← Book details Nakasa Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 99 OF 154

Sashe 99

Nakasa Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Ameena kuwa yau da wuri suka tashi, a hankali suke tafiya ita da ƙawarta Samira, har suka iso bakin harabar inda suke aje motocinsu, shiru Ameena ta ɗanyi tare dacewa Samira.
"Yau baki fito da motarki bane?".
Murmushin Samira tayi tare da cewa.
"Eh yau a napep nazo, Æ´ar uwatace motarta na wurin gyara, kuma sunada biki a danginta, shiyasa na bata nawan".
Cikin fidda numfashi Ameena tace.
"Uwar gidanki ko?".
Kai Samira ta gyaÉ—a mata alamar eh,
cikin sanyi Ameena tace.
"Kinji dadi Samira inamw ace nima Allah zai yaye min kishi in samu in saki jikinda uwar gidana, dan wlh ita dai irin kice."
Murmushi Samira tayi tare da cewa.
"Uhum Ƙawata ai abin mai sauƙine muddin kika sauƙaƙawa kanki to Allah zai sauƙaƙa miki in kuwa kika tsananta wa kanki zakisha wuya, ni da uwar gidana wlh ko ƴan uwa sai haka, bamu da matsalar komai sabida mun sawa ranmu haƙuri, bawaifa bama kishin bane, no ai kishi kumallon matane, amman kishinmu mai tsari mukeyi, ina gaya miki ki saki ranki da abokiyar zamanki zakuji daɗin zama, tunda keda kanki kin shaida min ita bata da kishinki asalami ke gani kike wai kamar bata son mijin nakune, to wlh Ameena bawai bata son mijinku bane ba mamaki ma ta fiki sonshi kawai dai ta iya takunta ne, babu mamaki ma ta fiki sonshi sai dai wata ƙil ita sonta irin son nanne da zaka so miji ka kuma so duk abinda yake so, kawai dai ta iya sarrafa kantane."
Cikin sanyin jiki Ameena tace.
"Shiga motata muje in sauƙeƙi dama ina son muyi mgna".
kai ta gyaÉ—a mata kana suka shiga Mota,
shiru sukayi saida Ameena ta dai-dai ta hancin motarta kan titi kana ta juyo ta É—an kalli Samira cikin sanyin jiki tace.
"Wato ko Samira ni kaina nasan zuciyata bata min adalciba akan Ammin Adeel, na yarda na gane tana masifar son ɗana so kuma na gaskiya, kana tana kawar da kanta akan harkata da mijinta tamkar bata san me mukeyi ba, bawai ina jin na tsaneta bane a a wlh ni kaina ina sonta sai dai ina masifar kishinta,ina son Abban Adeel wani irin son da ni kaina bansa adadinshiba shiyasa nake kishinsa bana son yayi nesa dani, kinga tsabar zugar kishi wallahi yanzu sai yayi ta bina yana son haƙƙinshima sai inji to ai yanada wata matar."
Juyowa Samira tayi ta fuskanceta da kyau cikin wayewa da iya salon kishi na Musulunci tace.
"Kin wahala kin ɗorawa kanki dala ba gammo, ke ƙawata in banda tsaurin ido irin namu na mata ki samu mace da mijinta kice zaki zafafa kishinki yo in dai ita bata zafafabaai ke kuma bai dace ki zafafaba me ruwanki da ita zamanki da ban nata da ban, tsakaninku babu babbancin matsayi ku duk matanshi ne, ki dena sawa ranki yafi sonta, ko ganin wani ƙira nata, ki gyara zuciyarki zakiji daɗin zama da kowa a gidan".
Shiru Ameena tayi jiki a mace dan ta Æ´arda da batun Samira tasan gsky take gaya mata,
ita kuwa Samira cikin kula ta kalleta tare da cewa.
"Ni kam Ameena kiyi haƙuri ba gulma bane menene ya rabaki da mijinki na fari wanda kika cemin yayanki ne ɗan baffanki kuma a wurin iyaye shi kika girma".
Wani nannauyan ajiyan zuciya Ameena ta sauƙe tare da maida numfashi,
ganin haka yasa Samira cewa.
"Sorry bawai na matsa bane in san sirrinki,ina son in fahimci wani abune inji ko laifin ya Amir ne".
Kai ta rausayar cikin sanyi tace,
"Akwai kam, akwai laifinshi".
Cikin kula Samira tace.
"Menene laifin nashi?"
Hankalinta ta maida kan tuƙin da takeyi kana ta fara bawa Samira labarin.
"DADY Baban Ya Amir ƙanin babane uwarsu ɗaya ubansu ɗaya, babanane babba,
Allah ya azurta babana da dukiya da ilima kana da Æ´ara dan mu Æ´aranshi mun kai goba.
Yayinda Dady kuma Allah ya bashi tarin dukiya da ilimi amman É—anshi É—aya ne rak a duniya wato ya Amir É—in,
Mommo matarshi tana masifar sona tun ina ƙarama ita ta roƙi Mamana da Babana aka bata ni,
shine sanadin da yasa na girma a Abuja dan iyayena asalin Æ´an Jada ne.
Ya Amir ya tashi cikin tsananin so da gata shiyasa ya zama sangartacce, kana Ya Amir irin mazananne masu azabar jaraba mace bata isarsu da wuri,
Kuma tun ina ƙarama yake sona sabida Mommonshi ma tace shi tayiwa kamu,
haka kuwa muka taso yana sona nima ina sonshi, to matsalar ya Amir É—an bunsurune baya iya rayuwa saida mace.
Amman ni a lokacin ban saniba hakama Dady bai saniba, amman ita mommo mamanshi ta sani ganin ya tsananta bunsuranci yasa tace, kawai ayi aurenmu in ƙarisa karatuna a gudanshi, ita a nata zaton tunda jarabace kuma mace yakeso to ai in an aura mishi ni zai daina neman mata.
Kuma koda yaji batun aurenmu da iyayenmu suka tayar yaji daÉ—i sosai.
Madadin iyaye ke tsuma amarya tofa shi ya Amir shine ma ke seyo min abubuwan gyara ya kawomin, kuma sosai na dage ina gyara kaina
Alhamdulillah kuwa akayi aure lfy lafiya, muka tare a anan cikin gidan namu side É—inmu nacan nesa dana Dady.

A darena na forko da Ya Amir bai ɗaga min ƙafa bai sahir taminba,
haka yayi ta caccakata kamar ba gobe,
na wahala sosai a wurinsa, washe gari da safe, Mommo da kanta ta gyarani naji dama-dama ta kula dani sosai sanadin haka na ɗanji sauƙi dan mommo da zuciya ɗaya take sona,
still a dare na biyuma haka Ya Amir yayi ta caccakata,
abu kamar wasa ya maidani kamar abinci, rana ta uku nace ni kam na gaji bazan iyaba,
mafarin matsalar kena, dan wlh ido da ido yace min.
"Tunda bazaki iyaba bari in kira Dina tazo ta taimaka min".
Wlh ni na É—auka wasane, dina sakatariyar shi ce kuma arniya ce,
in taƙaice miki a gabana ya kirata yace su haɗu a hotel,
Shine ma farin kishina, dan ji nayi kamar zan mutu,
duk da dare yayi naje na sanarwa Mommo ranta yayi masifar ɓaci ta kirashi baya ɗagawa, koda ta gayawa Daddy yaji baƙin cikinda bazai misaltuba yayi ta faɗa yacewa Mommo.
"Wlh da nasan Amir mazinaci ne da bazan haɗashi da ƴar ɗan uwanaba, ƴarinya da ta kame kanta in haɗata da fasiƙi".
Sosai mommo taita kuka.
Ranan a side É—inta na kwana washe gari daya dawo suka solleshi soso da sabulu,
abin ta kaici sai yayi ta kuka wai to a ƙara mishi wata matar in munyi biyu zamu iya da buƙa tunshi, niko jin zai ƙara aurene tun satin forkoma bai ƙareba nace na yarda ni zan iya dashi".
ÆŠan rage gudun motarta tayi kana ta É—an kali Samira da ta zuba mata ido cikin sanyi taci gaba da cewa.
"Yanajin haka yace to shike nan in sha Allah ya dena bin mata, ke da haka muka koma side É—inmu dake yana hutun amarci,
ranar tare muka wuni yana ta bidirinshi dani,
tun ina jin zafi har na dena ji, kamar wasa cikin kwanaki biyar, muka zama kamar tib da taya,
dan nima na tsumu da mugunguna da yake bani kuma shiyasa nake jin daɗi in muna sex sosai Ya Amir ya liƙe min nima kuma na fahimci ina ɗaya daga cikin mata masu buƙata matsalar da aka samu, rashin sabo da kuma zafin amsar budurci yasa nake ɗan gajiya,
randa mukayi kwana biyar ɗin ne ya wuni liƙe dani koda dare yayi na gaji yayi yayi in bashi kaina na gaza nace ya bari saida safe, ina fir yaƙi, nan na gane ya Amir Harijine,
gashi dare yayi,
ganin zai matsamin yasa na gudu na koma É—aya É—akinmu,
ashe ya kira Dina tazo har cikin gidanmu a É—akinmu na sunna akan gadona,
sukayi masha'arsu tun dare har asuba.
koda na dawo na samu Dina a É—akina,
na kusan kasheta dan da keret aka kwace a hannuna, kuma ina ihu da hargowa har Dady da Mommo sukazo suka samemu a nan da keret Dady ya kwace a hannuna gudun kar inyi kisan kai.
To nan take Dady yasa Ya Amir ya sakeni.

Haka kuwa yamin daɗi dan gaba ɗaya Ya Amir ya fice min a rai na tsanesa sabida Allah ya sani ina ƙyawar zina da mazinatan.

Koda Baba na yaji yaso ya meda auren Dady yaƙi,
daga nan na koma sashin Mommo kamar da mukaci gaba da zamanmu tana sona.

To matsalar forko dana samu itace yawan sha'awa ina yawan shiga damuwa, in begen sex ya dawo min domin gaba É—aya Ya Amir ya dawo dani irinsa cikin sati É—ayan nan da mukayi, ga magungunan daya É—uÉ—É—ura min sun kamani sosai.
Allah ya sani Samira daga nan na zama jarabebbiya, ina tajin tsoro kar naje na samu lusarin miji in boni domin a zaman da nayi dole azumi na yawaita yi shiyake rage min kaifin fitinar da Ya Amir ya raɓa min.
Randa kuma na fara ganin Abban Adeel naji tsoron wani abu da nagani, dan ya zarta ya Amir nesa ba kusaba,
koda na koma gida wlh sai naita mafarki dashi muna sex,
raina da zuciyata sun Æ´ardarmin shine irin mijin da zai iya magance min matsalata, na sani bazan iya jure zama da lusarin mijiba,
shiyasa kikeji ina ce miki bana son Abban Adeel yayi nesa dani, Alhamdulillah kuma shima É—in ba tayan baya bane".
Ta ƙarishe maganar cikin jin kunya,
ita kuwa Samira dariya tayi sosoi kana tace.
"Wato ya Amir ne ya maida min ke fitinenniya".
Murmushi kawai tayi,
tare da karya konan shiga layinsu Samira.
Ita kuwa samira cikin kula tace.
"Yanzu ya Amir É—in yayi aurene?".
Da sauri ta gyaÉ—a kanta tare da cewa.
"Ya musuluntar da Dina tayi istibira'i ya aureta dan itama harijace irinsa, yanzu yaransu biyu yamin takwara da yarshi ta biyun Amina sai É—an farinsu Hisham ita kuma Dina yanzu sunanta Fatima".
Chapter 99 · 0% Book details