← Book details Sakar Makafi Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 81 OF 95

Sashe 81

Sakar Makafi Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read

A hankali ta lumshe idonta fuska a yamutse ta buɗe idon ta tsaida kallonta kan fuskarsa da Saka nose maks ga baƙin glass ɗinsa. cikin mamaki ta juyo kan Sadiq sai kuma ta jingina da kujerar dan ganin Sadiq ya maida ƙofar ya rufe yana faɗin. “Allah ya kaimu lfy”. Baba Malam dake gabansu yana ta jero musu addu'o'in isa lfy da neman kariya ta zuba wa ido, tana amsawa da amin kamar yadda duk Aunty Saddiqa suke amsawa a hankali motocin suka fara fita gidan, shine mota ta huku data fita, yana fita Motar Mujahid na shiga shida Yah Farooq da dake kallon motar dasu Zainab ke ciki ɗan kaucewa saura motocin dake fitowa yayi. A jere suka biyosu a baya. Zuciya cike da mamaki take kallonsa tamkar taga sabon halitta ta yaya akayi yasan yanzu zasu tafi? ta ina ya shigo? Malam ya sani kuwa? Me yake nufima to?. Su Aunty Saddiqa kuwa da basu gane shiba shiru sukayi, sai Zaid ne ya zame ya isa jikin seat ɗin Mahmoud ɗin yana leƙo fuskarsa yace. "Appiy”. Ya salam shine abinda Aunty Rashida ta faɗa a ranta, Aunty Saddiqa kuwa ƙasa tayi da kai ganin Zaitoon ta rarumo Zaid ta tsaya kusa dashi tana faɗin. Owowo Appiy!”. Ɗan juyowa yayi yana shafa kansu cikin so da kulawa yace. "Hello my happiness kunyi missing Appiy ko?”. Da sauri duk suka miƙa mishi hannu suna ƴar dariya harda kerketawa. Jawosu gaba yayi, maƙale masa wuya sukayi Zaid ta gaba Zaitoon ta gefen kafaɗarsa, yana kissing Cheek dinsu ya ɗan kalli Aunty Saddiqa da tayi kamar bata cikin motar yace. "Our Aunty Barka da safiya”. Da sauri ita da Rashida sukace. "Barka dai Appiyn Zaid yasu Abba da Ummi ya ƙarfin jiki”. A taƙaice yace. “Alhamdulillah”. Salma na gyara riƙon wayarta da take magna da Salim tace. "Appiyn Zaid ina kwana ya jiki”. Ba tare da ya kalletaba yace. "Alhamdulillah”. Cikin girmama kai da kunya Saddiga tace. "Appiyn Zaid ka shiga ɗawayyinia damu kai da ba isashshen lfy ba zakayi Long journey damu Form Kano 2 Taraba ai tafiyar bata wasa bace”. Yana kallon titin yace. “Ba komai Aunty Saddiqa, Allah ya kaimu lfy”. Amin sukace baki ɗayansu. Daga nan ba wanda ya kuma magna sai danna waya shi kuwa gyara zamansa yayi da kyau yaci gaba da driving cikin iyawa da ƙwarewa, ita kam Fariyda har lau ko ƙala bata ce masaba, sai wayarta take jujjuyawa a hannunta. Ido ya ɗan zuba mata fakaice, jin alamun yana kallonta ne yasa ta ɗan juyo kanta, ganin wani irin shu'umin kallon yake matane yasa tayi ƙasa da idonta haɗi da tura ɗan lip ɗinta tace. "To ina kwana”. Yana miƙa mata Zaitoon data fara gyangyaɗi yace. "Sai na roƙa ko”. Amsar Zaitoon tayi ta miƙa Salma tana cewa. "Ke gasu karɓi saida nace zan barsu a gida ai kika wani nace kika addabeni sai in ɗaukesu harda su Aunty Saddiqa na tayaki”. Amsar Zaitoon tayi tana murmushi haɗi da ƙara yin ƙasa da muryarta tace. "Wallahi babe Appiyn Zaid ne gashi nan dashi muke tafiya”. Tayi mgnar can ƙasa ko Aunty Rashida dake kusa da ita bata jitaba. Shi kuwa Salim dariya yayi yace. "Hmmm lallai kam na yarda Mahmoud ɗan air ne na mijin duniya”. Shi kuwa Mahmoud baki ya ɗan taɓe yana gyarawa Zaid kwanciya a jikinsa yaci gaba da tuƙi. Aunty Saddiqa ne ta ɗan ɗago kanta ga mamakinta har sun iso Wudil cikin mutuntaka tace. "Appiyn Zaid kawoshi nan, kana driving kuma ga yaro a ƙafa”. Fariyda tayi saurin sunkuyowa ta ɗaukeshi ta miƙawa Aunty Saddiqa. Gyara mayafin tayi dare da musukutawa ta gyara zamanta ta ɗan karkace gefen jikin marfin motar saboda masifeffen sanyin Ac daya kwarara musu a motar, ga kuma sanyin hunturu na December to January da ya rufe weather da hazo. Cikin ƙwarewa ya wuce motoci ukun gabansa dan gudun Hillux ɗin ya zarta nasu. Numfashi mai sanyi suka fesar a tare lokacin da ya kunna musu sautin karatun Alqur'ani mai girma na Sheikh Afif Muhammad Tajj cikin suratul Baƙara. Rashida Charting takeyi da Khadijah tana faɗa mata sufa Mahmoud ne yazo kawosu sune a cikin Hillux nan. Aunty Saddiqa kuwa jingina kai tayi jikin kujerar tana bin sautin karatun Alqur'ani mai girma. Ita kuwa Salma har yanzu waya take yi da Salim. A ƙalla tafiyar awa biyu ana uku sai gasu a Jigawa. Time Fariyda ta duba sun taso ƙarfe bakwai dai-dai na safe yanzu tara da rabi gasu cikin Jigawa. Ɗan juyowa tayi tana kallon motar su Raihana da take bayan tasu, sai kuma sauran da suke can ɗan baya. Shigarsu ɗan gargadar ne yasa duk suka ɗan gyara zama duk da ba wani jin gargadar sukeyi ba. Juyawa yayi ya ɗan kalleta, sai kuma ya maida hankalinsa kan titin, ɗan ronƙofowa yayi ta kanta, hannunsa yasa ya jawo seat belt ido ta ɗan rumtse lokacin da ya ɗan kafa guiwar hannunsa kan caɓɓullenta. "Ahshhh Appiyn zafi fa”. Ta faɗa cikin sasssyan sauti. Da sauri ya ɗan janye hannunsa yana saƙala mata seat belt ɗin kanshi na kusa da kafaɗarta bakinshi ya ɗan manna da kunnenta a hankali yace. "Ki zama jaruma mana, me na wannan rakin, muryar nan da ashhhhhhhh zasu sa in saki siteri fa”. Baki ta ɗan tura a hankali tace. "Allah da zafeeh fa”. Ta faɗa tana rau-rau da idonta. Hannunshi yasa yana shafa kanta yace. "Oh so Sorry”. Aunty Saddiqa kam zuwa yanzu ji take kamar tayi naso a cikin motar, Aunty Rashida kuwa murmushi tayi tana gayawa su Aunty Khadijah duk motsinsu a charting da sukeyi. Salma kuwa ɗan guntun video tayi musu ta turawa Salim tana cewa kaga zahiri ko. Ƙara manna gefen fuskantar yayi da nasa a hankali ya fara goga sajensa kan wuyanta murya can ƙasa yace. “Har yanzu yana zafi?”. Ya ƙare maganar yana yin ƙasa da hannunsa kan caɓɓullenta ya fara shafawa cikin raɗa yace. "Sorry ya bari ko”. Tana gyaɗa mishi kai haɗi da janye jikinta ta ɗan ture kanshi daga kafaɗarta tace. "Appiy kalli gabanka driving kakaye fa”. A hankali yace mata. "Toh ya bar zafinne?”. Da sauri tace. "Eh ya bari”. Madadin ya kalli gaban titin sai ya sunkuyar da kanshi yana kallon kan Papi ɗinsa da yake bayyana masa cikar lfyarsa”. Fuska ya ɗan tsuke kamar bashi ba ya kuma ci gaba da tuƙin. Shiru sukayi ba motsin komai sai gudu da yake tsulawa, a ƙalla awa biyu kiran Aunty Sadiya da ya shigo wayarta ne ya katse musu shirun. "Ke wai ku kuna ina ne kam”. Aunty Sadiya ta faɗa. Tana kallon Aunty Aisha dake gefenta a hankali tace. "Muna kusa da ku ai kune a bayan su Raihana ko”. Da sauri tace. "Mujahid ɗin ne yazo da wannan uban Hillux ɗin ya ɗaukeku, ni baki gayyaceni ba ai da nima nan zan shigo”. Ƙasa tayi da murya tace. "Ba shi bane bafa. Appiyn Zaid ne”. Dariyar shaƙiyanci da Aunty Sadiya da A'isha sukayi ne yasa ta katse kira tana tura lip ɗinta na ƙasa juyowa tayi kanshi jin yadda yaja numfashi haɗe da yin miƙa, harshensa ya ɗan zaro haɗe da karkaɗawa a hankali yana ɗaga mata gira alamun. “Ya dai”. Kauda kai tana ƙara rufe jikinta. Kai ya jinjina yana mai ci gaba da tuƙinsa, su kuwa a baya kai baka ce da mutum bama, kunyar shiga motar surki tasa duk sun takure, Salma ce ke ta famar waya da Salim ɗinta suna gulmarsu Fariyda. A hankali ta juyo ta kalleshi lokacin da suka iso Darazau dara birnin bauchi, cikin ƙosawa da masifeffen sanyin da tsuma tace. "Appiy a kashe Ac nan mana, sanyi har cikin ƙashi nafa”. Kallon baya yayi ta mirror a hankali yace. “Su ai zasuji zafi”. Ya ƙare maganar yana zare suit ɗinsa ya miƙa mata haɗi da cewa. “Sa wannan”. Sanyin da takeji ne yasata amsa ba musu, hannunsa yasa ya ɗan karkarta akalar mafesar sanyin gefe kaɗan. Sai kuma yaci gaba da driving yana kallon time har sha biyu ta kusa, cikin kamala yace. "Aunty mu tsaya anan kuyi breakfast ko sai mu shiga Gombe”. Cike da kamala Aunty Rashida tace. "A'a mu ƙarasa cikin Gombe zaifi mun ƙara rage tafiya”. Yana ƙara taka motar yace. "Okay”. Salma ne ta matso ta miƙa mata waya tana faɗin. “Fariydah Yah Salim na mgna”. Amsa tayi cikin Muryar da ta fara disashewa alamun mura da sanyin AC ya sakarmata tace. "Hello Uncle Salim ya gida”. Yana dariya yace. “Gida dai kam da daɗi kin ɗauke min mata kin ɗauke min ɗan uwa”. Cikin sanyin muryar muran daya rabke mata murya tace. "Kahuta da masifa ai yau sai dai yayiwa titi faɗan gashi sai fesa gudu yake yi kamar zamu tashi sama”. Da sauri yace. “Ai shiyasa Abba baya barinsa yayi driving ɗin Long journey dan gudu da yake yi kuma ba damuwarsa bane yana gudu in yaji bacci yace muku zai yi na 5 to 10 minute kuma fa yana tuƙin dan haka kisa masa ido sosai da kinga ya jingina kai da seat yayi shiru to tadashi, dama shi yasa nace a baki waya”. Cikin gamsuwa dan ta sanshi farin sani da bacci in yaga dama a tsayema bacci yake yi, haka yasa tace. "In sha Allah zan kula”. Yana dariya yace. “Bashi wayar”. Fuska ya tsuke lokacin data miƙa masa wayar yace. "Baka da number tane”. A hankali ta miƙawa Salma wayarta, jin wayarsa na Vibrating Fariyda tace. "To ya kira ka ai”. Yana kallon ya amsa wayar. "Dan Allah ka kulla da irin tuƙin da zakayi ka daiga ka kwashe mana mata a mota, wlh da nasan can zaka tafi da na bika yau kwana nawa ka rabani da Madam sannan ka zille kabi taka ni ka barni da rungumar pillow dan haka ka kula da tuƙi ka dawo mana da matanmu lfy karkayi bacci a mota”. Kwaffa yayi a ranshi yace. "Ina wannan mayataccen zai barni in samu natsuwar bacci ya addabeni da tsallen zalama”. Ya ƙare maganar zucin yana kallon Papi ɗinsa, a fili kuwa tsaki yaja tare da cewa. "Kayiwa Sulaiman wannan bayanin”. Daga nan ya katse kiran. Shi kuwa Salim shiru yayi yana nazartar kalamansa murmushi yayi dan in ta kintata dai-dai to zai
Chapter 81 · 0% Book details