Sashe 91
Sakar Makafi Part 2 Complete Hausa Novel · about 3 min read
By
*GARKUWAR MARUBUTA**SAƘAR MAKAFI*
Page 84
Na
*Aysha Aliyu Garkuwa*
Mutanen Arewapen ayi following na a latsa min like
https://arewapen.com/u/garkuwa
"Wai me sukewa dariya ne? Me yasa Mujahidin ɗin ya fita ko gaisawa bamuyiba”.
Sadiq da dariya ke son kwabce masa ya miƙe yana danne dariya ya fita dan tsoron kar Mahmoud yayiwa Mujahid wani abu da ya faɗo masa a rai.
Farooq kuwa ƙanwarsa Salma dake bawa Arɗo Habu labarin yake harara yana faɗin.
"Ku dai in kun san abun mutum ya shiga uku more Especially ke da Aunty Rashida”.
Hajja inna kuwa kwaffa tayi tace.
"Ni kam ba basa son juna ba”. Aunty Saddiqa tace.
"Na rabaki da faɗin haka Hajja inna ai su irin nasu salon soyayyar kenan”.
Acan waje kuwa da sassarfa mai haɗe da gudu Sulaiman ya isa inda ya hagon Mujahid na zaune cikin motarsa, Mahmoud kuwa na tsaye riƙe da marfin motar wani irin matsiyacin kallon tsana yake auna masa murya a harzuƙe cikin isa yace.
"Kai kace mayen matane kai ko? Matan ma matatace abun harin ka ko?”. Cike da tsoro Mujahid ke jujjuya kai kamar irin wanda ubansa ke masa faɗa, shi kuwa Mahmoud harara ya auna masa yana gyara riƙonsu Zaid haɗi da faɗin.
"No kamaci gaba da harinta, wlh tallahi sai na ɓalla duk wani ƙashi na jikinka, in zubda maka haƙora duka idon da suke kalle min mata sai na tsiyayesu ko a shari'a bani da laifi in Kuma kanaga bazan aikataba ci gaba da kallon ta”. Murya cike da karaya yace.
"Kayi haƙuri ni wlh ban san baka saketaba”. A daƙile yace. "Dama can uban waye ne yace ma zan saketa ko na saketa, kai an gaya ma ko mutuwa nayi kurwata zata barka ka aurarmin matata ne, ai wlh tun ranar da akace an ɗaura mata aure dani ta harta maka kenan har gaban abadan”. Yana ƙara matsawa can cikin motar yace.
"Ni wlh ban sani bane kuma bani ba ita wlh ko gidanku bazan ƙara zuwaba ko magna zan daina yi mata”. Da ƙarfi ya rufe marfin motar gib haɗi da cewa. "Da kace kai shegene kaine mai hancin jin ƙamshin turaren matata da yake kai ɗan iskane a gabana wai zaka kama mayafinta zaka sunsuna ai wlh ka sake gigin matsowa kusa da ita ko zama inda take wlh zan kasheka banza”.
Isowar Sulaiman ne yasa Mujahid sauke numfashi mai nauyi.
Hannu Sulaiman yasa ya kamo nashi yana faɗin.
"Please dan Allah kayi haƙuri karkace komai”. Harara ya auna masa ya miƙa masa su Zaitoon haɗi da buɗe motarsa dake gefe ya shiga.
Dai-dai lokacin ta iso wurin ido ta rinƙa jujjuyawa sai kuma ta juyo a sukane jin yadda ya ja dogon tsaki tare da buɗe front seat fuska ba wasa yace.
"Shigo mu tafi”. Sai kuma ya kalli inda Mujahid yake kwaffa yayi ganin ko kanshi bai ɗagoba, jin yadda ya mata magna cikin kaushin muryane yasa ta matso kusa da motar tana faɗin.
"Yau nefa dinner kuma in anyi sallan azahar ne zamu tafi can taraba, muje mu ga gidanta nacan mu shirya da dare za'ayi dinner ɗin kuma kace mu tafi”. Fuska ba wasa murya faɗace yace.
"Zaki shigo mu tafi ko sai na fito na soke pala palan kunnunwansa da ya baza yana jin muryarki”. A hankali ta shiga motar dai-dai lokacin kuma Sadiq ya iso, da hannu yayiwa Sadiq alamun yazo.
Cikin girmamawa ya iso kusa dashi yana faɗin.
"Gani Yah Mahmoud”.
Yana kallon ta inda Mujahid yake yacewa Sadiq.
"Ka amshi su Zaid ka kaiwa Mrs Salim su, kuma in kunzo Taraba kai zaka koma da motar Sulaiman, shi kuma zai tafi da tawa”. Ido Sulaiman ya zuba mishi yana faɗin.
"To kai da me zaka koma”. Ko ƙalla bai ce maiba yayiwa motar key ya bar farfajiyar gidan.