← Book details Nakasa Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 85 OF 154

Sashe 85

Nakasa Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Zaleeha kuwa tunda tayi sallan isha tana nan zaune akan sallayan bata tashi ba, suratul falaq take karantawa acikin ranta, dan nemawa Adda Maryam dama duk wani musulmin daya rigayemu gidan gaskiya gafara awajen Allah.
Shigowar Hayatuddeen ne yasa taÉ—an É—ago kanta ta kalleshi, cikin kulawa yace.
"Adda Zaleeha kizo muyi dinner inji Ummi."
Kanta ta jinjina masa, sannan ta soma ƙoƙarin tashi daga kan sallayan, hijab ɗin jikinta ta cire, nan cikin drawer'nta ta ciro wani ɗan mayafi mai kauri, ta yafa ajikinta, sosai tayi kyau, dan kalan mayafin ya karɓi kyakkyawar fuskarta, duk Hayatuddeen na tsaye ajikin ƙofa yana kallonta, ganin tana ƙoƙarin fitowa batare da ta saka turare ba, yasashi kamo hannunta suka koma cikin ɗakin, turaren daya saya mata ya ɗauka ya ƙara fesa mata, murmushi ta saki tare da cewa.
"Kaidai Hayatuddeen rigima ne dakai, ɗazu fa na fesa turaren kuma har yanzu akwai ƙamshin ajikina."
Kansa ya jinjina tare da cewa.
"Eh naji ai, amma so nake ki ƙara".
Murmushi kawai tayi sannan tabi bayansa suka fice daga cikin É—akin.

Daddaɗan Ƙamshin turarenta shiya fara ziyartan hancinsu, ahankali yaɗan lumshe idanunsa tare da haɗiyan wani yawu daya tsaya masa amaƙoshi, Ameena kuwa da sauri ta juyo dan bakaɗan ba ƙamshin ya tafi da ita, idanunta na sauƙa akan Zaleeha taji gabanta ya faɗi, saboda wani irin kyau da taga Zaleehan ta ƙara, kau da kanta tayi tare da ƙara matsaya kusa da Saifuddeen, har jikinsu na gogan na juna, Zaleeha kuwa cikin nutsuwa ta ƙaraso kan dining ɗin, fuskarta ɗauke da ɗan murmushi tace.
"Ummi barka da dare." Murmushi Ummin tayi, tare da cewa.
"Yauwa dai Zaleeha sannunki, dan kema yau kinsha aiki, daga samun sauƙi kuma sai shiga kitchine".
ɗan murmushi Zaleehan tayi tare da miƙa hannu ta karɓi Adeel, dai-dai lokacin Saifuddeen ya buɗe idanunsa ya sauƙesu akanta, murmushin daya bayyana dimples ɗinta tayi, tare da ɗan manna fuskar ta da ta Adeel ta sakar masa kiss akan bakinsa, cike da ƙaunar yaron tace.
"I miss you my sweet papy na."
Baki Adeel É—in ya wangale yana yi mata dariya.
ÆŠan lumshe idanu Saifuddeen yayi, tare da lasan lips É—insa, dan kiss É—in da Zaleehan tayiwa Adeel haka yaji kaman shi tayi wa, a ranshi yace.
"Uhummm da yadda akeson Adeel haka akeson Abbanshi da duniya tai mana daÉ—i, kalli yadda take son yaron kamar tana son ubanshi".
Kujera Zaleehan taja ta zauna, wanda kuma hakan yasa suke facing É—in juna ita da Saifuddeen É—in, É—an kallon Ahmad tayi cikin muryarta me É—auke da sanyi tace.
"Barka da dare Ya Ahmad."
Hakanan yaÉ—anji tausayinta ya kamasa, fuskarsa yaÉ—an saki sannan ya amsa mata.
Fuskarta ɗauke da murmushi ta kalli Ameena wanda keta ƙara shigewa jikin Saifuddeen, murmushi tayi mata tare da cewa.
"Ummun Adeel sannunki da dare."
Duk yanda Ameena taso daure kishinta akan Zaleeha abun naneman fin ƙarfinta, dole haka ta daure ta ƙaƙalo murmushi, cikin muryarta da ta maƙale tace.
"Yauwa."
Ummi ne tasa hannu ta amshi Adeel É—in, cikin kulawa tace.
"Kawo sa yanzu saiki fa ke dashi kiƙi cin abinci, nasan halinki sarai, tashi ma kiyi seving ɗin mu."
Murmushi Zaleehan tayi tare da miƙewa tsaye, food flasks da kuma plates ɗin ta jawo gabanta, cikin nutsuwa tashiga zubawa kowa abincin,
Kyawawan idanunsa ya zuba mata, a Æ´an kyawawan yatsunta yake kallo, komai tanayinsa ne acikin nutsuwa.
Ameena da gaba ɗaya haushin Zaleehan ya cika zuciyarta, ɗan kallon Saifuddeen ɗin tayi, ganin ya ƙure hannun Zaleehan da ido, yasa taji kaman ta tashi awajen, wani baƙinciki da kishine suka tokare maƙoshinta, gaba ɗaya da zuwan Zaleehan sai duk taji ta raina kanta, hakanan taji babu ma irin ƙamshin da ta tsana kamar ƙamshin oud ɗin da ke jikin Zaleeha'n.
Zaleeha kuwa sam hankalinta ma ba akansu yake ba, cikin nutsuwa ta gama seving É—in kowa, É—an matsowa gabansa tayi ta ajiye masa nasa abincin, komawa tayi ta zauna, tare da jawo plate É—in da ta zubawa kanta abinci aciki, dubanta Ummi tayi cikin kulawa tace.
"Zaleeha ɗan wannan abincin shi zaki ci kuma har ki ƙoshi".
Murmushi ta É—anyi, tare da cewa.
"Eh Ummi, amma idan ban ƙoshi ba zanci na Hayatuddeen."
Kai Hayatuddeen ya jinjina, murmushi kawai Ummi tayi, haka suka shiga cin abincin.
Loman farko da yayi, ya lumshe kyawawan idanunsa, dan kuwa sosai yaji É—anÉ—anon abincin abakinsa, tabbas Zaleeha ta iya girki sosai, wanda har yau yana mamakin a ina ta koyo girki kala kala haka.
Abinda bai saniba ƙabilar su mama sunyi zarra a iya girki kuma Zaleeha Mama ta gado a iya girki kana ta samu horon Mamy iya sarrafa abin da za'aci.

Ameena ma tun aloman farko da tayi, gaba É—aya jikinta yayi sanyi, dan kuwa taji É—anÉ—anon abincin ya banbanta da wanda Raleeya ta saba girkawa, maganan Hayatuddeen ne ya katse mata tunani, inda yace.
"Kai Adda Zaleeha wallahi kin iya girki."
Jin cewar Zaleehan ne tayi girkin yasa duk taji abincin yafita aranta, domin Zaleehan iya girki nesa ba kusa ba.
Ahmad shi kansa yau ya yaba da abincin dan buÉ—e cikinsa yayi yaci sosai.

Zaleeha kuwa ahankali take É—an tsakuran abincin tana kaiwa bakinta, yanayin yanda take tauna abincin cikin nutsuwa shi yasa Saifuddeen yake ta faman satan kallonta.
Ganin haka yasa Ameena tsaida cin abincin tayi shiru, hakanan taji idanunta na neman kawo ruwa, ɗan juyowa Saifuddeen yayi ya kalleta, ganin yanda tayi shiru ne, yasa ya ɗan tsiyayi drinks acikin cup, hannunsa yasa miƙa mata cup ɗin,
Rau-rau tayi da ida nunta hawayen kishi na gab da zubo mata,
Tuni Saifuddeen ya karanci Ameena tanada masifar kishi, har ga Allah yasan ta tsananin sonshi amman yana mata addu'a Allah ya sassauta mata zafin kishinta.
Gani tana gabda zubda hawayene yasa yayi niyar bata abu mai sanyi tasha zataji sassaucin abinda takeji a ranta.
A hankali yakai cup ɗin drinks ɗin bakinta, ɗan shagwaɓe masa tayi, tare da buɗe baki ya bata drinks ɗin, saida tasha rabin cup ɗin sannan ya ajiye, da ido ya nuna mata filet ɗin alamun taci abincin,
kai ta sunkuyar cikin sanyi tasa hannu ta É—auki spoon É—in madadin taci sai tayi ta wasa da cikalin.
Numfashi ya É—an fesar kana yasa hannunshi akan nata,
hannu dake gefenshi murza hannu yake É—anyi a hankali alamun taci. itakam dama abun da take nema kenan, saboda haka saita biye masa, duk dan saboda tanason kawar da hankalinsa akan Zaleeha, Kallo É—aya Ummi tayi musu ta watsar tare da girgiza kanta, dan ta fahimci cewa sam Saifuddeen bayajin kunyarta, Ahmad kuwa murmushi kawai yayi yaci gaba da cin abincinsa.
Raleeya ma ƙasa tayi da kanta, hakanan taji wani iri, sam batason abun da zaisa Zaleeha taji babu daɗi aranta.
Hayatuddeen kuwa baki ya sake yana kallonsu, har acikin ransa yana mamakin dalilin dayasa ayanzu Hamman nasa ke ƙoƙarin nunawa Ameena kulawa agaban kowa.

Itakam Zaleeha kallo ɗaya tayi musu ta maida kanta ƙasa , kwata kwata abun nasu baya damunta, wani lokaci ma sai abun da sukeyi ɗin yana bata dariya, dan ta fahimci kamar Ameena'n bata iya sirranta soyayyarta ba, amma ganin ba huruminta bane, shiyasa ma takeyin kamar bata gani ba.

Saifuddeen kam har acikin ransa da yakeyin hakan dan sassauta kishin Ameena, kana a wani sashin kuwa da gaggan yakeyi dan kawai Zaleehan taji wani abu aranta, Ameena kuwa gaba É—aya ta sakankance, shiya dinga yi mata wani irin kallo, tana mejin wani irin daÉ—i acikin ranta, hakanan idan Saifuddeen na mata hakan agaban Zaleeha take jin kanta kaman tafi kowa a duniya.
ganin ta girgiza mishi kai alamun ta ƙoshine yasa ya sake bata abin sha.
Ɗagowan da Zaleeha zatayi ta gansu ahaka, take taji ƙirjinta ya buga. Cikin sauri ta kauda kanta wani sihirtaccen murmushi tayi kana ta miƙe a hankali hannu ta miƙa ta karɓi Adeel dake hannun Ummi, kana ta juya ta nufi cikin falon,
sam Ummi batayi yunƙurin hanata ba.

Wani irin murmushi Saifuddeen yayi, tare da ɗan cije laɓɓansa, cikin zuciyarsa yace.
*"Ƴarinya yanzu aka fara wasan."*

Hayatuddeen ne ya miƙe yayi ɗakinshi,
Hakama Raliya ta miƙe tabi bayan Ahmad.

Ido Ummi ta zubawa Saifuddeen ko ƙibtawa batayi,
ganin haka yasa itama Ameena ta miƙe ta nufi side ɗinsu dan taje ta sake wonka dan ta lura yau Saifuddeen a matsaye yake.

Shiru falon ba motsin kowa,
gaba ɗaya Ummi ta hana Saifuddeen motsi dan yasan tun yana yaro in ya mata laifi taka hukunta shi da hakan, cikin fargaba ya ɗan gyara zama tare da yin rau-rau da ida nunshi wanda da gaske sun cicciko da ruwa dan bai fahimci abinda yayi yanzu bane ya ɓata mata rai.
kai ya rangwafar tare da mata mgna da yarensu.
"Ki gafar ceni Ummi ban san me nayiba, na tuba gaya min laifiba?".
Kwaffa tayi tare da cewa.
"Uhummmm yayi kyau Saifuddeen kaci gaba da cusawa ƴar mutane baƙin ciki".
Kanshi ya jujjuya cikin alamun mgnarsu yace.
"Ummi me kuma nayi, na kaita gidan su na tayata bada haƙuri, duk sun yafe mata nima na yafe mata, kuma yanzu meya rage?".
miƙewa tsaye tayi tare da cewa.
"Key ɗin ɗakinta zaka bani, ta koma ɗakinta,kuma ka raba musu kwana kamar yadda shariya ta buƙata".
Wayarshi ya zaro tare da rubuta mata.
"Wlh Allah Ummi na mance inda na ɓoye key ɗin amman insha Allah zan neme shi in na ganshi zan bakishi".
kai ta jinjina tare da cewa.
"Tom yayi kyau".
Daga nan ta juya ta nufi É—akinta.
Shiru Saifuddeen yayi yana saƙa da warwara a ranshi, wani irin munafikin murmushi yayi kana ya wuce side ɗinshi, yana tafe yana rubuta wa Ameena saƙo ya tura mata kana kai tsaye ya wuce ɗakinshi.

Wasa farin girki sannu-sannu bata hana zuwa sai dai a daɗe ba jeba, muna gab da shigo wani sashi mai ɗan karen zaƙi a littafinsa biya ɗarinki uku ki karanta ba tare da haƙƙin kowa a kankiba, in kina buƙata ga number ta 09097853276 ki turo katin mtn na 300 ko kimin transfer na 300 ta asusuna na 0005388578 jaiz bank Aisha Aliyu Garkuwa.

By
Chapter 85 · 0% Book details