Sashe 36
Sakar Makafi Part 2 Complete Hausa Novel · about 9 min read
Ya sauƙe numfashi haɗe da ƙara manna bayanta da ƙirjinsa har tana jin bugun zuciyarsa.
Tana mutsu-mutsun kwace hannunta tace.
“Ni ka sakeni ba mgnar da zanyi da kai, Abba yana jirana”. Matse hannunta da yayine yasata sakin ɗan ƙara tare da manna bayanta da kirjinsa da ƙarfi, cikin magiya tace.
“Dan Allah ka sake min hannuna”. Gefen lip ɗinshi na ƙasa ya datse da haƙoransa biyu, yana kallonta ido cikin ido yace. “Zan ɓallaki in baki nitsu kin gaya min dalilin da yasa duk wani mayen mata da ya tareki yace yana sonki kike basu number wayata ba, wlh sai na karyaki ba targaɗeba akan me kike basu digit na?”. Ya ƙare maganar da ƙarfi tare da matse hannunta duka biyu cikin hannunsa ɗaya, da sauri tayi ƙasa da idonta wanda rabon da ta kalleshi ido cikin ido tun ranar da yayi mata tijarar nan a hotel a Lagos tana jujjuya kai tace. "Wallahi ni ban basu number kaba number Yah Amin nake basu”. A kufule yace.
“Baki da hankali ko Yah Amin ne yake amsa call ɗin matsiyata yan jarabar banzaye masu kama da mata maza da kike bawa number ko ni, baki san wannan wayar aikin Company bace, to wai baki da wayane?”. Kai ta fara jujjuya mishi haɗi da cewa. "Ina dashi”. Murya a fusace yace.
“To meyasa bakya basu taki sai number company wacce muke business zaki bawa ko wani shegen Sa'ad ya addabeni kin kuma ƙarowa wani Zubairune ko Faisal sun hanani sukuni akanme zaki medani P.A ki mai amsa miki call”. Ido na cika da ƙwalla tace.
“Wayyo Allah Appiy Hannuna”. Cikin tsuke fuska yace.
“Bance karki ƙara kira Appiy ba”. da sauri tace.
"To Mudy”. Ɗan ƙara ta sake jin yadda yasa hannunsa ɗaya ya matsota jikinsa. Sai kuma ya ƙara matse hannun har Saida ta fara bubbuga sawunta a ƙasa cikin fushi yace.
“Sabida baki da imani kika yaye min yara ba tare da izinina ba, kika hanasu abinda Allah ya halatta musu, tun lokacin yayesu baiyiba kin cutar dasu Allah zai saka musu ni kuma zanyi mgnin abin sai duk bashin da kikaci na yayesu lokacin bai cika, zaki biya shi ne yarinya irin biyar da bazaki manceba kafin kuma in haɗa miki da Allah ya is”. Da sauri ta fara magna cikin rawan murya.
"Dan Allah karka jamin Allah ya isa”. Tayi mgnar tana tura lip ɗinta na ƙasa.
A hankali ya sake hannunta tare da ɗan ja da baya, hakan ya bata damar ficewa da sassarfa ta sauƙa ƙasa, parlour Abba ta shiga da sallama a bakinta, sai kuma ta tsaya gis a bakin ƙofar tare da zubawa Idaya ido cike da mmki, ita kuwa Idaya durƙushe take gaban Abba da Ummi da Goggo Dada, sai Sulaiman da Salim dake gefe, ido suka zuba mata ganin ta tsaya a wurin. Abba yace
“Shigo ciki Fariyda zo nan ki zauna ya nuna mata gefen Ummi. Cikin mmki ta iso gefen Ummi ta zauna idonta duk na kan idayatu wani irin ƙasƙantaccen kallo mai bayyana ƙyama take mata ita da yar yarinyar dake gefenta wacce bazata gaza 9 years ba.
“Ina Mahmoud din”. Abba ya tambaye ta.
Kai ta ɗan sunkuyar cikin girmamawa tace.
“Yana zuw”. Sallamarsa ce ta hanata ƙarasa abinda zatace.
Yana gyara riƙon system nashi ya shigo Parlour da tuni ƙamshin turarensa ya cika ko ina.
Da sauri ya tsaya ya rumtse idanunsa da ƙarfi lokacin da ya sauke idonsa kan Idayatu da wata yar budurwar yarinyar da bazata gaza.
“Innalillahi wa inna'ilaihi raji'un, azoobikalmatil”. Sai kuma ya juya da nufin fita yana mai ƙara addu'ar neman tsari da sharrin shaidan da shaiɗanu.
“Zo nan Mahmoud kar ks kuskura ka fita, shigo ka zauna”. Jin yadda Abba yayi magna cikin bada umani da shakeƙƙiyar muryar dake nuna tsananin tashin hankali da ɓacin rai gami fushine ya sashi juyowa a hankali ya zauna cike da fargaba
Inda Abba ya nuna masa ya zauna a gefensa ya zama suna fuskantar juna da Fariyda, idonsa ya meda ya rumtse yana mai tuno rayuwarda yayi a baya wacce baya fatan tunata, amman gashi yau da alamun mugun labari zai riskeshi.
shigowar Amina da sallamarta ne yasa su ɗan kallonta sai kuma suka meda kai suka sunkuyar.
Tamkar ido zai faɗo haka Amina ke kallon Idaya da yarta, kaɗuwa da tsoron da ya rufe tane ya hanata magna sai zama da tayi a gefen Goggo Dada tana meda idonta kan Mahmoud da yayi ƙasa da kansa har lau idonsa a rumtse, sai ta kuma kalli Fariyda dake yiwa Mahmoud ɗin kallon dubunsa zai cika kenan.
Gyaran muryan da Abba yayi ne yasa duk suka gyara zama da meda hankali kansa, illa Mahmoud da ya ƙara yin ƙasa da kanshi tamkar zai shige cikin ƙasa yayinda hawaye ke ratsa fatar idonsa da ya rumtse suna zubowa har kan system nashi dake kan cinyarsa, cikin Muryar da ta firgita musu zukata Abba yacewa Idaya.
"Gashi nan yazo gani mahaifinsa ga mahaifiyarsa ga matarsa ga sauran yan uwansa, kiyi ki faɗi abinda ya kawoki ki bar min gidana”.
Cikin sheshheƙan kuka mai fizge numfashi Mahmoud yace.
"Abba ka yafe min, dan Allah kada kayi fushi dani wlh nayi nadama kuma na tsarkake rayuwata”. Da sauri ya meda kansa ƙasa ganin Abba ya ɗaga masa hannu tare da watsa mishi kallon da ya raunata masa zuciya.
Ita kuwa Idaya gaban Abadan ta ƙara matsowa ta durƙusa kan guiwowinta da kyau tana kallon Mahmoud ta fara magna cikin rawan murya dake cike da nadama da danasani.
"Abba nazone in nemi gafarar Mahmoud da yafiyarsa a kan cutar da shi da rayuwarsa da nayi a baya, na nemi inzo gidane a gabanku dan kuma in nemi yafiyar cutar da zuƙatanku da nayi akan lalata muku rayuwar ɗanku Mahmoud da kuma neman alfarma ku tayani bashi haƙuri ya yafe min don girman Allah da Manzonsa Mahmoud ka yafe min Abba Ummi ku yafe min ku tayani bashi haƙuri akan cutar da nayi masa”. Tunda ta fara mgnar jikinta da muryarta ke rawa, hawaye na kwaranya a idonta.
Abba kuwa dasu Ummi kab ba wanda ya iya ce mata komai duk idonsu na kan yarinyar nan dake gefenta zuƙatansu cike da tsoron kaddai jinin Mahmoud ce yarinyar.
Salim ne da yasan komai ya kalli Mahmoud da yake ta jujjuya kai murya a cushe yake faɗin.
“Ko zan yafewa kowa a duniya banda ke a ciki, saboda kin min cutar da babu wanda yamin ita a duniya, wlh har yan boko haram da suka sa bom a matsalaci ya tashi damu yayi sanadin rasa lafiyar wani sashi na jikina, na zan iya yafe musu amman ke dai kam sai munyi shariya a gaban Allah, sai ki wankeni a gaban Allah na tsarkaka akan aikata zunubi da najasa da kika sani”. Da sauri ta juyo kanshi cikin tashin hankali mara misaltuwa tace.
"Na sani Mahmoud na cutar da kai kuma ban cancanci yafiyarka ba, akan yadda na tirsasa maka yin alfasha dani da yadda nabi bokaye suka juya maka kai ka fara rayuwar alfasha dani har ta kai ga ƙawayene na saka yin abinda ko yaushe in ka yishi sai kayi ta kuka kana buga kanka a jikin gini, amman dan Allah da Manzonsa ka yafe min ko dan rayuwar Iyabu ta daidaita”. Cikin tsuke fuska da hautsinenniyar murya Abba yace.
"Ke ki gaya min me kikayiwa ɗana”. Zama tayi dirsham cikin kuka take kallon yadda duk suka zuba mata ido tamkar zasu rufeta da duka, sai Fariyda da hankalinta ke kan Mahmoud da yake sheshheƙan kuka mai cushe numfashi cikin rawan murya ta fara basu Labarin.
“Tun ranar da na fara ganin Mahmoud ranar da muka fara zuwa BUK Allah ya jarbceni da sonsa da muradin kasancewa dashi wanda tsananin kyansa da haibarsa tasa duk yan matan department ɗin mu arnan da gura gura gurbin musulmai irina suke ribibi a kanshi harma da wasu musulman kirki da suke masa so na aure, saɓanin irin sonda ni da Sara da wata Barira muke masa irin na alfasha, shi kuwa Mahmoud ko magna baya yi mana, in Banda abokansa maza Fadil sai Sulaiman da Salim da Kabir kuma dama duk kullum tare suke zuwa.
Haka nayi ta bibiyar Mahmoud Amman ko magna bai taɓa yimata ba har suka tafi shera ta biyu. Duk department nasu ba wanda bai san naci da son da take mishi ba, zuwa lokacin kuma duk wata cikar haiba ingarman na miji ta gama bayyana a kan Mahmoud ilimi da Allah ya bashi na saurin fahimta ya ƙara jawo hankalin yan mata kanshi. Idaya Sara da Barira kuwa kullum hankalinsu na kanshi rashin samun fuska a wurinsa yasasu fara nazarin neman mafita. Idaya itace ta fara samo mafita a karan kanta dan burinta ace yau gata gashi haka yasa kafin su gama shekarsu ta biyu, ta fara bin malamai kowa sai ya tabbatar mata akwai rabo a tsakaninta da Mahmoud kawai lokaci ne a haka taje can Lagos wurin dangin Babanta, A hotu ɗan bappanta yaga Mahmoud daga nan duk ta bashi lbrin yadda yake da mislilanci da ƙin kula mata, cikin yaƙini yace mata zai haɗa mata magani da zaija hankalinsa ta yadda har abada bazai rabu da itaba, amman tayi alƙawarin zata bashi kanta, da fari ta yarda sai kuma daga baya tace yayi haƙuri sai Mahmoud ya kasance da ita in taga burinta ya cika zata dawo Lagos ta cika mishi alƙawarin harda ihsanin kuɗi dan tasan in dai Mahmoud ya shigo hannun kuɗi ba matsalarta bane, jin haka ne yasa ɗan bappanta yarda, ba ɓata lokaci ya fara haɗa mata magunguna tana wanka hayaki da sha da surkullen tsafin kiran sunan Mahmoud a duk sanda zatayi hayakin a ƙalla kwana tara suna aiki, a kwana na goma akayi sanarwar an janye yajin haiki haka yasa ta shirya ta dawo. Koda ta dawo washe gari ta fara zuwa makarantar a ranar Mahmoud bai zoba sai Salim da Sulaiman da ta ɗan fara sabawa dasu.
Sai washe gari Mahmoud yazo a ranar su Salim sunyi mmki dan suna fitowa lectures Idaya dake biye dasu tacewa Mahmoud Papi sunan da duk makarantar ake kiransa dashi kenan dan jin sunan a bakin su Salim haka yasa ba'a wani sanshi da Mahmoud ɗin sosai ba.
“Papi ba mgna ne”. Ga mmkin su Salim sai ji sukayi yana ce mata.
“Me zan ce miki?”. Yayi magnar ne da yanayin da kaganshi ba cikin nitsuwarsa yakeba, ita kuwa Idaya cikin Farincin ganin alamun cikar burinta dan bai taɓa mata mgna ba sai yau haka yasa cikin yauƙi tace.
So nake ka cemin me nake so. Cikin jujjuya kansa da yake ji ba daɗi ya tambaye ta me takeso. Da sauri tace masa. Kai nakeso. Sosai Sulaiman ya karaya da lamarin lokacin da yaji Mahmoud na ce mata.
Kin sameni ai, nemi wani abun kawai. Tana kallon su Sara dake mmki ta ce masa. To yau ka maidani gida nan zan san na sameka. Da sauri Sulaiman ya riƙo hannunsa ynqa faɗin kai nifa na gaji mu tafi, ko inda sulaiman yake bai kallaba sai motarsa ya buɗe mata yana mata nunin ta shiga, haka yasa Sulaiman shiga motar Salim yana faɗin, Mahmoud ya bita fa, Salim yace. To ai dolenshi sufa mata dolene kawai ka bisu dan suke da mulkin zuciyar maza wata ƙil ya fara sonta ne kaga nacinta ai ya mata aiki.
Shi kuwa Mahmoud koda suka je gidansu Idaya iyayenta basu dawoba dan suna can kasuwa shagon robobinsu ko ƙannenta ma da sun tashi makaranta kasuwar suke wucewa sai gab magrib suke dawowa.
Haka yasa suna isa tace ya shigo, ba musu ya bita, suna shiga parlour mamanta wakai ta juya ta rungumoshi........