← Book details Nakasa Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 132 OF 154

Sashe 132

Nakasa Part 2 Complete Hausa Novel · about 7 min read

Ɓangaren Ameena kuwa wonka tayi mai rai da lfy sannan tayi shirin baccinta.
Tana kammalawa kai tsaye side É—in Ummi ta nufa,
a falo ta samu Ummi da Ahmad suna zaune, hannu tasa ta amshi Adeel daketa miko mata hannu gefe ta zauna tana kiciniyar bashi nono.
Cikin kula Ahmad yace.
"Yauwa Ameena kinada E passport a kusa ne?".
Kai ta gyaÉ—a tare da cewa.
"Eh inada dashi".
Ummi ce ta gyara zama tare da cewa.
"Yauwa to ki kawo mishi, dan zaiyi muku booking ɗin tafiyarku India ta online dan Dr Aliyu yace ya tafi da ke tunda Dr Adnan bazai samu damar tafiya a kuma ana buƙatan masanin jinyar kusa dashi".
cikin mamaki da jin daÉ—i tace.
"Ummi tafiyar har ta zone kenan kuma dani za'a je".
Ahmad ne ya gyaÉ—a mata kai tare da cewa.
"In sha Allah tafiya tazo, dan jibi  ma akwai jirgin da zai tashi zuwa India, sai dai New Delhi zai sauƙa kuma a Mumbai za kuga likitan, to amma dana sanarwa da Dr Acash prasad  yace ba matsala, shi zai taho da Dr zuwa New Delhi ɗin".
A hankali tace.
"Alhamdulillah, to amma  wurin aikina fa Ahmad".
Kai ya rausayar tare da cewa.
"Eh Ya Adnan yaje ya sanar musu uzurinki harma an baki daman  kuyi tafiyar tare".
Wani irin daÉ—i ne ya cika mata zuciya, cikin jin daÉ—in tace.
"To Allah ya kaimu lfy ya kuma bamu sa'an tafiya".
Amin Amin sukace baki ɗaya kana Ummi ta miƙe ta nufi ɗakin Hayatuddeen dan yiwa Saifuddeen saida safe.
Konce ta sameshi system É—inshi na gabanshi, a hankali ta zauna gefenshi,
ido ya zuba mata cikin jin daÉ—in yace.
"Ummi meya hanaki bacci har yanzu?".
Kanshi ta shafa tare da cewa.
"Farin ciki mana, yau babana yana magana da bakinsa".
Murmushi yayi tare da cewa.
"Hakane fa Ummi".
Murmushi tayi kana tace.
"Yauwa batun tafiyarka India, zaku tafi da Ameena, dan Ahmad zaije Dubai sari, Ya Adnan É—inku kuma ba'a bashi dama ba a wurin aikinsu, saboda Dr Arabi baya nan, ba yadda za'ayi a bar sashinsu ba kowa".
Kanshi ya jinjina a hankali yace.
"To Ummi ba matsala, Allah ya kaimu lfy".
Amin Amin tace tana mai son karanto haƙiƙanin abinda ke ƙasan zuciyarsa, amman saidai ta kasa gane shin yaji daɗin tafiya da Ameenan ne ko baijiba,
Abinda kuma nima kaina ban gane ba kenan, because  duk wani yanayinsa sirrin zuciyarsa ne.

Kanshi ta kuma shafawa  tare da cewa.
"Saida safe".
Tattausan murmushi yayi yace.
"Allah ya bamu al'khairi". 
"Ameen" tace kana ta fita daga É—akin.
Ameena da Hayatuddeen ta samu a falon cikin bada umarni tace.
"Ameena kije ki kula dashi, kai auta kazo É—akinsu Raliya".
To sukace mata baki É—ayansu.

Daga nan ta wuce, kana Hayatuddeen na biye da ita a baya.
Ita kuwa Ameena É—akin ta nufa.

Konce ta sameshi yayi lib a gadon jin sallamarta ne ya sashi buÉ—e ido, wani irin sassanyan murmushi ya sakar mata, tare da miko mata hannunsa alamun tazo.
Kontar da Adeel tayi can gefe kana tazo kusa dashi, jawota jikinshi yayi cikin sanyin murya yace.
"Zanyi wanka".
Da sauri tace.
"To".
bathroom ta shiga ta haɗa mishi dukkan abin buƙata, tana fitowa ta sameshi zaune bisa kekenshi amman gaba ɗaya jikinshi rawa yake, sai wani irin zufa ke tsastsafo mishi sabida azaban ciwo da bayanshi keyi.
Ahankali tace.
"Sannu".
Kai ya gyaÉ—a mata alamar yauwa kana ya nufi bayan gidan.

Ganin shigansa toilet, yasa ta gyara gadon, tare da ƙara gudun A/C.
Ba jimawa ya fito daga wankan,  cikin ƙarfin hali da dauriya, ya sauƙa kan kekenshi ya zauna bisa gado,
man Hayatuddeen da turarenshi ya shafa sannan ya konta.

Jawota jikinshi yayi tare manna mata kiss a goshi cikin sanyin murya yace.
"Kinyi bacci ne?".
A hankali tace.
"A a idona biyu".
ajiyan zuciya ya sauƙe tare da cewa.
"Shine ko ki kulani".
Juyowa tayi da kyau kana ta ɗan raɓa jikinshi a hankali tace.
"Yanzufa jinyan bayan zamuyi".
Murmushi yayi tare da cewa.
"To ban ceba, ni lafiyata lau, karki wani ce ai banda lfy ne in kina so dai gani nan ras".
Dariya tayi sabida ganin ƙarfin halinshi,
shima dariyar yayi kana ya ruggumeta sukayi baccinsu a haka.

Washe gari da Safe Dr Aliyu da ya Adnan sukayi sammakon zuwa dubashi, dan Dr Aliyu zai koma Abuja,
bayan sun bashi duk taimakon da zasu iya bashi ne, suka sallami Umminshi suka tafi.

Jirgin da ya kawo su Saminu da Raihana shine ya juya dasu Dr Aliyu.

Sosai Raihana taji daÉ—in ganin Hammanta na mgna da bakinshi.
A ranar dai haka baƙi suka rinƙa zuwa tako ina, Masha Allah.

Zaleeha kuwa sosai Ummi ke kula da ita Alhamdulillah kuma jiki yayi ɗan sauƙi dan ta samu kula na musamman.

Maman Ameena da babanta ma sunzo sun duba Saifuddeen É—in da jiki.

Hakama manya-manyan ƴan kasuwa, da ƴan ƙungiyar Jonapwd, da kuma jami'an sirri na  SS suma sunyita zuwa dubiya a wannan wunin, shiyasa bai samu keɓewa da matanshi ba, Baba Bello ma  da matarsa sunzo haka abokanshi baki ɗaya.

Ishaq kuwa hadda Rashida nshi yazo a daren
shida Saifuddeen sukayi ta hirarsu ita kuwa Zaleeha da Rashida sukayi ta hirarsu.
kafin su tafima tara tayi ganin haka Zaleeha tayi mishi saida safe.

Adda Rahma kuwa yauma da ita aka wuni.
sai yanzu ya Adnan yazo ya É—auketa, haka su Goggo Dada da Aunty Mina duk sun zo.

Hakane yasa Ummi tace Hayatuddeen ya haura sama ya kwana a É—aya É—akin,
Goggo Dada kuma tazo É—akinta Aunty Mina kuma da Raihana su kwana a É—akinsu,

Ranar ma dai Ameena ce ta kwana dashi.

Washe gari kuma, shine ta gama kwana biyunta, kuma gobene da sassafe zasu wuce Abuja dan tuni an gama musu shirin tafiyarsu.

Bayan sallan isha'i  suka ɗan taɓa hira, a falon Ummi ganin tara ya kusa yasa Ameena ta miƙe ta shiga ɗakin Hayatuddeen dan yiwa Saifuddeen saida safe.

Gefenshi ta zauna bisa dukkan alamu mgna yakeyi da Dr Acash dan taji bayanin yadda yakeji yake faÉ—a.
juyowa yayi  ya kalleta bayan ya gama wayar cikin kula yace.
"Ameenatu ya akaine naga kinyi shiru".
Kai ta rausayar tare da cewa.
"Kawai zazzaƙar muryarka ne nakeji, tabbas na godewa Allah daya nufeni da jin muryarka, ji yadda kake zuba turanci kamar cikakken ɗan America".
Murmushi yayi tare da riko hannunta a hankali yace.
"Gobe iwar haka muna hanya, ko mun isa ko mun kusa isa, kinyi shiri ko?".
Kai ta gyaÉ—a mishi tare da cewa.
"Shiyasa ma zanje in shiga da wuri,  inyi bacci  dan nasamu in tashi kan lokaci".
Gefen fuskarta ya shafa tare da cewa.
"Da wuri haka, bazaki tayani hira ba".
Miƙewa tsaye tayi tare da rungume Adeel fuska a sake tace.
"Bari inje in turo ma Ammin Adeel tazo ta tayaka hirar ban kwana".
Yi yayi kamar bai jitaba, ita kuma juyawa tayi ta fita daga É—akin.

Saida safe tayiwa su Ummi da Raihana da Raliya kana ta wuce side É—insu.
Kai tsaye falon Zaleeha ta shiga,
ita kuwa Zaleeha ta gama shirin baccinta kenan har ta konta taji sallaman Ameena, a hankali ta tashi ta buɗe ƙofar cikin sakin fuska suka kalli juna a hankali Ameena tace.
"Abban Adeel na kiran ki".
Kai ta gyaɗa alamar to kana ta miƙa hannu zata karɓi Adeel,  da sauri Ameena tace.
"A a barshi kije kiji da rigimar tsohonshi".
Kai ta É—an sunkuyar, tana murmushi.
Itama  Ameena murmushi tayi kana ta juya ta tafi.

A hankali ta zauna abakin gado, abayyane  tace.
"Uhum ni bana son zuwa side É—in Ummi tunda Raihana tazo, ni ban san me nayi mataba, har ga Allah har raina ina sonta ita da É—anta, amman ita na lura ko ganina bata sonyi, ya Allah ka sani ni babu abinda nai mata."
Jiki a mace ta ɗauki ƙaton hijabi tasa kana ta fito ta nufi sashin Ummi.

A falon ta samesu baki É—ayansu, a hankali ta koma gefen Raliya cikin sanyi ta gaida Ummi da Goggo Dada da kuma Aunty Mina.
Hayatuddeen ne ya É—an kalleta cikin kula yace.
"Adda Zaleeha jikin ne?".
Kai ta jujjuya lokacin da taga Raihana nata hararanta ƙasa-ƙasa,
cikin sanyi da neman yadda zatayi ta samu ta shiga É—akin Hayatuddeen É—in tace.
"A a,  na fara bacci ne, to kuma na bar wayata a ɗakinka, ɗauko min its mana".
Kanshi ya ɗan rausayar kana ya miƙe yana shiga ba daɗewa ya fito yace.
"Nifa na dudduba ban ganiba, Hamma Saifuddeen yace kije ki duba da kanki".
Kai ta ɗan gyaɗa kana ta miƙe ta nufi ɗakin.

Su kuwa Ummi  ce ta fara miƙewa tayi musu saida safe.
daga nan duk suka watse kowa ya tafi makoncinsa.
Chapter 132 · 0% Book details