← Book details Sakar Makafi Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 90 OF 95

Sashe 90

Sakar Makafi Part 2 Complete Hausa Novel · about 3 min read

kanta da kafadarsa, kusan a tare da Khadija Aunty Rashida sukace. "Appaiyn Zaid kun rigamu isowa kenan ina kwana”. ba tare da ya kallesu ba yace. "Our Auntys ina kwana”. Ya faɗi yana lumshe idanunsa jin Zaid ya rungumeshi ta baya. Adda Nana Aunty Saddiqa da Sadiya ne suka amsa suna cire idonsu daga kanshi ganin yadda yake ƙara sa Fariyda mug ɗin a bakinta. Ita kuwa Fariyda cike da kunya take ɗan matsawa daga jikinsa haɗi da jawo Zaitoon ta rungumeta tana mai sauƙe numfashi ta ajiyeta a tsakaninsu. dai dai lokacin kuma Su Farooq suka shiga Sulaiman dake bayan Mujahid da ya ja ya tsaya haɗe da yin ƙasa da kanshi cikin tsoron hango Mahmoud da ya kasa dannewa yace. "Innalillahi”. Gefensa Sulaiman ya raɓa yabi bayan Farooq da Sadiq Humaira na biye dashi a baya Zainab na gefen Farooq ɗin. Zama sukayi gaba Arɗo Habu, bayan sun gaisane Sulaiman da har lau idonsa na kan Mahmoud ne hannu ya bashi yana faɗin. “Ina ka maƙalene”. Yana amsar Zaitoon daga hannun Fariyda yace. "Sama na maƙale”. yayi mgnar da murya can ƙasa yadda Sulaiman ɗin ne kaɗai zai iya ji. Hannu ya ɗan miƙawa Ardo Habu yana faɗin. "Mu zamu wuce”. Yana bashi hannu yace. "Zamu ɗan kwana biyu ai ko kaji kalar sanyin garinmu”. Fuska ba walwala yace. "In sha Allah zamu sake zuwa na musamman zamuyi gida anan dan ku”. Ya ƙare maganar yana dire masa rafan kuɗi yan dube-dube guda biyar, sai kuma ya ajiye biyu gaban Hajji Inna ya miƙe Zaid da Zaitoon na maƙale da wuyansa. Miƙewar da yayi da juyowan da yayi haɗi da ido biyu da sukayi da Mujahid, da murɗawar da cikinsa yayi da bugun zuciyarsa duk a tare suka kasance, da sauri yayi ƙasa da kansa haka kawai yaji Mahmoud ya masifar bashi tsoro, idonsa har kamar wuta yake feso masa shi yasa yayi ƙasa da kai, shi kuwa Mahmoud tunda yaji an ambaci sunan Mujahid ɗin ƴar guntuwar fara'rsa ta ɓace ɓat. Ɗan juyowa yayi ya kalleta murya a daƙile yace. "Mu tafi”. Fuska a kwaɓe ta zuba mishi ido ta buɗe baki da nufin magna taga ya juya ya nufi hanyar fita yana faɗin. "Taso mu tafi”. Gefen Mujahid ɗin ya ɗan tsaya yana masa wani irin kallo haɗi da hucin numfashi mai zafi wanda sautinsa yasa Mujahid ɗin da tuni jikinsa yake rawa far-far a tsorace ya kare fuskarsa da hannunsa mai lafiyar ɗaya hannun da Mahmoud ya karya kuwa yayi saurin karkacewa jiki na rawa tsoro ya juya a saba'in ya fita. Kwaffa yayi haɗi da mara masa baya. Haka ne da Sulaiman ya gani yayi saurin miƙewa yabi bayan Mahmoud ɗin. Ita kuwa Fariyda dariyar dasu Aunty Rashida suka farayine ya ankarar da ita, cikin dariya harda riƙe ciki Khadijah tace. "Hege mai wuya kamar lagoni yaga maza wlh duk jikinsa rawa yakeyi”. Aunty ta dafe cikinta tana kallon Fariyda data haɗe fuska cikin dariya tace. “Da shegen ƙugu kamar na buzuzu ya wani ɗamare kamar gangan yana ganin Mahmoud fa ya kasa ƙarasowa wlh duk jikinsa tsuma yakeyi”. Adda Nana dake danne dariyarta tace. "Yo gskyarsa ai gwara ya gudu ko ya samu ya tsira da sauran haƙoransa”. Cikin dariya Aunty Saddiqa tace. "Yo zai bari kansa yayi murfune yasan karonsa dashi na farko yadda abun ya kaya masa haƙora biyu babu har yanzu sai wawulumon baki ga hannu a karye ina zai tsaya a ƙara masa wani karayan”. Aunty Sadiya tace. "Kai wlh ya bada maza da gudu ya fita fa”. Arɗo Habu ne ya kalli Salma dake cewa. “Hege yaga maza bisa kansa dole ya tsere, kuma fa Appiy ya bishi karfa yaje ya masa wani abun”. Jin haka ne yasa Fariyda miƙewa tayi wajen da ɗan sauri cike da tsoro kar yaje ya illatashi, Arɗo Habu kuma Farooq da Sadiq dake zaune gabansa ya zubawa ido haɗi da cewa....
Chapter 90 · 0% Book details