← Book details Nakasa Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 33 OF 154

Sashe 33

Nakasa Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Ƙiran Ya Ameenu ne yashigo wayan Ahmad, da sauri Ahmad ya ɗaga wayan.
Daga ɓangaren Ya Ameenu, wanda ke zaune acikin falon Baba Malam, kasancewar dukaninsu suna cikin falon, hakan yasashi sanya wayar a speeker,  yanda kowa zaiji, tambayar Ahmad yayi akan saƙon dayaga Saifuddeen ya turo masa, nan take Ahmad yayi masa bayanin dukkan abun da Saifuddeen ya faɗa masa, inda yace ta hanyar yin tracker Saifuddeen ɗin ya gano inda take.
Nan take gaba ɗaya suka cika da mamaki, domin koda wasa basu taɓa zaton cewa zataje Numan ɗinba, saboda su kwata-kwata ma sun manta da cewa Mama tana da ɗan uwa acan, domin kuwa ba zuwa take ba, suma kuma ba zuwa suke ba.
Ya Ameenu na kashe wayan, Baba Malam dake kishingiÉ—e yana shan fruit salad, É—in da Mamy ta haÉ—a masa ya saki É—an guntun murmushi irin nasu na manÆ´an dottijai murmushi mai cike da ma'anoni da manufa masu tarin yawa,
  cikin baƙin ciki Ya Ameenu ya rusuna gaban Baba Malam ɗin cikin neman izini yace.
"Kayi haƙuri Baba idan kayimin izini kabarni naje ayau ɗinnan na taho da ita gida."
Ahankali Baba Malam ya aje bowl ɗin dake hannunsa kai ya jujjuya mishi alaman a a,  cikin kulawa ya dubi Ya Ahmad, wanda yayi jigum, anutse yace.
"Ahmad ka É—auki matarka gobe ku koma, banason zamanka hakanan, saboda haka ka koma bakin aikin ka."
Cikin salon bada umarni wa yaran nashi ya kalli Habu dake jin tamkar yayi fiffige ya fire yaje Numan cikin haiba da kamala yace.
"Kai kuma Habu nabaka izinin gobe kaje can Numan É—in, badai kasan gidan yayan Mamar taku dake can ba?."
Kai Ya Habu ya jinjina tare da cewa,
"Eh."
Ajiyar zuciya Baba Malam ya sauƙe tare da cewa.
"To nayi maka izini kaje, duk wani abu dakasan na Saifuddeen ne wanda Zaleeha tatafi dashi ka ƙwatosa ka kawomin, sannan ka ɗauko masa kayayyakin aurensa wanda ta tafi dashi, amma kuma koda wasa kada kace zaka ɗauko ta, badai ta zaɓi guduwa da zaman can ba, shikenan kubarta ta zauna acan ɗin, da sannu duniya zata koya mata hankali, kadai ji abun dana faɗa maka ko?".
Da sauri Habu ya gyaÉ—a kanshi alamun eh, shi kuwa Baba Malam a kausashe yace.
"Bana buƙatar ta saboda haka koda wasa kada kayi kuskuren ɗauko min ita, kabarta acan, amma kaya dai dayake mallakin Saifuddeen kada kabar ko abu ɗaya awajenta."
Cike da gamsuwa Ya Habu ya jinjina kansa don shima, zaifison abar Zaleeha'n, ta ɗana ƙunci da baƙin ciki data ɗana musu.
Duban Ya Ameenu Baba Malam yayi cikin kulawa, ya dafa kafaÉ—unsa, kana yace.
"Matarka bata da isashshen lafiya Ameenu, saboda haka ku koma gida kaje ka kula da ita, saboda tana buƙatar kulawanka, in sha Allah Maryam ƴar aljannace, domin takasance ƴa mai biyayya ga mahaifinta, haka kuma ga mijinta, tabbas Maryam ƴa ɗayace tamkar da dubu, sannan itaɗin mafi soyuwa ce agareni, saboda haka bazanso ace kayi mata nisa, ka ɗauketa ku koma gida kaji!."
Cikin yanayin gamsuwa Ya Ameenu yace.
"To."
Gyara zama Baba Malam yayi, cikin nutsuwa yace.
"Kudukan ku idan kuka sake sanya damuwar Zaleeha a cikin ranku, to tabbas zanyi fushi daku, haka ta zaɓa haka kuma take ganin yafi mata, saboda haka mu ƙyaleta, ita da kanta wata rana zata dawo, kutashi kuje kowa yayi sabgogin gabansa, ko da ita ko babu ita zamu rayu."
Haka dukansu suka miƙe, inda Ya Ahmad gaba ɗaya jikinsa yayi sanyi, har acikin ransa yaso ace Baba Malam ya bari aɗauko Zaleeha'n, baiso ace an barta acan ba, duba da cewa ba'a cikin musulmai take ba, sannan basu san ma wani irin rayuwa takeyi acan ba.
Su Ya Ahmad É—in nafita, Mamy ta gyara zama cikin kwantar da murya, haÉ—i da tausasa zance tace.
"Amma Malam kanaga barinta acan É—in shine mafi alfanu?, da a so nane a É—aukota, sai ayi mata koda nasiha ce, nasan gaba zata gyara."
Murmushi Baba Malam yayi tare da girgiza kansa, bowl É—in fruit salad É—insa ya jawo, cikin kulawa yace da Mamy.
"Ina da babban dalilin dayasa nace abarta acan, duniya zata koya mata hankali."
Shiru Mamy tayi tare da É—an jingina bayanta, ta shiga nazari.

Numan.
Cikin kaɗaici haka take gudanar da rayuwarta anan Numan ɗin, sosai takejin ƙyaman mutanen da take tare dasu, domin kuwa a iya arean nasu Solomon gaba ki ɗayansu christan's ne babu musulmi ko guda ɗaya, sai ita da tashigo cikinsu ayanzu, wanda kuma ba daɗin rayuwa dasu takeji ba, tana dai zaunene acikinsu bisa dole, sau da yawa Solomon baya zaman gida, kusan koda yaushe yana gona cikin lamɓunshi na shuke-shuken kayan marmari danginsu ,Ayaba, Gwaiba, Dabino, Kwakwa, Lemun zaƙi dana tsami Kankana Abarba sweet milo Aya, Gyaɗa, ɗanyar Masara, Dankalin hausa dana turawa, rogo, tumatur attaruhu albasa da dai sauransu, wanda shine sana'arsa daya dogara da ita.

Hakanne yasa basosai suka cika zama dashi ba, sabida babu salla babu salati ko yaushe yana can yana yiwa ƙasa aski don inƙanta al'barkatun gonar tasa, itakuwa matarsa Elizabet baƙin halinta ma ya isheta, wanda tun Zaleehan bata fahimta ba harta fara fahimta, hakanne yasa itama take ɗauke mata kai,
Sai dai can gefen unguwar su Solomon akwai rugar Fulani masu mutunci da tsabta,da riƙo da addini sosai Zaleeha ta fara sabawa dasu, wanda kullum sukan kawo mata Nono da Zuma mai kyau da inƙanci wanda hakan yake matuƙar taimaka mata ta samu abin sawa a bakin salati sai kuma ƴaƴan itatuwa da Solomon kan kawo mata.

Yanzuma kwance take akan ƴar katifar da suka bata, gaba ɗaya batajin daɗin gidan, babban matsalan data fara fuskanta ma shine rashin samun ingantaccen wutan nepa, acan Gombe tasaba unguwarsu kwata kwata ba'a ɗauke musu wuta, koda kuwa ma an ɗauke tsanani bai wuce 5 minute andawo dashi, haka koda ta koma gidan su Saifuddeen ma kullum cikin wuta suke, amma tunda tazo nan saita kwana ta wuni bata ga idon wuta ba, kuma koda ma sun kawota bai wuce mintuna 50 sun ɗauketa, ita da ta saba kwana cikin sanyin AC kan makeken gado na alfarma, da tattausan blanket masu taushin gaske amma sai gashi yanzu kusan kullum dare cikin zafi take kwana, hakanne yasa gaba ɗaya takejin komai bayayi mata daɗi, gashi wayarta ayanzu bata samun wadataccen caji, wani lokaci ma tanason shiga yanar gizo don ɗebe kewa, amma rashin ƙarfin network haka yake hanata, dolenta haka zatayi jigum tayi shiru, yanzuma kwanciyar da takeyi ne ya isheta, hakan yasa ta miƙe tsaye, wani ƙaton hijabinta ta ɗauka ta zura daga kanta zuwa idon sawunta dan tasan akwai igiyar aure a kanta wani flat shoe ɗinta ta zura, sannan tafito daga cikin ɗakin.
Babu kowa atsakar gidan, hakan yasa kai tsaye tanufi hanyar fita daga gidan.
Tsayawa tayi daga ɗan nesa tana me hango wani wutsinyan tafkeken kogi Numan, wanda ruwan cikinsa ke gudana da ikon Allah, sosai sanyin wajen ke shiga jikinta, kasancewar da yammaci ne, ahankali ta ƙarasa kusa da kogin, zama tayi akan yashin dake shimfiɗe awajen tare da zura ƙafafunta cikin ruwan, idanunta ta lumshe tare da sauƙe ajiyar zuciya.
Wani sabon shauƙin ƙaunarsa, wanda ke kwance a ƙasan zuciyarta ne ya taso mata, aduk tsawon kwanakin nan koda sau ɗaya ne soyayya da kewarsa, basu ragu acikin zuciyarta ba, kullum da soyayyarsa take kwana take kuma tashi, har yau bata fidda ran cewa watarana zai zo gareta ba, duk kwanan duniya soyayyarsa ƙara ninkuwa take acikin zuciyarta, zuwa yanzu kewa da muradinsa ya zamo wani sinadari na cikin rayuwarta, tajima awajen, ganin magriba ta gabato ne yasa, ta tashi inda ta koma cikin gida, a bakin fonfonsu ta tsaya ta buɗe ruwa mai tsabta, wanda dashi tayi alwala, ɗaki ta koma, koda tayi sallan Magriba, bata tashi akan sallayan ba, har saida ta sallame sallan isha.
Haka nan take jin tausayin Baba Malam na cika mata can ƙasan zuciya, ji takeyi kamar tayi fiffige ta fire ta ganta gabanshi amman bazata iyaba ta rasa meyasa ta kasa yiwa mahaifinta biyayya.
A wani yanki na zuciyarta kuwa, tana yawan tuno Ummi dasu Hayatuddeen da Raliya,
musamman uban gayyan taken haÉ—e fuska taja tsaki duk sanda ya faÉ—o mata a rai.
Yanzunma hakance ta kasance wani É—an gajeren tsaki taja,
tuno yadda ya rinƙa tsotse mata sweet lips ɗinta,
ido ta rumtse da ƙarfi tare da cewa.
"Hmmmm gwarafa dana gudu, in na tsaya wannan zalamemmen zaimin sagegeduwa, mugu duk ya lallatseni caɓɓullena,wannan in na zauna sai ya maida min nono kamar biredi ko bolon-bolon da mutumtaka ya rinƙa wani shana, mugu kawai mai idanun jaraba."
a hankali ta miƙo hannunta ta jawon hand bang ɗinta wanda a ciki aka sa mata kuɗin fansan idonta da rafan sadakinta wanda Baba Malam ya damƙa mata lokacin da za'a kaita gidan wancan jarabebben.
zazzage jakarta tayi gaba É—aya kuÉ—in ta zubesu kan sallayar,
cikin mmakin yawan kuÉ—in ta fara haÉ—e kansu,
ta daÉ—e sosai kafin ta gama kana ta irgasu, cikin mmki tace.
"Kai har dubu É—ari huÉ—u da talatin."
Taɓe baki tayi tare da cewa.
"Uhmmm kasa abokanka da Æ´an uwanka zubda kuÉ—aÉ—ensu a banza, ni É—innan dai nan gani nan bari sadakin agalawa yaseen cinye kuÉ—in sada kinka zanyi kuma budurcina nan gani nan bura awaran mayya ga yaji ga albasa kuma babu damar ci."
Ƙasan pillow tasa ƙuɗin sabida baccin daya fara fin ƙarfinta.
Daga nan kuma kwanciya tayi, domin yau É—in da wuri taji bacci naneman É—aukarta.

Washegari.

Gombe State.

Tun da sanyin safiya Ya Habu ya gama kimtsawa, inda ƙarfe 7 na safiya atasha tayi masa, kasancewar a motar haya zai tafi, saboda idan yaje can ɗin, har motar da Zaleehan ta tafi dashi zai ɗauko, domin kuwa Saifuddeen ne yasaya motar, tunda ta rufe ido ta gwada cewa bata ƙaunarsa kuwa, to bazasu taɓa bar mata komai nasa awajenta, wanda yake shiya saya mata ba.
Chapter 33 · 0% Book details