Sashe 7
Sakar Makafi Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Numfashi mai sanyi ya fesar lokacin da ya shigo cikin parlour, zama yayi yana mai lumshe idanunsa saboda yadda yake jin cikinsa kamar ahautsine kamar mai jin amai. Ledan hannunsa da ke ɗauke da tambarin Agora mall ya ajiye kan Centre table ɗin gabansa, sai kuma ya maida bayansa ya jingina da jikin kujerar, Riƙe da kayansa ta fito parlour jin motsinsa ne ya tabbatar mata da dawor nansa, gefenshi ta ɗan tsaya tare da miƙo masa kayansa murya can ƙasa tace. “Ga kayan naka”. Banza yayi mata, sai ma ƙara rumtse idanunsa da yayi dan jikinsa dake tsuma yake yi ta ciki. “Ga kayanka”. Ta kuma faɗa hakan ne yasashi buɗe ido ta gefen idon ya ɗan kalleta, ɗan gajeren tsaki mai sauti yaja yace. “Nine zan sake sa kayan da kika gama jagulawa, kin buɗa min wondo, ki wani cemin ga kayana, sai ki riƙe kije kiyi ta sawa har iya tsawon rayuwarki”. Ido ta zuba mishi ganin yana miƙo mata ledar daya shigo da ita tare da cewa. “Gashi daga yau karki sake samun turarena, kai karma ki sake kallona ni da kayana ma bare ki taɓa min, in kuma zakici gaba da yi min satane Bismillah”. Sassayan ƙamshin dake fitowa a ledar ne yasata amsar ledar tare da juyawa ta koma ciki da kayanshi a hannunta, har saida taje bakin ƙofa ta ɗan juyo tace. “Na gode”. Baki ya taɓe tare da meda kanshi ya jingine gami da binta da ido har saida ta ɓacewa ganinsa ya lumshe idonsa. Da sauri ta lumshe idanta tana mai ƙara jan wani sassayan numfashi shaƙar ni'imtaccen ƙamshin turarukan masu ɗan karen daɗin da zai bayyana tsadarsu har kala 4 da ya saya mata ta rinƙa fesawa ɗaya bayan ɗaya in 2 minute bedroom ɗin ya ɗauki wani irin dausayin ƙamshi mai sakar da kasala, yess duk turarukan da Sa'ad ya kawo mata masu ƙamshi ne da tsada, amman in an haɗasu da waɗannan sam bazasu jiyu ba, ƙara fesasu tayi a jikin pillows ɗin, sai kuma ta jawo nasu Zaid su kuwa sassayan ƙamshi garesu sai set ɗin mayuka masu masifar kyan gaske da tsada kama da sabulu mai shampoo conditioner ba abinda babu a ciki, harda su mouthwash brush Makilin da dai sauransu komai uku uku ne a ciki nata da na yaran wasu tattausan riga da wandon kala uku shigen irin nasa data saka duka wandunan bazasu wuce iya guiwarta baki ta taɓe tana waresu tace. “Yoh ai ko na saya min bama bazan sake sa nakaba, tunda kai ɗan tijarane ina sawa zakayi min tsirara ka cuceni”. Sai ta jujjuya kayan tana shafa taushinsu tare da kallon price dinsa dake manne a jikinsu ɗan jin tayi tana lissafa kuɗin kayan da sauran tarkacen a ƙalla kusan 1m kenan a ɗan wannan tarkacen dan iya turarenta biyu daga ciki yan ɗari da tamanin-tamanin ne a fili tace. “Ai dama in dai barnar kuɗine kaine kan gaba”. Cikin jin dadin ƙamshin turaren ta ajiyesu ta kwanta tana mai bibiyar status din yan uwanta tana kallon duk wani hotuna da videos ɗin shagalin bikin auren Salma da Salim wanda ake ta shan shagali babu kama hannun yaro. Shi kuwa Mahmoud bacci mai nauyi ne ya dannesa shine ya hanashi amsa video call ɗin da abokansu keyi masa. Bayan kwana huɗu zaune suke a parlour Dr Sarala shi da Dr Imran ɗin, plate ɗin da ta zuba mishi ferfesun jan nama da yasha gadalulluka iri da ban da ban masu ƙarfin gaske ya kalla a karo na barkatai, gamsuwa da tsabtarsu da kuma yadda shi da kanshi yake tayata wanke abubuwan aikin yasa yaji baya ƙyaman ci sai dai ƙarfin gadalulluka da suke buge shi tun kan ya fara cine yasashi zubawa plate ɗin ido, a hankali ya fara ci bisa tursasawar Dr Imran ɗin da kuma mahaifiyatasa, da kyar ya iya cinyeshi dan dama kaɗan ne. Tsumin daurin ganyayyakin da kullum sai ta bashi in yazo ta bashi cikin ɗan glass cup ɗin amsa yayi ya kurɓeshi ido a rufe saboda murdar da har yau bata barshi ba bai samu yayi amai ɗin ba kuma. Kwance take bisa 3 seatter waya take yi da Salma. “Nima ban san yaushe zamu dawo bafa”. Salma tace. “Tun last week dai yacewa Yah Salim an gama komai na Zaid ba abinda ya rage, da dai yace a satin zaku dawo ma, to ban san me ya dakatar da tahowar taku ba”. Tana miƙewa tsaye saboda jin ya shigo bedroom ta wuce. okay an gama komai ma kenan, bari zan mishi magna gsky ni na gaji da wannan zaman jarabar mutum yayi ta zama shiru kamar maye in ma shi bazai koma ba ni zan koma in shiga yan uwana. Ƴar dariya Salma tayi tare da cewa. “Amman dai ke Fariyda kin shiga uku da taurin kai wai yanzu kina nufin har yanzu zaman kare a karofi kikeyi, ki samu irin wannan damar kiyi wasa da ita, Mahmoud a matsayin miji sannan India daga ke sai shi sai ƴan yaranku, kina da duk surar da ko wacce ya mace ke fatan samu shima yana da surar da duk namiji ke fatan samu ku zauna ku hana junanku morar lfyarku da ƙuruciyarku Wlh kina cin amanar hips and breast ɗinki shi kuma kina cutar dashi, dan ba na mijin da zai rayu dake wuri ɗaya da bazaki hanasa samun sukuni ba dole bawan Allah yayi ta hali da fushi yayi yaji ya bar miki masauƙin mana tunda bakya sama masa nitsuwar komai sai azabar barinsa da fitinar tsaye”. Tunda ta fara magnar Fariyda ta zaro ido waje cikin kunya da mmki da takaicin ta yaya ma Salma zata suffanta haɗuwarta da Mahmoud a wannan salon ai har abada ƙanin Yah Amin fa, ai shima ba wannan a ransa a fili kuma tsaki mai ƙarfi taja jin Salma na cewa. “Ai ni Yah Salim baida haƙuri”. Cikin takaici tace “Yanzu dai zaki nuna min kin san namiji kenan, kina son in san kuna kwana ɗaki ɗaya kenan? In na fahimciki so kike ki faɗa min sirrin zaman aurenku kenan ko Salma”. Da sauri tace. “A nifa kar ki canza min magna faɗa dai nake miki, kibi mijinki dama ai tunda kin san nayi aure kan kin san nasan na miji tunda ni ba irin ki bace da zan bar mijina da azaba har yayi fushi dani tunda nasan fushinsa na tare da fushin Allah da mala'ikunsa a kaina”. Harara ta dannawa Salam tace. “Sannu uwata to zageni daɗinta dai kin san ni ba jahila bace”. Dariya mai sauti Salma tayi tana kallonta tace. "Ai gwara jahili da masanin da zai take sani, in zakiji tsoron Allah dai kiji ki bawa mijinki haƙƙinsa, ni kinga nayi nan mijina ya dawo”. Daga nan ta katse kiran. Da sauri ta ɗago idonta jin ƙamshin turarensa, kanta ta sunkuyar zuciyarta na harbawa da ƙarfi. Innalillahi yaushe ya shigo ya jimu kenan, a hankali ta kuma ɗago kanta, har yanzu idonsa na kanta ko motsasu bayayi. ganin haka ne yasa ta fara magna cikin tsoro da rauni tace. “Ni ba mgnarka nakeyi bafa, Wlh ban ce ma yaroba”. Baki ya tsɓe ba tare da ya kulata ba, ya wuce gaban gadon su Zaid dan tun safe daya fita bai dawo ba sai yanzu kusan goma na daren addu'a yayi tare da shafa musu kana, ya juya ya shiga bathroom cikin rashin kuzarin da yake fama dashi yayi wanka. Washe gari da safe da sauri ta isa bakin ƙofar yana gab da fita tace. "Wai sai yaushe zamu koma ne?”. Bai kulataba bai kuma fitaba. “Gsky ni na gaji ina son koma gida”. Ƙofar fita ya nuna mata tare da cewa. “Na riƙeki ne? Ko na rufe ƙofa? Document ɗinki suna cikin briefcase na tunda kin iya sata ki bincika ki ɗauka mana ki tafi tunda ban rufe samaba”. Tunda ya fara magna ta lankwasa kai bisa kafaɗarta ta zubawa fuskarsa da lips ɗinshi ido, wato shi dai in kaji yayi doguwar magna to faɗa zai yi ko soka baƙar magna a kufule yace. “Ke cire mayatattun idonki a kaina kin san bana son kallon maita kin wani addabeni da munafukan idanunki”. Da sauran tayi ƙasa da kanta, tsaki yaja tare da juyawa ya fita. Da harara ta rakashi gami da murguɗa baki tace. “Nidai kam an cuceni tunda aka azabtar dani da zama da wannan mara mutuncin a inuwa ɗaya, in ba dole ba ai bazan kalli ko ta inda kake ba to me na zan kalla fuska ko ysushe kamar ta shanu”. Godiya Dr Imran Patel yayi masa tare da bashi hannu sukayi musabaha lokacin da ya tura masa miliyoyin kuɗaɗen hotel ɗin su da na cinsu da shansu da na aikin Zaid da maganinsa da na zamansu a hospital ɗin da na zirga-zirga da driver sukeyi musu da kuma na mgnin da Dr Sarala tayi masa da duk wata hidimar da akayi musu a hotel din. Tare suka fita daga nan gidanta suka wuce magunguna ta haɗa masa cikin sanyin jiki da karayar rashin ganin alamun nasara a aikin take tambayarsa wani sauyi ya samu a jikinsa yayi amaine ko ruɗewan ciki gudawa ko zazzaɓi ko ciwon ƙirji ko jiri?. Kai ya rinƙa jujjuya mata alamun duk babu abinda yayi sai dai ɗan murɗar da yakejin kuma baiyi amain ba. Tana mai nazari a cikin abubuwan da ta lissafane in yayi wani abu a ciki zata gane ya warke in kuma yayi wani a ciki zata gane bazai taɓa samun lfyar ba, to shi duk gefe biyu da ɗaya yake ɗauke da Amai da jiri ɗaya gudawa da ciwon ƙirji to duk ba wanda yayi bare ta gane wanne mataki yake ciki. Tana mai haɗa masa magunguna tacewa Dr Imran ya maida masa kuɗin daya tura da sunan a bata har sai an san matakin da yake kafin ya biyata in ya warke in kuma bai warke ba bazata karɓa ba. Da sauri ya girgiza mata kai gami da cewa ya bata ne wannan ba biyanta yayi ba in ya warken zata biya na musamman, haka a dole ta haƙura kana ta bashi magungunan da Dr Imran Patel yayi musu tambarin Hospital ɗinsa haɗe dana Zaid dan su