← Book details Sakar Makafi Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 13 OF 95

Sashe 13

Sakar Makafi Part 2 Complete Hausa Novel · about 3 min read

Assalamu alaikum jama'a ta jama'ar arziƙi fatan muna lfy ya gida da yaranmu.
Matan alkhairi mata masu duniya, akwai garaɓasa fa ta musamman da na watannan na maulud promo haɗine na musamman kashi da ban da ban, akwai naku na manyan mata, da kuma amare bazaaawara ko budurwa, da masu joge ɗanyen jego ko barden jego.
08069423567 gata inda zaku yi min magna ta WhatsApp,
Set ɗin kayana mataki biyu ne.
Na forƙo daga 40k ne zuwa ƙasa shine ƙananan 40k 35k 30k 25k 20k 15k 10k Akwai Maganin Infection sadidan yar uwa ba haufi, shi kuma set 10k.
Sai kuma manyan set ɗin hajia taho kiji daga 50k 60k 70k 80k 90k 100k 120k 130k 140k sa sha kundum uban makiya 150k ne yar uwa.
Haɗine na musamman.
Kana akwai kayayyakin turaren wuta dasu Humra da kulacca suma haka farashinsu yake.

Idan kin sayi kaya in dai set ɗin kayanki yakai daga 50k 60k 70k 80k zan biya miki rabin kuɗin Delivery, daga 90k 100k 120k 130k 140k 150k to free delivery ne, Ni zan biya Miki.

0005388578 Jaiz bank Aisha Aliyu Garkuwa.

By
*GARKUWAR MARUBUTA**SAƘAR MAKAFI*
Page 50
Na
*Aysha Aliyu Garkuwa*

kallo mai cike da tsoro da tsayuwar ƙwaƙwalwa ta fara yiwa fuskarsa tare da fara jijjiga hannunsa murya cike da mafi ƙololiwar tashin hankali, gami da tsinkewar zuciyar da ya sakar mata rawan jiki da murya take faɗin.
“Appiy! Appiy!! Appiy!!! kana jina ka buɗe idonka”. Yadda take kiransa da yadda jikinta ke tsumane yasa Nurses ɗin nan yin saurin riƙeta tare da ajiye ta kam kujerar dake gab jikin gadon cikin sauri tace.
“Ki nitsu ba abinda ya sameshi fa, bacci yayi ba mutuwa yayi ba, zauna kinga yana numfashi kalli zuciyarsa na bugawa yadda akeso”. Ta ƙare maganar da nuna mata na'urar da ke nuna bugun zuciyarsa da numfashi.
Da sauri Yah Saleh da kiran Abba ya kuma shigo wayarsa ya matso tare da amsa kiran yana kuma kallon Fariyda da ta saki sheshheƙan kuka raunataccen sauti da tsuma zuciyar duk mai sauraro a hankali yace.
“Fariyda yi shiru ba komai fa, kinga bacci yakeyi”. Harara mai cike da tsana kishi da tafasar zuciya Amira take auna mata tamkar idonta zasu faɗo ƙasa. Aunty Maryam kuwa cikin taɓe baki tace.
"Kawai dai ta fita daga ɗakin kada ta hanashi bacci, ina take har ya shiga wannan yanayin”.
Abba ne dake jin duk abinda suke faɗa da kuma sautin sheshheƙan Fariyda ya cewa Yah Saleh.
“Bawa Fariyda waya”.
Cikin shashsheƙan ta amsa kiran da Abba yayi mata. Abba ya ɗaura da cewa. “Kiyi shiru ko Fariyda ki daina kuka kiyi masa addu'a yanzu ina yake?”. Murya cike da rauni sanyi tace. “Abba cemin yayi zai mutufa, kuma gashi ya daina magna baya ko motsi fa yanzu ya rufe idonsa”. Cikin tausasawa Abba da Yah Saleh ya masa bayanin allurar amai da akayi masane yasa ya sake numfashinsa da bugun zuciyarsa duk lfy lau ne yasa yace.
“Ba komai Fariyda in sha Allah zai samu lfy, kiyi ta masa addu'a ki kwantar da hankalinki ina ƴaƴan naku”. Tana lumshe idonta tace. “Suna waje wurin Sajida, yana son ganinsu kuma yanzu idonsa na rufe Abba bai gansu bafa kuma yayi shiru”. Ummi dake jin duk mgnar tasu ne ta kalli Goggo Dada dake cewa.
“Ayyah yarinta ita Fariyda dama ko su Zaid ke kuka itama kuka take”. Kai Ummi ta kwantar jikin kujera tace.
“Ni na zaƙu su dawo”. Abba daya gama wayar ne ya ɗanyi shiru na kusan 3 to 4 minutes sai kuma ya sauke numfashi mai nauyi yace.
“Allah ka dubemu da idon rahama ka bashi lfy, in sha Allah zamu tafi Istanbul jibi”.
Chapter 13 · 0% Book details