Sashe 31
Sakar Makafi Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Cikin zarra yake taku tare da kutsa kanshi cikin babban hall ɗin hotel ɗin inda suke da mitting na musamman wanda zasuyi na gamayyar manyan Yan kasuwar Arewa da kudu dan kyutata mu'amala a tsakanin ɓangarori biyun da samar da sauƙin farashi wa junanmu. Da sauri ya ƙarasa ciki tare da zama kan ɗaya daga cikin kujerun dake zagaye da babban table ɗin dake ɗauke da kujeru sama da 126, babu ƙaɓilar da babu a wurin akwai wakilci dukkan 33 State da kuma wakilcin dukkan kamfanin masu zaman kansu da manya-manyan yan kasuwa. Yana zama suka fara gabatar da manufar zaman nasu. A ƙalla 3 hours suna tattaunawa Alhamdulillah basu tashiba har saida suka tsaida matsaya ƙarfe she ɗaya dai-dai ya shigo ɗakin bayan ya amshi jallabiyarsa da ma'aikacin ya kawo ma lokacin da ya iso bakin ƙofar. A inda ya barta a nan ya sameta a durƙushe har yanzu ko ƙwaƙwaran motsi batayi ba, jallabiyar ya wurgar kan gado ya juyo yana kallon su Zaid da tuni sunyi bacci a kan kujerar 3 seatter ɗin numfashi mai sanyi ya tare kallonta ta gefen idonshi, hannunsa yasa ya jawo jallabiyarsa daya bari kan gadon turarukansa masu sanyin ƙamshi ya fesa tare da zura jallabiyar akan 3 quarter and shirt dake jikinsa Wayarsa ya zira aljihunsa yana mai rataye jakar system nashi a kafaɗarsa na hagu ya sunkuyo ya ɗaukesu duka biyu ya ɗaurasu a kafaɗa, ɗan jujjuyawa yayi ganin ba wani abu nasa daya mance, to dama da iya briefcase nasa kawai yake wanda ya kimtsa komashi a ciki kafin ya fito wanka kamar yadda itama komanta yake cikin hand bang ɗinta. Ƙofar ɗakin ya buɗe a hankali yana kallon agogon roles ɗin dake hannunsa yana gyara riƙonsu da tabs ɗinsu yace. “Ke mu tafi”. Ya faɗa yana kallonta da dukkan idonsa dan tabbatarwa tana motsi ko dai suma tayi dan ya lura bata da wuyan suma suman daɗi yake mata. A hankali take yunƙurowa tare da haɗe lips ɗinta ta matse tana mai dafa jikin wardrobe ɗin ta samu ta miƙe tsaye ba tare da ta kalli inda yake ba ko idonta nauyin ɗagosu takeji, handbag ɗinta ta ɗauka a hankali ta zura ƙafarta cikin takalmanta, duk abinda take yi idonsa na kanta har saida yaga ta nufo bakin ƙofar sannan ya juya kai ya buɗe ƙofar ya fita tana biye dashi a baya. Tunda ya shiga motar bai juyoba kamar yadda itama bata ɗago kantaba, ganin sun shiga Airport ne yasata lumshe idonta a hankali ta fara motsa bakinta tana jin garɗin Grapes daya zuba mata har yanzu bai bar bakinta ba. Ƙarfe sha biyu dai-dai jirginsu ya ɗaga Lagos to Kano. Bayan tashinsu da 36 minute ya ɗan juyo ya kalleta har yanzu kanta na sunkuye idonta dake ɗan kumbure alamun ta ɗanyi kuka ya kalla sai lips ɗinta da gogesu da tayi tayi kafin yayi mata aika-aikan yasasu yin jazir kamar an shafa mata jan jambaki. Numfashi ya sauƙe tare da kwaɓe fuska mai haɗe da murmushin gefen baki ya maida kanshi kan su Zaid da suka farka daga baccin. Suna sauƙa a Kano Ana ana kiraye-kirayen sallan azahar wasu masallatanma tuni sunyi salla. A hankali take biye dashi a baya, tamkar wacce bata da laka a jikinta. Suna fitowa Arrivals ta ɗago kanta a hankali jin anyi mata rungumar da tasa ɗan kuzarinta dawowa, Hafiza da Samira ne da Raihana sukayi mata rungumar da tasata dariyar Farin ciki Hafiz kuwa da sauri ya amshi Zaitoon Huzaifa kuwa Zaid ya karɓa sai kuma Sulaiman da yayiwa Mahmoud ɗin side hug tare da ɗan sakeshi sai ya kuma rungumeshi yana murmurshi mai haɗe da jin daɗi ganin yadda su zama tamkar taurarine sa ƙyalli suke shi yasa suke ta kallonsu. Sadiq na sauri ya miƙawa Mahmoud hannu tare da gaidashi cikin girmamawa. Sulaiman na amsar su Zaid a hannun Huzaifa dake gaida Mahmoud ɗin yace. “Welcome back my son.” sai kuma suka kalli Raihana dake cewa. "Yah Salam Zaid haka ka girma”. Samira na amsar Zaitoon tace. “Yanzufa ya danne Zaitoon”. Murmurshi mai cike da jin daɗi tayi tace. “Ai kuwa kamar ta fishi tsowo”. Da sauri Huzaifa yace. "A'a fa Aunty Fariyda mace bata taɓa fin namiji tsawo ko yaya in dai za'a godasu sai anga na mijin yafi tsawo, nimafa nafi Aunty Hafiza tsawo”. Mare ƙeyarsa Hafiza tayi tace. “Dama ai nasan haka zaka ce”. Sai kuma duk suka haɗa baki wurin gaida Mahmud ɗin da tuni ya nufi motar shi da Sulaiman yazo dashi, ba yabo ba fallasa ya amsa musu gsisuwar ba tare da ya juyo ba. Haka yasa suma duk suka biyo bayansa Hafiza da Samira motar Hafiz suka shiga, Fariyda da Raihana da Huzaifa kuwa motar Sadiq suka shiga. Huzaifa ne a gaba riƙe da Zaid, Zaitoon kuwa tana can hannun Samira, ba tare da ya janye idonsa daga bayan motarsa da Sulaiman ya ɗauko yazo ɗaukrsa da shiba ya ɗan ɗaga hannunsa yayiwa su Hafiz da Sadiq alamun su tsaya, haka yasa duk suka tsaya ba tare da sun kashe motocinba suka maida hankalinsu kanshi shi kuwa Mahmoud juyowa yana kallon Sulaiman da ya iso kusa dashi. “Shiga mu tafi mana”. Da hannu ya masa nuni daya buɗe bayan motar. Kai Sulaiman ɗin ya jinnina cikin jin karsashi da fatan cikawa Jidda dake baya burinta na samun kusanci da shaƙuwa da Mahmoud wanda suke fatan ya kaisu ga aure, yana buɗe marfin motar ya watsa mata kallon da yasa ta saurin yin ƙasa da kanta tace. “Yayah barka da dawowa”. Tsuƙe fuska yayi yana mai watsa mata kallon takaici ya nuna mata hanyar fita sai kuma ya juyo yana kallon Sulaiman. “Akan me zaka kwaso ko wanne irin tarkace ka cusa min cikin motata kasan ba kowa yake shiga min mota bako, ke fice min da gani kar in ƙwaƙwali indon kallon mayun nan da kasan kowa ka samu zaka kwaso da sai ka ɗauko motarka ai”. Ya ƙare maganar ba tare da ya kalleta ba, sum-sum ta fito tana kwɓe fuska motar Hafiz dake bayansu ta buɗe ta shiga baya kusa da Hafiza, ita kuwa Fariyda baki ta taɓe tana mai ƙara yin ƙasa da kanta don har yanzu bata bari sunyi ido biyu ba shayin haɗa ido dashi ma take yi. Da sauri Samira ta fito tana miƙo mishi Zaitoon, amsarta yayi yana mai kallon Huzaifa yace. “Huzy kawo Zaid”. Cikin sanyi Huzaifa y fito tare da miƙawa Raihana hannu ya amshi Zaid ɗin tafiyar Huzaifa ta lukutayen yara yake kallo haka nan ya ɗanyi murmushi gefen baki cikin son ɗan yayartasa da ƙaunarsa da yadda lukutancinsa ke sashi nishaɗi yace. “Kacewa Farriyyhah tazo nan”. Fuska Huzaifa ya ɗan kwaɓe cikin alamun ɗan shaƙuwarsa dashi yace. “Our Uncle wacece haka”. Ido ya zubawa Fariyda dake jin duk abinda suke cewa kamar yadda duk sauranma keji saboda kusancin su da ida yake da kuma sauƙe glass da sukayi dan jin dalilin tsaidasu da yayi. “Farriyyhah zo nan”. Ya faɗa yana shiga gaba rungume dasu Zaid. Jidda kuwa kai ta jinjina cikin fusatar zuciya da zafin kishi da ƙara kafa zuƙar cimma burinta ita ta koreta wannan yar girman kan kuma ya kirata. “Aunty Fariyda kije sai mun haɗu a gida”. Sadiq da Raihana suka haɗa bakin faɗa, ido cike da yanani na sanyi tace. “Sadiq mu tafi kawai ni fa ta gida nake son mu fara ina son ganin Baba Malam dasu Mami”. Da sauri Sadiq yace. “To ai ko a mota tane ma ni bazan biya dake can ba saida sanin Yah Mahmoud ɗin in ya baki izi kafin in kaiki in dai ba so kike malam yayi fushi da niba”. Sulaiman da tunda yasashi buɗe mota ya kori Jidda ya zuba mishi ido har yanzu bai ɗauke kallonsa a kansa ba da mmki mai tafe da nazari. “Madam ke muke jira”. Ya faɗa yana kallon Fariyda, a hankali ta shiga bayan motarsa Prado ce baƙa, bata taɓa ko taɓata ba kai ko tsayuwa kusa da itama bata taɓayi ba sabida sanin halin masifarsa yo ko Hafiz ma bai taɓa shigarta ba, Amina sau ɗaya taɓa shiga, wacce yaje da ita gaida Baba Malam ta shiga Benz ce, duk motocinsa baƙaƙene masu sheƙin sabunta da gyara tana shiga Sulaiman ya rufe ƙofar. Tunda ta shiga taji alamun an buɗe but da alamun ana sassaka kaya a ciki, kusan 13 minute ana shirya kaya a ciki kafin ya maida marfin but ɗin rufe, ya juya ya shiga gaba driver seat yaja motar. Yayin da Hafiz dake bayan Sadiq kuwa tuni sunyi gaba. Tunda suka shiga motar ko tari bata ƙara yi ba, sai wayarta da take ta jujjuyawa kanta a sunkuye duk sanda ta tuna abinda yayi mata sai tayi saurin rumtse idonta tana mai tsumashi matsayin ƙanin miji bata taɓa zato ko tsammanin wannan tijarar ba daga gareshi, lallai ta yarda Mahmoud ya ƙware a tijara da iya iskanci na gasken gaske. Shi da Sulaiman kuwa suna hira duk da ƙarfin hirar Sulaiman ne yake yi da dariya harda ƙyaƙyata shi kuwa sai ɗan murmushi dake nuna eh sosai yake jin daɗin hirar. Tafiya mai tsawo sukayi wacce bata san ina sukeba saboda kanta dake sunkuye jin an buɗe gate ne yasa ta ɗan ɗago kanta, numfashi mai cike da farin ciki jin dadi ta sauƙe ganin sun kutsa kai cikin farfajiyar gidansu, ido ta lumshe tare da ɗaukar hand bag dinta ganin sunyi parking ne yasa ta buɗe marfin motar da sauri ta fara kiciniyar sauƙowa dan tudun motar yasata ɗan riƙe gefen ta fito dai-dai lokacin Dr Nasir ya fito part ɗin Mami da nufin shi ga part ɗin Baba Malam cikin sauri ya juyo kanta da sassarfa ta nufeshi tana isa inda yake ta rungumeshi. Mami dake biye dashi a bayane ta tsaya cikin mmkin ganin Mahmoud da Sulaiman da suka fito cikin motar shi kuwa Mahmoud tunda ta abka jikin Dr Nasir ya kauda kanshi daga kansu. “A'a ikon Allah mutanen India barka da isowa, sauƙar yaushe?”. Sai kuma ta meda hankali kan Fariyda data rungumata ta baya tana faɗin. "Mami i miss u”. Ta ƙare maganar cikin zubda ƙwallan farin ciki. Tana ɗan murmushi mai cike da jin daɗin ganin yar tata ta