← Book details Sakar Makafi Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 9 OF 95

Sashe 9

Sakar Makafi Part 2 Complete Hausa Novel · about 10 min read

By
*GARKUWAR MARUBUTA**SAƘAR MAKAFI*
Page 48
Na
*Aysha Aliyu Garkuwa*

“In kira ma Dr'nsu ne”. T Cikin fizgo mgnar yace.
“Bana son shishshigi fa, ki fita harkata kin addabeni kin takura min rayuwa ta”. Tana kallonsa cikin mmkin jin yadda sautin muryarsa ta disashe ga alaman ciwo a fili amman a hakama sai ya hantareta ya nuna baya son taimakonta tana kauda kai tace.
“Allah shi ƙara”. Tana kunna ɗan tv gabanta ta fara kallon wani India film. Bai kula ba bare ya tanka, a haka dai har lokacin lafawarsa yayi, can kuma taga ya miƙe zaune kamar ba shiba, su Zaid ya jawo jikinsa ya rungumesu yana ɗan sunsunar wuyansu da kissing goshinsu. Ƙarfe tara saura kwata sukayi landing a Istanbul Airport (IST) Wani irin numfashi mai nauyi Fariyda taja saboda wani irin nataccen sanyi Istanbul ɗin da yayi welcoming ɗinta, wanda yasa a take ta fara tsuma da fara kame jikinta, shi kuwa Mahmoud cikin jan numfashi da jin daɗin weather ɗin sanyin nasu da ya taimaka wurin busar da zafin da murɗan cikin ya fara sakar masa, a hankali yake taka steps ɗin jirgin yana riƙe da karfen gefe-gefen duk tafiyar da yake yi idonsa a rufe saboda jirin da yake ji.
“Ke! Karɓesu”. Ya faɗa idonsa a rufe, cikin rawan sanyi tasa hannunta ta karɓi Zaid Zaitoon kuwa kafaɗa ta maƙale alamun bazata zoba, cikin sanyi yace.
“Barta”. Daga nan yaci gaba da sauka a hankali.
Bayan sun fitone aka kawo musu Bus ɗin da zai kaisu hotel ɗin dan transit dinsu kusan 23 hours ne, sai kusan gobe uwar haka zasu tashi zuwa Nigeria. Tafiyar 37 minutes sukayi suka isa.
Homey Airport hotel shine Abinda ke rubuce kan tamfatsetsen ginin tsarerren hotel ɗin da yake iya kar ganin mai kallon.
Bayan duk sun fito kowa ya nufi Room ɗinsa. A hankali yake jan ƙafarsa da travelling luggage dinsa rungume da Zaitoon bayan sun fito daga lifter. duk abinda yake yi idonsa a rufe yake yi, har suka isa bakin ƙofar Room ɗin nasu, ɗaya daga cikin ma'aikatan hotel ɗin ne dake riƙe da akwatin Fariyda ne ya buɗe ƙofar, baya ya ɗan ja baya yayi musu alamun su shiga, cikin sanyi da tsananin azabar murɗa da yakeji da jirin ya kutsa kai ciki, bisa ƙaramin gadon da yake can gefe kaɗan ya kwantar da Zaitoon da tuni ta maida bacci.
Ganin yadda yake tafiya ne yasa ta tsaya a tsakiyar ɗakin tana binsa da ido. Bakin babban gadon ya iso kamar wanda ke cikin maye ya faɗa kan gadon ba tare da ya cire koda takalmin sawunsa ba, ruf da ciki ya kwanta rib sai fuskarsa dake kallon tsakiyar ɗakin. Kai ta jinjina wa ma'aikacin nasu dake nuna mata manu ɗinsu dake kan bed side drawer ya ƙara mata da bayanin ta duba akwai number kitchen Reception, laundry ya ƙare maganar yana nuna mata wayar Telephone dake kan wani kyakkyawan table dake can gefe da kujeru biyu a gabansa.
Ganin ta amsa mishi ne yasa ya juya ya fita.
Ita kuwa Fariyda a hankali ta ɗan ƙara matsowa kusa da shi kaɗan idonsa a rufe rib yayi tsit kai kace baya ko numfashi saboda yadda yayi shiru ba alamun wani motsi, numfashi ta fesar saboda ɗumin ɗakin yasata jin buƙatar yin wanka ko zataji sauƙin gajiyar dake tare da ita dan in batayi wanka bazata iya rumtsawanba rabanta da wanka tun na bayan sallan asuba da tayi.
Su Zaitoon ta gyarawa kwanci tare da rufesu rub musamman Zaid.
A hankali ta kuma kallonshi a hankali yake jan numfashi.
Gyalen da tayi Rollin kanta ta fara warware wa tare da ɗan ninkeshi ta ɗaura kan kujerar dake gefenta, sai kuma ta ɗan kalli wayarta jin tana ringing.
“Mamy Barka da dare”. Ta faɗa bayan ta amsa kiran ta fara zare rigar ta.
“Barka dai Fariyda ya hanya kun isa lfy”. Numfashi ta fesar dan cire rigar ya taimaka mata wurin jin ɗumin room heater ɗin ya ratsata. “Alhamdulillah Mamy yanzun nan muka iso, ko zama banyi ba”.
Mamy tace.
“To Alhamdulillah Barka da isa lfy ina mutanena sarakunan rigima musamman Zaid uban rikici”. A hankali ta fara yin ƙasa da robar wondon jikinta tare da yar dariya tace.
"Mamy yanzu Zaid ya zama salihi har Zaitoon ta fishi rikici, baya kukan banzan nan”. Mamy tace. “Barka ai yayi lfy ne dama ciwone”.
A hankali ta zare kafafunta daga cikin wondo ta ɗagashi shima ta ninke kamar yadda ta ninke rigar ta ajiyesu kan kujerar ya zama daga ita sai tattausan gajeren wondo da iya karsa guiwa sai bra. tana ɗan ƙara matsowa inda akwaitinta yake tace.
"Haka Ummi tace dama ciwone ke sashi rikici”.
Mamy tace.
"To bari in barki ku huta ki gaida Mijin naki?”. A hankali tace to, tare da juyowa.
Zaro ido tayi lokacin da taga ya buɗe idonsa da yake cike da wani irin launi mai cike da wahalar burɗa da jirin da yanzu ya samu ya ɗan lafa ne yasashi buɗe ido, ido cikin ido sukayi ta ita, da ƙarfi ta saki ƙara mai sauti tare da tsugunawa ta kifa ƙirjinta kan guiwowinta kana tasa hannunta duka biyu ta kama kanta.
Shi kuwa Mahmoud kanshi ya juya gefen hagunsa inda bazai gantaba ya maida idonsa ya lumshe yaci gaba da kwanciyarsa.
Cikin fitinennen kunya da takaicin kanta da kanta ta ɗan ɗago kanta jinsa shiru baiyi mgnaba bai motsaba, ganin ya kauda kansa gefene yasa ta faɗa bathroom da ƙarfi ta maida ƙofar gib ta rufe.
Cikin sauri ta meda idonta ta rufe saboda ganin kanta a madubin ya ƙara ruɓanya jin kunyarta da takaicin kanta ganin yadda take daga ita sai dan wondo and bra jingina tayi da jikin ƙofar bathroom tana sauƙe numfashi ta fara tattare gashin kanta da ribbon ɗinta ya sule wurin cire rigarta.
Wanka tayi da ɗan ƙaramin sabulunsu mai fitinannen ƙamshi da kumfa mai sa sulɓin fata.
Sabon brush and Makilin dake wurin tayi amfani dasu tanayi tana cire idonta daga jikin madubin, alwalar kwanciya bacci tayi.
rigar wankan da ke saƙale a angar wanda cikin ledarsa yake ta ɓare tare da zurawa a jikinta ɗan towel ɗin kai dake ciki ta zare ta sa a kanta tare da manna botur ɗinsa bayan ta kalmashe bakinsa.
A hankali ta buɗe ƙofar bathroom ɗin kaɗan leƙowa tayi cike da kunya mai nauyi da kashe ido. Ganin bashi ba alamarsa akan gadon ne yasata yin saurin fitowa, kai ta fara jujjuyawa bashi ba Travelling luggage dinsa ba briefcase ɗinsa ma, numfashi ta fesar a hankali tare da zuwa bakin ƙofar ta rufe gam.
Kanta ta ɗan kalla jikin madubin bayan ta gama shirin baccin kan babban gadon ta kwanta, bayan ta rage musu hasken ɗakin addu'a tayi ta shafa ta gyara kwanciyarta riƙe da waya tana kunna Wi-Fi ɗin. Washe gari da yamma gab da magrib shiru tayi ta zurawa ƙofar ɗakin indo, tunda ɗaya daga cikin ma'aikatan hotel ɗin ya shigo mata da abinci da flacks biyu daya na ncoffee ɗaya na Custard ɗin su Zaid.
Tun jiya daya fita har yanzu bai dawoba. numfashi mai sanyi ta fesar ta ƙara matse jikinta duk da ɗumin room heater ɗin buɗe ƙofar da akayi ya ɗan sa sanyin ƙusa kai ciki. Lokaci ta kalla a karo na barkatai, to ina yaje? Me yake nufi transit ɗin da yau ne zasu wuce Nigeria kuma shiru har yanzu. Sanyin daya ɗan fitinetane yasa ta tsiyayi zazzafan coffee ɗin, Sipping take yi a hankali dan zafinsa, su Zaid dake bacci rungume da juna ta ɗan kalla, kiran sallah da taji ne yasa ta miƙe a hankali bathroom ta shiga al'wala tayi kana ta fito. Bayan ta idar da sallan isha'i ta jawo wayarta kusan ƙarfe 8:00 pm kuma 9: pm flight ɗinsu zai tashi a yadda yake a tsarin transit ɗinsu.
Hmmmmm taja numfashi mai nauyi, ta ɗaura da cewa. “In ma tafiya yayi ya barni a nan zai koma ya samu Abba daram”. Sai kuma ta ɗan dakata a hankali tace. “Ko zai tafi ya barnima dole zai nemi su Zaid”. Bakin gadon ta kwanta riƙe da wayarta tana kallon travelling luggage ɗinta da yake kimtse da su Zaitoon dake bacci. WhatsApp ta shiga, voice ɗin Aunty Jamila ta gani tana tambayarta ya hanya da jikin Zaid. Amsa ta bata kana ta buɗe na Zainab sai kuma ta kalli Voice ɗin Amina playing tayi.
“Mutanen India ya hanya da sanyin Istanbul, yanzu nai waya da Mahmoud yace ya ɗan fita”. Tana ɗan gyara rufuwa da duvet ɗin ta fara bata amsa.
"Alhamdulillah ga mu nan sanyi kamar zai karmu, ni tuni na gama shiri shi nake jira”. Tana dariya tace.
“Tab ai kuwa Mahmoud da wuya ya shiga Istanbul ya barsa a kwana ɗaya dan baza'a rasa kayan da ake buƙata ba”. Cikin baccin daya fara ɗibarta tace.
“To sai yaushe”. Amina dake kallon Salim da ya kawo mata Amarya Salma tace. “Ni ina zan sani ke da mijinki ba sai ki tambayeshi ba ni sai anjima nayi baki Salma sanuda zuwa”. Daga nan ta katse kiran. Washe gari da safe tana bawa su Zaid abinci tanayi tana tunanin to me haka yake nufi, ido ta zuba wa kayan da wani baturkiye ya kawo mata, wanda jacket ne da Sweater and Scarf, Socks, gloves, kusan kala shida-shida komai na Zaid da Zaitoon iri ɗaya, sai kuma nata Jacket and Sweater and Scarf Socks gloves da long coat irin nasu na can kala shida ko wanne da wonɗonsa sai irin takalmansu sau ciki sai turaruka.
Tunani take to hotel ɗin ne suke bayarwa ko shine ya aiko, tsaida nazarinta tayi akan hotel ɗin ne ke badawa customers dinsu ganin ma'aikacinsu ne ya kawo mata, kamar yadda duk lokuta ukun cin abinci suke kawo mata abinci har room ɗin nata safe rana dare, sai coffee da shima suke kawo mata a kai akai da abincin su Zaid kala da ban da ban. Goge musu baki tayi da tissues kana ta ɗaurasu ka yan kekunan wasa da aka kawo musu, kayan ta ɗauka ta shirya cikin wardrobe ɗin saboda akwatinta ba fili.
Waɗanda ta sawa su Zaitoon ɗin ta ɗan kalla Sweater ɗin da aka saƙa da farin ulu da haɗin pink yayi masifar musu kyau. Ɗan abincin ta ci. Sai kuma ta kunna TV tare da gyara zamanta, cikin jin dadi ganin wani kekkyawan film da suke yi na yarensu ganin akwai Subtitle English ne yasa ta sauƙe numfashi taci gaba da kallo cikin jin daɗi.
Washe gari da safe tana kallon ci gaban Film ɗin jiya da take kallo wanda kullum suke yi na awa ɗaya. Kiran Ummi daya shigone ta amsa cikin sauri.
“Barka da rana Ummi”
Ummi tace.
“Barka dai ɗiyata, ya Istanbul ta riƙe mana ku, duk mun cika da kewarku mun ƙosa ku dawo”. Cikin girmamawa da son Ummi da kewarsu tace.
“Allah Ummi nima nayi kewarku, jiya su Zaid har Abba Abba sukayi ta kira bayan Hafiz ya haɗamu munyi video call dashi”.
Cikin kulawa Ummi tace.
"Allah dai ya dawo mana da ku lfy yasa jinkirin ya zama al'khairi, ina Mahmoud ɗin yana nan ko ya fita”. A takaice tace. “Baya nan”. Ummi tace. “To ina su Zaitoon”.
Juyowa tayi tana kallonsu tace gasu sunata wasa.
Ummi tace.
“Ton sai anjima ko”. Daga nan sukayi sallama.
Washe gari da yanma Ummi ta kuma kiranta bayan sun gaisa ne tace.
“Ya Mahmoud da jikin”.
Shiru ta ɗanyi tana tunanin bai da lfy kenan yees tun a jirgi ta lura baida lfy ranar da suka zo sai kuma ta ɗan meda hankalinta kan Goggo Dada da ta ɗan ɗaga sauti tana cewa.
“Hello Fariyda jikin nasa da sauki ko”. Da sauri tace. “Eh Ummi Alhamdulillah da sauƙi Goggo Dada ya fita bayan nan mafa”.
“To Allah ya ƙara sauƙi in ya dawo kice masa Hajja Dada na son yin mgna dashi ne taji ya jikinsa gashi kuma baya amsa kira, mu kuma yanzu zamu wuce Kano munzo mun dubatane in ya dawo ya kirata”. Ta ƙare maganar da miƙawa Hajja Dada wayar nan suka gaisa tare da tambayarta jikinsa daga nan sukayi sallama.
Yau kwana biyar kenan daren na shida, har yau bashi ba labarinsa, komai na buƙatarsu kan su nema ma, an kawo musu, Movie da take kallo da masu dogon zango ɗin da take bibiya ya taimaka sosai wurin jin dadin zaman ƙasar.
Gyara kwanciyarta tayi tare da jin voice ɗin Mamy.
“Me kikeyi a online a tsohon daren nan ina mijinki ya jikin nasa da sauƙi ko”. Da sauri ta rufe Wi-Fi ɗinta ta fara addu'a kwanciya bacci da mgnar zuci to wai ina yake? To make damunsa ne? To ni da ban san ina yake ba me zan masa.
Yau kwanasu takwas cib-cib kenan a Istanbul.
Cikin wani irin tsuma da karkarwa yake wani irin galabaitaccen kakarin Aman da tun jiya ya ɓalle mishi, ido ya rumtse da ƙarfi saboda masifar jirin da yake ji..........
Chapter 9 · 0% Book details