← Book details Sakar Makafi Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 48 OF 95

Sashe 48

Sakar Makafi Part 2 Complete Hausa Novel · about 7 min read

Ƙarfe tara dai-dai na safe ta fito kitchen bayan ta gama shirya komai.
Goggo Dada tace.
“Na gama shirya su Zaid kema jeki shirya dan naji Mahmoud na cewa zakuje gidan Bappa Lawan dan tun jiya Abba yace ya kaiku ku gaida Mama”. Kai ta gyaɗa alamun to, sannan ta nufi sama tana tuna yadda sukayi da Jidda ranar da su Goggo Abu suka zo duba Zaid suna tafiya tazo wai zata duba Mahmoud da jiki.
Fariyda tace yana bacci Jidda ta dage wai ai ganinsa zatayi kawai ta fito ita kuwa Fariyda tace mata. "Sai dai ta jirashi a nan sai ya fito ta ganshi ita ba'a shigar mata bedroom. Banda Huzaifa da sukayi haka a gabanshi a parlour Fariyda a sama ba wanda yasan suyi haka.
Da wannan tunanin tayi wanka ta shirya, cikin wani tattausan lace mai masifar kyau da taushin da ka ganin lace ne mai zadar gaske, Sky blue ne sai ratsin pink and orange color kaɗan kaɗan ɗinkin riga da pencil siket ne, rigar kuma half garene wanda aka kamashi cib cib da jikinta, siket ɗin kuwa tamkar saida aka gwada hips da mazaunenta aka ɗinkasa yayi caras a jikinta, ta kitse jelarba dogon gashinta bayan ta tubƙe gashin da ribbon pink collar, ɗaurin a setta ta murza mai ɗan karkata, tasa yan kunnen gold da sarka masu ɗan sauƙin girma, shantilly Veil medium size orange color ta ɗan ɗaura akanta tare da ɗan yaneshi ta maida jelarsa ta baya, sai takalminta mai ɗan madaidaicin tudu Pink da yar jakarsa shima pink.
Yar ƙaramar wayarta da tunda ya kwace babbar ta fito da ita ta fara amsa kira dashi ta saka cikin jakar, turare ta ƙara feshe jikinta dashi daga nan ta fito. A parlour Ummi ta sameshi tsaye riƙe dasu Zaid Ummi na cewa.
"Duk saurinka fa dole ka jirata, dan da ita Abbanku yace kuje”. Fuska ba walwala yace.
"Hafiz ya kaita”. Ganinta ne yasa Goggo Dada cewa.
“Fatabarakallhu feeh ahsanil khaliƙin kai masha Allah Fariyda na kinyi kyau kin ganki kuwa tamkar fure sai sheƙi da ƙyalli kikeyi”. Cikin jin kunya ta ɗan sa tafin hannunta ta kare fuskarta tare da cewa.
"Nagode”. Ummi ma ita ta zuba wa ido cikin tsananin sonta tace.
"Ai ɗiyata ba bayawa bace wurin kyau ga ado da gayu, Allah ya tsare minku”. Tana kallon Hafiz da ya fara ɗaukarta hoto tace.
“Amin Ummi na”.
Baki ya taɓe tare da juyawa ya fita.
Da sauri Goggo Dada tace. "To sai kun dawo ko Allah ya kiyaye hanya”. Amin tace tare da juyawa ta fita, Hafiz da Samira na biye da ita a baya, suna fitowa harabar gidan Hafiz yace.
"Wow Aunty kunyi masifar dacewa fa da Uncle Mahmoud ni sai yanzu ma naga ashe shima Sky blue ne collar kayansa.
A fakaice ta kalleshi lokacin da yasa su Zaid a bayan motar rowar da baya son a shiga ya maida marfin ya rufe, wani datsetstsen getzna ne Sky blue a jikinsa sai ƙelli da sheƙin mai yake bazawa, rigar half jombace cib da jikinsa.
Sai hula damanga mai zane baƙi da Sky blue ɗin, sai takalmin half cover suma baƙaƙa.
Juyawa yayi ya shiga drivern seat ya maida marfin gib ya rufe.
Da sauri Huzaifa ya buɗe mata front seat yana cewa.
"Tab shiga kisha ƙamshi wannan motar kamar shagon saida turare take yaseen, ki duba drawer kuwa chocolate ne iri da ban da ban”. Sai kuma yayi shiru ganin kallon da Mahmoud ɗin yayi masa Camera da dake kafaɗarsa ya jawo yana kallon Zaid da ya miƙe tsaye ya ɗan leƙo kanshi ta gefen Mahmoud Sai kuma Zaitoon ita kuma ta ɗan leƙo gefen Fariyda ɗan juyowa kaɗan sukayi suna kallon yaran sai ya zama kamar kallon love sukeyiwa juna hoto ya fara kebta musu cikin iyawa da ƙwarewa.
Da sauri Hafiz yayi ƙasa da kansa yana ɓoye camara tasa dan kallon gargaɗin da Mahmoud ɗin ya watsa mishi.
Kanta ta kauda daga kallon su Zaid ɗin ta ɗan matso jikin motar dan jawo marfin.
"Ke nifa ba drivernki bane da zaki barni zaune a ciki”. Ya faɗa yana murɗa key ɗin motar, har lau bata kalli ta inda yakeba ta gyara zamanta ganin, Huzaifa ya maida marfin ya rufe yana musu Allah kiyaye hanya. Samira kuma da sauri ta nufi bakin gate ta buɗe musu tana cewa babanta.
“Baba na hutar da kai.
Daga nan gidan Bappa Lawan suka nufa.
Tunda ta shiga baice mata komai ba bata ce masa komai ba, sai su Zaid dake ta wasa a baya Zaitoon tazo tsakanin seat ɗin tana loƙa fuskar Mahmoud tana gwarancin ta harda dariya da ɗan tafa ƴan hannayenta.
Hannunsa yasa ya buɗe drawer chocolate ya zaro guda biyu ya miƙa mata idonsa na kan titin yace.
"Ɓare ki basu”. Amsa tayi itama bata kalleshi ba, ɓaresu tayi sannan ta ɗan juyo hango Zaitoon ɗin ta koma ta zauna ne yasa ta ɗan ƙara karkatowa har ƙirjinta na taɓa kafaɗarsa ta miƙa Zaitoon tana faɗin.
“Gashi zo ki ƙarɓa”. Daga zaunen ta miƙo hannu haka shima Zaid haka yasa dole ta ƙara karkacewar ta miƙa musu, kusan duk ƙirjinta na kan kafaɗarsa. Fuskarta na kusa da tasa fuskar.
A hankali ta juyo zata koma mazauninta, ido ta lumshe jin yadda ya manna lips dinshi kan kumatunta ya sakar mata wani kafurin kiss mai cike da manufa.
Da sauri ta koma ta zauna haɗe da buɗe idonta ta zuba mishi su sai kuma ta ɗan tura baki ganin yadda yake kallonta tamkar ba shi yayi mata haka.
Tafin hannunta tasa kan dai-dai inda yayi kissing din ta fara gogewa tana turo lip dinta na ƙasa ta kuma ritsa na sama.
Kallon ta yake har lau kuma tuƙin yake yi.
Hannunsa ɗaya yasa ya tallabo ƙeyarta haɗe da ɗan jawo kanta kusa dashi, manna bakinshi yayi kan nata, ya tura tongue dinsa cikin bakinta ya kamo nata tongue din, a tare suka sauƙe ajiya zuciya mai nauyi, lumshe idonta tayi dan bata da ƙarfin halin kallon tsaurin idonsa sai kiciniyar ƙwace kanta da take yi sha kuma ya hanata damar samun yin hakan.
Su Zaid kuwa ko inda iyayen nasu suke basu kulaba, sunata hidimar cin ƙwalamarsu.
Hoon da sukaji ana danna musune ya dawo hayyacinsa, zare tongue dinsa yayi tare da meda hankalinsa kan tuƙin yana kallon motar da ta kauce musu gudun karo dan hanyar hannu ɗaya ne. Murmurshi mai motar yayi tare da cewa.
“Oga ka bari ku koma gida mana, gudun kar kuyi hatsari. Ya ƙare maganar yana buɗe idonsa da kyau yana kallonsu ta glass ɗin gaba dan na gefe da gefe tintek ne.
Shi kuwa Mahmoud hararnshi yayi sai kuma ya juyo kanshi kanta murya a dake yace.
“Sai na tsinka lips nan in baki daina turo min shi gaba, ba kiyi ta tsotso na ciki kamar mayya da haka kika kusan cinye min tongue, kuma dole in rama tunda ke baki iya gaisuwa ba”. Ya ƙare maganar yana ɗan karkatowa ta inda take.
Baki ta tura tana narai-narai da ido tace.
"To ina kwana”. Ta faɗa tana gyara zamanta.
Har lau idonsa na kanta yace. "Na roƙi ki gaisheni ne?”. Baki ta kuma cinnawa tace. "Naga kana ta kallona ne ai yanzu kace ban iya gaisuwa ba”. Wayarta ya zaro daga cikin aljihunsa ya miƙa mata yana meda hankalinsa kan tuƙin da yakeyi yace.
“Karɓi gudumarki karta ɓula min aljihu”. Da sauri ta amsa tana faɗin.
“Ni dai wayata ba gudu bace wayar ɗari takwas harda hamsin ɗin ne za'a cewa guduma”. Bai ƙara ce mata komai ba sai lips ɗinshi da ya taune idanunsa da suka sauya launi ya tsaida kan titin sai ajiyan zuciya da yake saukewa bana daƙiƙu kaɗan-kaɗan.
Suna isa harabar gidan ta hangi motar Salim da alamun shi da Salma duk suna cikin gidan.
Kai tsaye ya wuce parlour Bappa Lawan su Zaid na gaba yana biye dasu ita kuma tana bayansa.
Fuska ɗauke da murmushi Bappa Lawan ya jawo su Zaid ya ɗaurasu kan cinyarsa yana kallon Mahmoud da Fariyda da suka zauna a gabanshi.
"Yau dai Mahmoud ka kyauta ka kawo min aboki da amarya”. Cikin girmamawa yace.
“Tunda muka dawo ina son zuwa to baƙi shiyasa, sai yau Allah ya nufa”. Salim dake gefensa yana fuskantar Mama da takeyiwa Fariyda wani irin makirin kallo mai cike da baƙin ciki da hasada ne yayi murmushi tare da cewa Fariyda......

By
*GARKUWAR MARUBUUTA**SAƘAR MAKAFI*
Page 66
Na
*Aysha Aliyu Garkuwa*
Chapter 48 · 0% Book details