Sashe 17
Nakasa Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read
By
*GARKUWAN FULANI*
10/4/20, 7:04 PM - Mmn Khalid: Ahankali ta murɗa ƙofar toilet ɗin ta fito, sanye take da wani pink ɗin bathrube yayinda gaba ɗaya gashin kanta ke jiƙe da ruwa, da dukkan alama dai, daga wanka take, fuskarnan tata akwaɓe take sam babu alaman fara'a asamanta, sosai abunda Saifuddeen ɗin yayi mata safiyar jiya yake cinnta tare da ƙara sosa ranta, inda yake ƙara motsa duk wani ɓacin ranta,  ƙarasawa gaban dressing mirror tayi ta zauna, dai-dai lokacin aka turo ƙofar ɗakin aka shigo, azabure ta juyo don ganin kowaye yayi gangancin shigo mata ɗaki babu sallama.
Idanunta ne sukayi mata tozali da Balkeesu, ganin Balkeesu yasa ta sauƙe ajiyar zuciya, tare da juyawa tasoma ƙoƙarin shafa mai ajikinta, don acikin yanayin ɓacin ran da take ciki batajin zata wani iya nunawa Balkeesun cewa tayi farinciki da zuwanta.
Cikin yanayi na tsantsar mamaki Balkeesu ke kallon Zalihan, ba abun daya ɗaga hankalinta kamar ganin gashin Zaleehan ajiƙe da tayi, cikin mamaki haɗi da tsantsar gulma dake cinta tace.
"Zaleeha badai barinsa kikayi yayi ba?."
Juyowa Zaleeha tayi tare da É—an dubanta, cikin rashin fahimtan maganan Balkeesun fuska a haÉ—e tace.
"Yayi me?."
Hararanta Balkeesu tayi tare da cewa.
"Meyasamu gashinki naganshi ajiƙe? inafatan ba kanki kika mallaka masa ba dai ko?."
Wani irin harara Zaleeha ta bankawa Balkeesu, tare dayi mata kallo, irin na baki da hankali É—innan.
Cikin hasala ta furzar da iskan bakinta, inda tace "Allah ya sauwaƙe ni Zaleeha nabawa wani wanda ba zaɓin raina ba jikina, ke koda ma zan iya mallakawa wani kaina, to kidaina tunanin zan mallakawa wannan mugun virginty ɗina.
To wai ma kina tunanin ayanda yake always akan wheelchair zai iya amsan virgin É—in macene, chab shirme ma kenan, mutumin da kullum yake bisa kujera kamar wani sarki."Â
taƙare maganan tana me taɓe bakinta.
Murmushin jin daÉ—i Balkeesu tayi tare da cewa.
"Nasani ko zai iya karɓa abu a duhu."
Tsuka Zaleeha tayi tare da cigaba da shafa body lotion É—inta.
Tana kammalawa taɗan murza powder akan baby face ɗinta, tashi tayi tare da ƙarasawa gaban makeken drawer ɗinta, wani yadi mai laushi wanda yaji ɗinkin riga da sket ta ciro tare da sanyawa, sosai kayan yayi masifar amsar jikinta, sosai surar jikinta ya bayyana, musamman ma hips ɗinta, dogon gashinta ya kama atsakiyar kanta, inda tayiwa kanta wanka da wani turaren oud mai ƙamshin gaske.
Duk abun nan da takeyi idanun Balkeesu na kanta, sosai Zaleehan tayi mata kyau, tarasa meyasa hakanan Zaleeha kowani kaya tasa sai sunyi mata kyau, wannan yana ɗaya daga cikin abun da yasa, akullum kishin Zaleehan ke ƙara ruruwa acikin ranta, akusa da ita Zaleeha ta zauna tare da dubanta, cikin takaicin abun daya faru jiya tsakaninsu da Saifuddeen ɗin tace.
"Bazan zauna ba Balkeesu, inajin kamar ana huramin wuta aƙasan zuciyata, sam bazan iya cigaba da zama agidannan ba, wlh ji nake kamar ana korata daga ɗakin, akullum tsanarsa ƙara yawa take acikin zuciyata, banajin zan zauna har zuwa lokacin da muka tsara in sashi ya sakenin, idan ban gudu yauba to tabbas zan gudu gobe."
Murmshin gefen baki Balkeesu tayi, take zuciyarta tayi haske, dajin maganganun Zaleehan saitaji kaman an ɗauke mata wani nauyi dake kan ƙahon zuciyarta ne.
Gyara zama tayi tare da duban Zaleehan cikin ƙara ƙarfafa mata taurin zuciya tace.
"Bazan ce kada ki gudu yau ko gobe ba Zaleeha, saidai kuma guduwarki da gaggawa, zai iya haifar da rugujewar plant É—inmu, tunda ai in guduwa kikayi da aurensa a kanki zaki gudu ko, ni kuma nafi son ki sashi ya sakeki inma zaki gudun kinga kin fita rayuwarsa salim alim,
sannan kadafa ki manta da cewar shekaran jiyannan aka kawoki, kibar maganan guduwan nan har sai lokacin da muka tsara ya cika please ki tsurfa musu rashi mitunci gidan gaba É—aya ta yadda dole ya sakeki."
Kai Zaleeha ta rinƙa jujjuya mata cikin sanyin sauti tace.
"Bazan iyaba, me mutanen gidan sukayi min da zan musu rashin ɗa'a? Ina son Umminshi dan tanada kirki hakama ƙannenshi suna sona, kuma nima ina sonsu musamman Ummi da autanta,
Kuma shima É—in ya za'ayi in mishi rashin kunyar bayan tsoronshi nakeji yanada kwarjini da yawa, ko idanunshi bana iya jurar gani, kuma dai ko yaya zanyi yanzu yana matsayin mijina ne, ya zanyi mishi tijara Allah yayi fushi dani in tarawa kaina zunubi. Gwara kawai in gudu yafi min al'khairi, bazan iya zaman É—akin nanba da gidan Allah ji nake kamar korata akeyi."
Wani irin mugun harara Bilkeesu ta watsa mata kana tace.
"To mai imani da miji da tsoron Allah ai sai ki gudun kifi ruwa gudu in kinga dama ki dai sani in kin gudun nema tofa da aurenshi a kanki."
Shiru Zaleeha tayi tare da kawar da kanta gefe, tarantse bazata zauna da Saifuddeen ba, tagwanmace ta tabbata babu aure datai ta zauna dashi, tana ji a jikinta da zuciyarta cewa zata jira abun sonta, koda nan da shekara ɗari ne, sam zama da Saifudden banata bane.
Saifuddeen kuwa, hakanan yakejin zuciyarsa wasai tun jiyan,  sosai murmushi ke bayyana akan kyakkyawar fuskarsa, musamman ma idan ya tuna da mood ɗin Zaleehan na jiyan tsantsar tsoronshi ne da fargaba ya hango acikin ƙwayan idanunta can ƙasan tsiwar da take mishi, kaitsaye banɗakinsa ya wuce, wanka yayi sannan yafito inda ya kimtsa kansa cikin wata ɗanyar purpule ɗin shadda mai masifar kyau, sosai yayi kyau, yayinda farar fatarsa taƙara bayyana acikin kayan, shaddan irin ɗinkin nan na half jumper akayi mata,kasancewar haka nan shiyake bayason full jumper yafison half, duba da yanayinsa wanda ko yaushe azaune yake, so bayason duk wani abu dazai takurasa.
turarensa mai daɗin ƙamshi ya fesa, tare da sanya Cumb yaƙara taje kwantacciyar suman dake kansa, ƙarasawa gaban mirror yayi tare da ɗan duban kansa, shikansa yasan cewa yayi kyau, cikin nutsuwa ya danna madannin kekensa, wayoyinsa kawai ya ɗauka, inda ya fice daga cikin ɗakin, koda yazo falon na Zaleeha bai iske kowa cikinsa ba, hakan yasa kaitsaye yafice daga sashin nasu.
Direct ɓangaren Umminsa ya nufa, tundaga bakin ƙofar falon na Ummi yakejin hayaniya na tashi, koda ya shiga nan ya iske su, Ahmad, Ishaq, Wareesu, Saminu da kuma Saleesu, Mudassir harma da Hisham da Jabeer, Aziz gaba ɗayansu sun baje, yayinda aka cika musu gabansu da kayan ciye ciye, Ahmad da Salisu ba kunya haka suke lodawa cikinsu abinci, sam baruwansu da wani surkuntaka, saboda sunaganin duk suɗin ƴan uwan junane, haka kuma Ummi mahaifiyace agaresu, saboda haka babu wani batun noƙe-noƙe, duk da cewar ansan fulani da kunya, saidai sabo da kuma zumuncin dake tsakaninsu ya goge wannan kunyan.
Cikin mamaki yake kallonsu don sam basu sanar dashi zuwansu ba.
Ƙarasowa cikin falon yayi, inda yakai hannu ya zunguri Ishaq wanda ke ta faman suɗe hannunsa wanda yaci masa dashi, bakomai yasashi suɗe hannunba kuwa face daɗin miyar masan, shikam har yau baiga macen da takai Ummin Saifuddeen iya girki ba.
Ishaq kuwa cikin gane wanda ya zungureshi yace. "Banason wulaƙanci fa Saifuddeen, wato wulaƙanci zaka mana saboda mun riga mun damƙa maka amaryarka a hannunka ko?."
Gaba É—ayansu sukayi murmushi inda Saminu yace.
"Manta dashi da Allah, nasan bazai wuce haushinmu yakeji ba, kasan dai Saifuddeen sakaline baison wani ya raɓi masa Umminsa, kuma mumadai Ummin nan nasonmu."
Saminu yaƙare maganar yana me kai loman gandar fatan saniya, wanda yaji haɗi sosai, sai ƙamshin su kanumfari yake.
Kai Ahmad ya girgiza tare da duban Saminu cikin yanayi na tsokana yace.
"Surkinka nefa Yayan matarka."
Hararansa Saminu yayi tare da cewa.
"Kamanta tare mukai wasan ƙasa."
Dukansu suka saka dariya, banda Saifuddeen wanda shi kullum murmushine aikinsa, da haka yasaba kuma hakan yafi yi masa kyau, aduk sanda yayi murmushi idan kumatunsa da tsakiyar gemunshi da goshinsa suka lotsa, sai yayi wani irin fitinannen kyau.
Dai-dai lokacin Ummi da Goggo Dada suka fito daga cikin kitchine, bayansu kuwa Raliya ce riƙe da plate, wanda samansa ke shaƙe da yankakkun kayan fruits, agabansu ta dire musu plate ɗin, duban Ummi Saifuddeen yayi tare da shagwaɓe fuskarsa, cikin body language ɗinsa yayi mata alama da cewa.
"Shine kika wahalar da kanki wajen haɗawa waƴannan ƙattin abun karin kumallo ko bayan ga matansu!."
Gane abunda yake nufi yasanya Ummi sakin murmushi, ƙarasowa cikin falon tayi tare da sanya hannu ta shafi lallausan suman kansa, cikin kulawa tace.
"Ae duk al'barkacin aurenka sukeci."
Jin abun da Ummin nasa tafaɗa yasanyashi sakin murmushi, idanunsa ya ɗan lumshe, ahankali ya dubi Goggo Dada nan yayi mata alamun gaisuwa, da fara'a ɗauke akan fuskarta ta amsa, tare da ƙarayi masa murnar biki.
Nan suka zauna inda suka shiga ɗan taɓa hira kaɗan, su Hisham na gama kammala cin abincin Goggo Dada tasanar dasu cewa zasu buɗe kan ango da amarya tunda dai jiya bata samu taje wajen diner ɗinba, nan dukansu sukayi na'am, inda Aunty Meenat ma da fitowarta daga ɗakin Ummi kenan tace itama zata yiwa ango nasa liƙin, su Adda Rahama da Raihana ne suka firfito falon, nan fa Ummi tace da Raihana taje ta ƙirawo amarya.
Zaleeha kuwa har zuwa yanzu suna tare da Balkeesu, inda Balkeesu ke ƙara fomfata tana kuma kunnata akan kada ta gudu ta tsaya ta fetsarewa mutanen gidan ta yadda uwarshi da kanta zatasa ya saketa shi kuma ta nuna kasheshi zatayi, ita dai Zaleeha abun daya dameta ne ya isheta don wannan karon dai zugar bilkeesu ba abar ɗaukar mai hankali bane, to bare kuma asirin Mama ya riga zugar tasiri.
Ƙoƙarin kwanciya take, sukajiyo knocking door, azaton Zaleeha Zaheera dake kallo afalo ne hakan yasa tace.
"Yes come in."
Ahankali Raihana tatura ƙofar ɗakin tashiga, ganin Raihana yasa Zaleeha ɗan sakin fuskanta, duk da batasan wacece ita ba, amma kallo ɗaya tayi mata ta hango matsanancin kaman da sukeyi da Aljanin gurgun da tsanarsa tayi mata tsaye acikin rai sosai ta yaba da kyan Raihana kuma har ranta taji tana sonta.