← Book details Sakar Makafi Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 41 OF 95

Sashe 41

Sakar Makafi Part 2 Complete Hausa Novel · about 6 min read

dai lip ɗinshi na ƙasa da har yanzu yake datse dashi. Cikin jin sanyin na ratsata ta shiga bathroom wanka tayi tare da goge bakinta tayi al'walan kwanci bacci, A hankali ta fito tana ɗan leƙo fuskarsa, bacci yake sui haka yasa ta fara kimtsawa a hankali a hankali tanayi tana waiwayenshi, kullacar sirri ta shafa ta kimtsawa cikin tattausan riga da wando iya guiwa na bacci Black collor irin baƙi mai sheƙin nan daga ɗan saman rigar net ne har zuwa jikin hannun rigar da yake iya guiwar hannu, wondon ma daga ƙasa kusa da guiwarta net ɗin ne, hula tasa ta naɗe dogon gashinta ta tura a ciki bayan ta fesa turaren gashin sosai tayi wani irin mashahurin kyau ta fito kamar yar tsanar zinari bakin kayan bacci ya ƙara fidda asalin farar fatarta da ba algus sai glowing takeyi kamar star ƙirjinta cike cur da ɗan ɗakalellen cikinta ya taimakawa bayyanan kafaffun ƙirjinta sai mazaune da ƙugu da ya fita tamkar kalangu yan jajayen lips ɗin sai sheƙi sukeyi. A hankali ta juyo ta kalleshi a karo na uku, har lau bacci yake baya ko motsi illa motsin numfashi. Juyawa tayi ta buɗe Wordrobe ɗinta, shiru tayi tana kallon inda su Amina suka mayar mata dasu Beshid duvet blanket duk sun meadasu can sama, ɗan ɗigirgire tayi wai ko tsawonta zai kai ta samu ta jawo duvet ko blanket Amman ina ko na ƙasa da stap ɗin da suke ciki hannunta bai kai ciki sosai ba, juyowa tayi tana fuskantarsa bayan ta maida marfin Wordrobe ɗin ta rufe. Dardumar sallanta ta shimfiɗa kan Turkesh carpert dake gaban gadon, sai kuma ta ɗauko babban hijabin sallanta ta ƙara yaryaɗa mai turaren Hayatii da Oud Ma'aroop, ta zurashi jikinta da sauri dan sanyin dake busota na ac da aka ƙure masa, pillow ta jawo ta wurga kan dardumar ta kwanta bayan tayi addu'a ta shafa. Ƙarfe biyu dai-dai ya tashi zaune, yana mai lumshe idanunsa saboda hasken da ta bari a kunne sai kuma ya buɗe idon cike da mmkin ganin inda yake, ido ya zuba mata ta wani duƙunƙune jikinta ta haɗe wuri ɗaya har guiwowinta na taɓa ƙirjinta, ta tura ɗan lip ɗinta na ƙasa na sama kuma ta kamashi ta ciki tana tsotsa a hankali, na ƙasan sai sheƙi yake yi da ɗaukar ido yayi irin jannan mai jan hankali saboda ɗan tattarewa da yayi alamun sanyin yayi mata yawa. A hankali yake jujjuya kanshi yana kallon ɗakin tunowa da kukan Zaitoon ne ya kawoshi ya sashi ɗan waige-waige ganin babu Zaitoon ɗin ne yasa ya miƙe a hankali yana shaƙan ni'imtaccen ƙamshin sai kuma ya rufe idansa dan sarawa da kan nasa yayi wanda hakan ya tuna mishi lokacin da ta shigo da fita da tayi da gudu da shigowarsu Ummi bathroom ya shiga bayan kamar 6 minute ya fito da alamun yayi alwalar kwanciya da baiyiba gashi nafila yakeso yayi kuma sarawan kan yafi tsananta in yana tsaye, kanta ya sunkuya tare da ɗagata ciɗak da sauri ta maƙale wuyansa haɗe da manna kanta a ƙirjinsa, kwantar da ita yayi ɗaya gefen ya jawo duvet ɗin ya rufe ta yana kallon yadda take shan lip ɗinta sai kuma ya kalli na ƙasan. Baki ya taɓe ya komai ya kwanta ɗaya gefe. Ƙarfe biyar dai-dai ta farka, cikin mmki take kallon inda ta kwanta da kuma inda ta farka sai kuma ta kalli inda yake kwance baya nan, motsin ruwa da taji a bathroom ne ya tabbar mata shine. Da sauri tayi ƙasa da kanta lokacin da ya fito da alamun wanka yayi dan taji ƙamshin showergel ɗinta, a ɗan fakaice ya kalleta ganin yadda take kallon inda ta kwanta da kuma inda ta tashi ta samu kanta towel ɗinta dake hannunsa yana goge sumar kansa ta kalla sai kuma ta sauƙa kan gadon ta raɓa gefe ta shiga bathroom. Wanka tayi da brush kana tayi alwan ta maida kayan jikin nata. Kan gadon ta hangoshi kwance ya rufe jikinsa duka har kanshi saboda zazzaɓi da ya rufe shi ko Azkarul Sabah bai samu yayiba da ya idar da salla ya hau gado ya kwanta yana azkar ɗin, kunne ta ɗan ƙasa saboda jin kamar yana sambatune, sai kuma ta buɗe Wordrobe ɗinta tattausar Turkish Abaya ta zura kan kayan bacci tare da yin Rollin kanta da mayafin. Bayan ta idar da salla tayi azkar ne ta miƙe a hankali dan jin har yanzu yana sambatun da rawan sanyi a hankali ta ƙara matsowa ta inda yake sosai, cikin sanyi tace. “Appiy zazzaɓi ko”. Ba tare da ya buɗe kansaba ya gyaɗa mata kai alamar eh, hannu tasa ta ɗan ja duvet ɗin ta fidda fuskarsa a hankali ta kuma cewa. "Wanka kayi da ruwan sanyi ko”. Yana ɗan buɗe idonsa yace. “Uhmmm”. Tana kallon yadda ya takure tace. "In kashe Ac ne?”. Fuska ya kwaɓe tamkar zaiyi mata kuka a ɗan faɗace yace. "Ban saki ba”. Baki ta taɓe a ranta tace. “To Ayagi sarkin faɗa naji ai dama ance in baka da lfy kafi bala'i da iya baƙar mgna, a fili kuma tace. "In kawo ma tea”. Bai kulata ba kuma bai rufe idonshi ba bai kuma juya kanshi ba sai fuskarta da ya tsare da kallo more Especially lips ɗinta dake sheƙi, ganin yadda yake kallonta ne haka yasa ta juya ta fita parlour a kan Centre table ɗin su na parlour ta samu Tray ɗauke da kayan tea da cups biyu da flacks da bread mai taushi bisa dukkan alamu Goggo Dada ne ta kowo musu ɗaukowa tayi. A kan bedside drawer ta ajiye tare da zama bakin gadon cikin ƙosawa da sanyin tace. “Appiy in haɗama tea kasha kafin kasha mganinka sai ka maida baccin”. Da sauri ya jujjuya mata kai alamun a'a bazai shaba, sai kuma ya lumshe idanunsa, bayan kamar 4 minutes ya buɗesu saboda jin shiru, har yanzu tana zaune ta jingina bayanta da kan gadon idonta da suka lumshe alamun bacci takeji ya ɗan kalla cikin baccin da ya fara ɗibarsan yace. “Kwanta kiyi bacci”. Kai ta jujjuya mishi tare da gyara zamanta tana kallonsa, shi kuwa baki ya taɓe ya maida ido ya lumshe jin shiru bata tashiba bata kwanta bane ya kuma buɗe ido tana zaune a wurin tana lumshe da ido 47 seconds to one minute ta kuma buɗesu, da hannunsa yayi mata alamun ta matso kusa ta kwanta, kai ta jujjuya alamun a'a, ɗan tsaki yaja ya rufe kansa da duvet. Bayan 16 minute ya buɗe kai yana kallonta tuni tayi bacci a zaune mayafin Abayar ya zame yayi ƙasa gashinta ya zubo kan kafaɗarta, kwaffa yayi yana mai lumshe manyan idanunsa haɗe da shaƙar ni'imtaccen ƙamshin jikinta yasa hannunsa ya jawota jikinsa da hannunsa ɗaya, ɗaya hannun kuma ya miƙar dashi yayi mata pillow ya ɗaura kanta a kan damtsen hannunsa numfashi mai nauyi ya fesar haɗi da sa ƙafarsa ya...........
Chapter 41 · 0% Book details