikin shigar kayan sanyi.
Gefe ya ɗan ja ya mata sannu da hanya.
Cikin rawan sanyin ta kutsa kai cikin parlour wai ko zata samu ɗumin ciki, meda ƙofar tayi ta rufe tana ƙara kamƙame jikinta saboda jin parlour sanyi kamar waje, numfashi mai sanyi ta fesar ganin room heater ɗin a kashe kuma basu kunna wutaba a hankali tace.
“Shi mutum yana nan kamar shuka son sanyi duk sanyin garin nan amman ba room heater”. Tayi mgnar dan tunowa da yadda yake baza AC a kansa.
A hankali ta ɗan tura ƙofar tolet ɗin parlour gim ta jisa a rufe.
Cikin ƙarƙarwa ta ƙara matse jikinta wuri ɗaya.
Corridor ɗin dake gefen dama ta kalla wanda zuwansu da Yah Amin a ɗaya daga cikin bedroom ɗin dake wurin suka sauƙa.
Sai kuma ta kalli na gefen hagu inda Yah Amin yace nan su Abba ke sauƙa sai kitchen dake tsakaninsu
Cikin rawan sanyin ta ƙusa kanta corridor ɗin.
tana mai ɗan kallon ƙofar kitchen ɗin sai kuma ta juya kanta da sauri ta kalli dinnin area kan steps ɗin haurawa wurin dinnin table ɗin tayi ido biyu da katra da ya miƙe tsaye tare da nufota yana zare harshe da kaɗa binɗi..........
By
*GARKUWAR MARUBUTA**SAƘAR MAKAFI*
Page 52
Na
*Aysha Aliyu Garkuwa*