← Book details Sakar Makafi Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 82 OF 95

Sashe 82

Sakar Makafi Part 2 Complete Hausa Novel · about 5 min read

tasa Sulaiman ne tafiyar. Ƙarfe sha biyu da rabi suka isa cikin babban birnin Gombawa ɗiban fari ba'a kwana dasuba a tashi dasu Gombe doma. A tare suka sauke numfashi mai cike da salama da nishaɗi lokacin da suka shigo cikin City Star Restaurant din Gombe. Abubuwan da akayi ta dire musu suka zubawa ido ganin sai ƙaro wasu akeyi ne yasa Aunty Saddiqa saurin dakatar dasu. Shi kuwa Mahmoud da bai buɗewa Fariyda front seat ɗin ba ya hanata fita, har Saida su Raihana suka iso wanda dama motarsu ke manne da nasu bamba to bamba, bayan duk sun shigane, ya buɗe mata yana, hannunsa ya miƙo mata dan ɗan tudun motar kauda kanta tayi ta sauƙo tana tura baki, hannunta ya kamo baya ya dawo ya buɗe but din motar, basket ɗin da Aunty Amina ta haɗa mashi tun ƙarfe huɗu na asuba da ya fito masallaci yaje ya amsa ne ya ɗauka. Cike da mmkin lamarin ƙyanƙyamin shi ta bishi a baya dan hannunta da yake je. VIP side ɗinsu na matakin ƙarshen suka shiga, ajiye basket ɗin yayi, yana sauƙe numfashi yace. "Farriyyha yunwa”. Dai-dai lokacin Sulaiman ya shigo, ɗan miƙewa yayi yana kallon Sulaiman ɗin, da sauri Sulaiman ɗin ya ƙaraso inda yake side hug suka yiwa juna cikin so da shaƙuwar jini, kafaɗar Sulaiman ɗin ya ɗan buga sai kuma ya miƙa masa car key ɗin nasa yana faɗin. "Kazo da shiri ai ko, ga key ka kwashi box uku ka bar ɗaya Pink collar ɗin na, sauran ka maidasu motarka”. Murmurshi mai cike da jinjinawa ƙarfin halin Mahmoud Sulaiman yayi yana kallon Fariyda yace. "Kinga mijinki zai maidani driver ko, ni ban san da tafiya ba, ban shirya mata ba, ga aikin yamin yawa a office ya kuma ce dole in zo in ɗauki su Aunty Saddiqa a motata mu tafi Gembu membila”. Cikin mmki take kallon shi, cike da alamun tambaya gashi taji yace a bar mata box ɗin a motarsa. Ɗan buge ƙeyar Sulaiman yayi yace. "Kaje ka shiryasu, kazo ga lunch Mom Hafiz tayi mana”. Murmurshi yayi ya juya ya fita. Ita kuwa Fariyda ɗan gyara zama tayi tana kallon shi dan murar da tayi mata kamun gaske yasa muryarta disashewa. gashi sai atishewa taketa fesawa. Basket ɗin ya tura mata gabanta yana kallon yadda ta turo leɓen ƙasa, murya a disashe tace. "Nifa tare dasu zan tafi”. Fuska ya tsuke cikin bada umarni yace. "Ki samin abinci”. Plate ta zaro ta fara zuba mishi abincin. Jawo plate da bowl ɗin yayi gabansa ya fara ci, ido ta zuba mishi tana kallonsa kamar ta samu madubi. "Akwai abinda na sace mikine kike nemansa a jikina”. Ya tambaya ba tare da ya ɗaga kaiba, baki ta tura a hankali sai kuma tayi saurin kauda kanta dan atishawar data zomata. “Kiyi ta kallon mutum ba tausaywa kina tura wannan ɗan lip ɗin dan neman tsokana, in ance miki mayya ki fasarrashi ta wani wurin da ban ki kama kuka, bayan duk kin lashe zuciyar mutum.” Ido na cikowa da kwalla tace. "Ni dai ba mayya nace, kuma ni ban kalleka ba, mema zan kalla a jikinka”. Ɗan ɗago kanshi yayi yana kallonta sai kuma ya jawo hannunta ya ɗaura kan mararsa a hankali yace. "Shi zaki kalla mana kinyi missing nashi”. Da sauri ta fizge hannunta haɗe da kefe kanta kan table murya a ɗan disashe tace. "Bana so”. basket ɗin ya tura mata cikin kwaikwayar muryarta yace. "NI ina so, kuma dole sai an bani in anƙi inyi Allah ya isa kuma an san dai Allah ne yache a bani ko a shiga wuta”. Kuka ta fara cikin sanyi tana ɗan bubbuga sawunta kaɗan. A hankali ya ɗaura hannunsa kan fuskarta yana shafawa cikin tattausan lafazi yace. "Yi shiru in sha Allah wuta bata da rabo a jikinki, kici abinci, daga nan mu da tsayuwa sai a Taraba wata ƙil kuma zamu kai 6 to 7:00 pm kafin mu isa”. Tana longwaɓar da kai tace. “Bazan iya ciba, mura ya riƙe min wuya”. Wayarsa ya ɗan zaro yayi rubutu kaɗan ya maida ta ajihu, jim kaɗan aka kawo mata zazzafan ferfesun kaza da yaji yaji da citta, kanamfari sai kamshi yake bazawa. "Tura mata kusa da ita yayi, yana amsa kiran Yah Nasir daya shigo. “Alhamdulillah Yah Nasir muna cikin Gombe, in munyi salla zamu wuce”. Sai kuma ya ɗan yi shiru yana kallonta yace. "Muryarta bata fita mura ya kama mata wuya, wanne maganin ya kamata a saya mata?”. Kai ya jinjina haɗi da cewa. "Ok to ba matsala Yah Nasir sai anjima”. Daga nan sukayi sallama, duk yadda ta kai ga son cin abinci abin yaci tura. Shigowar Sulaiman ne ya miƙa mishi basket ɗin ɗaya side ɗin in da Raihana da angonta suke ya shiga. Bayan sun gama komai, sunyi salla. Suka fito a tare, Aunty Saddiqa dake waya da Adda Nana tace. "Tab ai mu a wani Restaurant din muka tsaya amman muma yanzu mun fito. Suka ƙare maganar suna shiga motar Mahmoud ɗin. Itama Fariyda da sauri ta shiga a ranta take cewa. "Bari mu ga dai iya tsaurin idonshi ko zai zo ya koresu a motar san ne sarkin marowatan mota”. Salma dake bakin ƙofar ya kalla a fakaice sai kuma ya ɗan juya yana kallon Sulaiman da yake ta kallon Humaira da zata shiga motar amarya murya a dake yace. "Mrs Salim ga motar Sulaiman zai rakamu nan kamar kun matsu”. Da sauri Aunty Saddiqa ta buɗe side ɗin da take tana faɗin. "Nima zan koma can”. Aunty Rashida ma ajiye Zaitoon tayi kusa da Zaid da Aunty Saddiqa ta kwantar tace. "Eh gskya bari muje can”. Suka nufi motar Sulaiman ɗin suna dauƙe ajiyan zuciya ko ba komai zasu sake. Da sauri Fariyda tace. "To ke Salma shiga nan ɗin”. Kai ya jujjuya ido a tsaye yace. "A'a taje can”. Dariya Salim dake jin duk abinda suke cewa yayi yace. "Babe je motar Sulaiman dan wannan yau babu sarki sai Allah ko ta ina bazai ɗaga ƙafa ba ku barshi da matarsa”. Murmurshi tayi ga juya....
Chapter 82 · 0% Book details