← Book details Nakasa Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 128 OF 154

Sashe 128

Nakasa Part 2 Complete Hausa Novel · about 7 min read

Dr Adnan kuwa ganin Rahama ta fita, ya sashi É—an É—ago kansa ya dubi Saifuddeen É—in, cikin kulawa yace.
"Nakasa gano sanadin tashin ciwon bayankan nan tunda babu cikakkun na'urorin a wurina wanda zanyi bincike dasu, ka faÉ—i akan bayan naka ne? ko kuma wani abu ne ya samu bayan?." ÆŠan lumshe idanunsa, yayi cikin sassanyar murya yace.
"Ba faÉ—uwa nayi ba." Idanu Dr Adnan ya zuba masa, saida ya nazarce sa naÉ—an wasu sakanni kafun yace.
"To meya faru?." can cikin ƙasa da murya yace.
"disvirgin ɗin Zaleeha nayi, tun alokacin naji bayan ya riƙe yana min ciwo sosai.
please Ya Adnan mu koma india, inajin bayana kaman zai ɓalle." Ajiyar zuciya Dr Adnan ya sauƙe, dan sai yanzu ne ya gano cewa, saboda Saifuddeen ɗin yayi sex da Zaleeha ne hakan ya faru.
Ahmad kuwa dariyar mugunta yayi tare da cewa.
"Hege uban ƴan longomi, wani ne ya aikeka ka jogalo ɓalgaceccen ƙugunka kazo kana mana raki da sakalci ji yadda kuka gigita mana Ummi kaida matarka mai shegen raki ko kunya bakwai".
Ya Adnan kanshi saida yayi dariya, shi kuwa Saifuddeen fuska ya tsuke.
Cikin nutsuwa motar Ameena ta kutso kai cikin gidan, wanda dawowanta daga wajen aiki kenan, anutse ta gama dai-dai-ta parking ɗin motar, saɓa Adeel akafaɗanta tayi, sannan ta buɗe motar ta fito, kaitsaye sashin Ummi ta nufa, duk da cewar agajiye takejin kanta, amma ta riga da ta saba, kullum idan ta dawo sashin Ummi take fara zuwa.
Da sallama É—auke abakinta ta shiga cikin falon.
Shigarta kuwa yayi dai-dai da fitowan Raleeya daga kitchine. Ganin Ameena yasa Raleeya ƙarasowa gareta da gudu, faɗawa jikinta tayi ta rungumeta ƙam, fuska ɗauke da mamaki Ameena tace.
"Raleeya farincikin me kikeyi haka?." Murmushi me kama da dariya, Raleeya tayi, cike da farinciki tace.
"Ranan yau ta kasance ranar farin cikinmune baki É—aya mu yau ranace mafi kyau acikin rayuwarmu, bansan tayaya zan nuna miki farincikin danake ciki ba Aunty Ameena".
Idanu Ameena ta zuba mata, hakanan taji zuciyarta na bugawa, cike da zaƙuwa tace. "Meyake faruwane Raleeya, dan Allah faɗamin, inajin kirjina na bugawa da sauri-sauri" Murmushi Raleeya tayi, tare da yi mata nuni da ɗakin Hayatuddeen, cikin farinciki tace.
"Kishiga ɗakin Hayatuddeen Hamma Saifuddeen nacan." Jin haka yasa Ameena cikin sauri ta nufi ɗakin Hayatuddeen ɗin. A ƙarfi ta tura ƙofar ɗakin ta shiga.
Jin motsin shigowan mutum yasa su dukansu suka kai kallonsu ga ƙofan shigowa ɗakin. Idanu ta zubawa Saifuddeen dake kwance wani irin tsorone ya rufeta ganin yadda yake konce to farin cikinme Raliya keyi bata bayan kuma taga alamun mijinta ba lfy, bata kao aya a tunanin nataba taga, yana miƙo mata hannu, cikin sassanyar muryarsa mai nuna baida lfy yace.
" _Aminatu_ bani Adeel." Kamar amafarki haka Ameena taji sautin muryarsa acikin kunnuwanta, a razane taÉ—an zaro idanunta, sosai jikinta ya É—auki rawa, bakinta na rawa haka ma muryarta tace.
"Abban Adeel, kaine kake magana ko kuwa gizo ido da kunnuwana suke yimin."
Idanunsa yaɗan lumshe tare da jinjina mata kai, cikin son bata ƙarfin guiwa yace.
"Ni ne Aminatu, ba gizo kikeji ba."
Cikin wani irin yanayin farin ciki da wani irin gudu mai kamar sassarfa ta ƙaraso cikin ɗakin tare da faɗawa jikinsa ta ruggumeshi gam-gam kamar mai tsoron a kwace mata shi, cikin tsananin farin ciki tasaki wani irin kukan farinciki, sam ta ma manta da su Dr.Adnan dake cikin ɗakin.
Hannunshin yasa ya dai-dai ta kanta dake kanshi cikin sanyin murya tace.
"Aminatu Zaki ƙara ɓalle bayan ki rasa na yin lilo gaba".
Cikin wata irin yar salama da jin daÉ—i tasa hannu ta shafi gefen fuskarsa, cikin matsanancin farinciki tace.
"Alhamdulillah Ya Allah, Alhandulillah." Murmushin ƙarfin hali yaɗan sakar mata, tare da sanya hannu ya amshi Adeel, dake ta dariya yana wutsil-wutsil da ƙafafunsa kamar yasan farin cikin da sukeyi.
Rungume yaron nasa yayi, yanajin wani matsanancin farinciki acikin ransa.
Ameena kuwa É—an sharce hawayen dake cikin idanunta tayi, tuna cewa su Dr Adnan na É—akin yasa ta É—an janye jikinta baya, tare da cewa.
"Abban Adeel yaushe ka fara magana?." Kasa amsa mata yayi saboda yanda yaji bayansa na wani irin duka, idanunsa ya rumtse da ƙarfi sosai, Dr Adnan ne yaɗan riƙe masa hannu, tare da zaro wayarsa, numbern Dr Aleeyu ya laluɓo, sannan ya danna masa ƙira. Bugu ɗaya kuwa ya ɗauka.
Bayan sun gaisane Dr Adnan ya É—an gyara zamansa.
Cikin nutsuwa yacewa Dr Aleeyu.
"Sir jikin Saifuddeen ne fa ya tashi sosai fa, amman kunnuwansa kuma sun buɗu yanzu duk wani motsi yanaji, sai-dai amma tun ɗazu yake ta complain cewar bayansa ya riƙe, yanzu haka ko zama da kyau baya iyawa, nakasa gano kan matsalan nasa, dan harma yace wai ko zamu koma India ne." Sosai Dr.Aleeyu yaji daɗin buɗuwar kunnuwan Saifuddeen ɗin, saidai jin wata matsala da ta kunno kai duk sai yaji babu daɗi acikin ransa, sai-dai yasan hakan ma wani matakin nasara ne a jinyar tasa dogon numfashi yaja cikin kulawa yace.
"Ai dama lokacin komawarsa india yayi harma ya wuce, bansan me yasa bayason komawa asibiti ba, lalle ya zama dole amaidashi india, dole anjima zan biyo jirgi nazo, zan taho da wasu allurai da magunguna wanda xasu É—an rage masa pain kafin a samu wucewa dashi India, ka gayawa Ahmad ya fara nema musu damar tafiya tun daga yanzu yayi musu bukin ta online."
Cikin jin daÉ—in hakan Dr. Adnan yace.
"Okay Sir shikenan sai kazo".
da haka sukayi sallama, yana ajiye wayar kuwa Ummi ta shigo cikin É—akin.
Ganin Ummi yasa Ameena tashi da sauri ta ƙarasa jikin Ummin cikin tsananin farinciki tace. "Alhamdulillahi Ummi, kunnuwan Abban Adeel sun buɗe ya fara jin magana, Alhamdulillah Ummi, tabbas Allah abun godiya ne."
Kai Ummi ta jinjina tare da cewa.
"Tabbas Ameena Allah abun godiyane, gashi cikin ikonsa ya buÉ—e masa kunnuwansa." Murmushi Ameenan tayi tana kallonsa, ji take kaman ta maidashi cikin jikinta tsabar murna.
Dr Adnan ne yayiwa Ummi bayanin yanda sukayi da Dr Aleeyu, sosai Ummi taji zuciyarta, ta gamsu da zuwan Dr Aleeyun saboda, yanda taga Saifuddeen nacije laɓɓansa, tasan yanajin ciwo sosai.
Ameena ne ta kalli Umm'in, cikin kulawa tace.
"Ummi ina Zaleeha?" Ɗan jim Ummi tayi cike da tausayawa tace. "Zaleeha bata da Lafiya, yanzu haka tanacan sashin Saifuddeen, akwance sai rawan sanyi take, zazzaɓi ne me zafi ya sauƙar mata, so nake idan Dr Adnan ya gama da Saifuddeen, sai muje yaɗan duba ta."
Idanu Ameena ta zaro tare da cewa. "Subahanallah, Allah sarki bari naje na duba ta, ko akwai wani taimakon da zan iya bata".
Kai Ummi ta jinjina, sannan Ameenan ta juya nufin fita,
sai kuma ta tsaya jin an riko hannunta ganin Saifuddeen ne yasa ta matsoshi cikin lumshe ido yace.
"Aminatu Kada ki ce mata kunnena ya buÉ—u kuma ina iya mgna, kinji ko Ummu Adeel".
Cikin jin daÉ—in yadda yake yawan kiranta da yadda yake kiranta Aminatu kana da mmki ta gyaÉ—a kai a ranta tace.
"To meyasa za'a ɓoye mata wannan abin farin ciki, to ko dan bata da lfy ne".
Kai kawai ta gyaÉ—a kana ta juya ta fita daga cikin É—akin.

Kamar yanda Ummi ta faÉ—a mata kuwa, kaitsaye sashin Saifuddeen É—in ta wuce, ganin bata ganta afalo ba, yasa tayi tunanin cewa tana É—aki.
Tana shiga kuwa ta samu Adda Rahama zaune agefenta, dan har yanzu Zaleehan bata daina sakin sheshsheƙan kuka ba.
Ƙarasowa cikin ɗakin tayi, cikin kulawa ta zauna abakin gadon tare dakai hannu taɗan taɓa wuyan Zaleehan, jin jikin Zaleehan zafi zau yasa tace.
"Subahanallahi Ammin Adeel sannu ya jikin naki?".
Kai kawai Zaleeha ta iya jinjina mata dan batajin zata iya wani dogon magana.
Ɗan sake taɓa jikin Zaleehan tayi, tare da duban Adda Rahama, tace.
"Adda Rahama miyene yake damunta bayan zazzaɓi?."
Ajiyar zuciya Adda Rahama tayi, asanyaye tace.
"Tace min tanajin jiri da kuma ciwo acikin jikinta, danko tafiya ma batayi da kyau, nadaiyi mata sit bath, amma gashi nan dai sai rawan sanyi take." Wani irin ƙaton abune ya daki ƙirjin da ran Ameena, har saida taji kanta yaɗan juya mata duhu ya gilmawa ganinta, take ta gano matsalan Zaleeha'n, murmushi taɗanyi tare dayin ƙasa da kanta tana jin wani sassanyan abu a ranta da zuciyarta da sauri ta katse shaiɗan da yin tasbihi, gaba ɗaya ji tayi jikinta yayi sanyi, sai-dai kuma yauɗin ranace ta daban agaresu ranace ta farin ciki su budurcin Zaleeha ya zame musu abin al'fahari tunda sanadin ƙarɓarsa a samu gagarumar nasara a rayuwar mijinta abin soyuwa.
Wayarta ta ciro inda ta laluɓo numbern wata ogarsu Dr Fateema, wanda take nan kusa dasu dan gidanta baida wani nisa, Dr Fateeman na ɗagawa, ta matsa ɗan gefe tare dayi mata bayani, kan cewa suna da patient agida, sannan tayiwa Dr Fateeman bayani, kan cewa ita bazata iya aikin ba.
Da yake Dr Fateema'n, macece mai sauƙin kai hakan yasa tace wa Ameenan gatanan zuwa, dan dama tana gida bata fita ba. Babu wani jimawa kuwa, saigata tazo, ganin yanda jikin Zaleehan yayi zafi sosai yasa tace su bata waje, zata dubata.
Chapter 128 · 0% Book details