← Book details Nakasa Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 15 OF 154

Sashe 15

Nakasa Part 2 Complete Hausa Novel · about 5 min read

Jin isowarsu yasanya dakanta ta buɗe murfin motar ta fice, ko tsayawa batayi ba, riganta na sharan ƙasa haka tanufi ɓangaren nasu, don ta zaƙu da ta cire rigan, sam bata wani iya zama da kaya mai nauyi ba, musamman ma wannan dayake wedding gown.

Shima Saifuddeen saita wheelchair dinsa yayi tare da hawa kai, kaitsaye yanufi cikin gidan nasu.
Kasancewar darene babu wani hayaniya, dayawan mutane bacci suke, waƴanda suka dawo daga wajen diner kuwa tuni kowa ya shige ɗaki don ya ɗan huta,  ahankali yake tura wheelchair ɗinnasa har yaƙaraso cikin falon, idanunsa ne sukayi masa tozali da Umminsa dake zaune acikin falon, yana ganinta yaɗan lumshe idanunsa tare da shagwaɓe fuska, murmushi Ummi tayi tare dayi masa duban tsab, tabbas tasan da cewa Saifuddeen bazai taɓa dawowa har ya kwanta  batare daya neme ta ba, tasan dolene zaizo gareta hakanne ma yasa tazauna afalon zaman jiransa, ahankali ya ƙaraso tare da ɗaura kansa akan kafaɗan Ummin, cikin yanayi na zallan shagwaɓa ya ɓata fuska tare da taɓe red colour lips ɗinsa.
Hannu Ummi tasa tashafi lallausan sumar kansa, cikin kulawa tace.
"Ka gaji ko?."
Kansa yajinjina mata alamar "Eh." Tare da ƙara maida kansa jikinta, tamkar wani yaro ɗan shekara shida haka ya koma mata, sakalci haɗi da shagwaɓa kawai yake zuba mata, komai ta cikin body language ɗinsa yakeyi mata,  sosai Ummin ke lallaɓinsa, sarai dama tasan ɗanta bayason wahala, gashi da ɗanbanzan shagwaɓa, abu kaɗan ke wahalar dashi sai dai jarumtar zuciyarshi na danne sakalcinsa, lallaɓasa Ummi tayi tare da cewa.
Yaje yayi wanka, tun tuni dama tasa anshirya musu abinci akan dinning area.
Da ƙyar Ummi ta iya lallaɓasa yabar part ɗin nata, yana fita yasamu su Ahmad da su Ishaq wai zasuyi masa rakiya zuwa wajen amarya, nanfa yace musu ya gode, ganin cewa dama suma sungaji yasa suma basu matsaba, nan kowa yanemi inda zai huce gajiyarsa, Ahmad da Saminu kuwa kowa matarsa ya kama suka ƙule aɗaki.

Cikin nutsuwa Saifuddeen ya kutsa cikin ɓangaren nasu, babu kowa acikin falon sai daddaɗan ƙamshin turaren wuta, dubansa yakai ga ƙofar bedroom ɗin na Zaleeha, nan yagansa agarƙame, baiwani damu ba yanufi ƙofar dazata kaisa zuwa falonsa, don kuwa  dole sai yabi ta falon Zaleehan kafun yasamu kansa cikin nasa falon.
Yana shiga haɗaɗɗen falon nasa kai tsaye ɗaki ya nufa, kayan jikinsa ya shiga ragewa, saida ya rage dagashi sai gajeren wando sannan ya nufi toilet, shida kansa ya haɗawa kansa hot water acikin bathtube, kwanciya yayi lub aciki tare da lumshe idanunsa, sosai yaji daɗin ruwan don ahankali yaɗanji gajiyan jikinsa naɗan warwarewa,  wanka yayi insa ya fito daga cikin bathroom ɗin bayan ya ɗauro alwala, koda ya fito wata marroon ɗin jallabiya ya sanya, duk da akwai gajiya ajikinsa ko kaɗan hakan bai hanasa yin sallah raka'a biyu ba yana idarwa ya shafa addu'oinsa sannan yabi lafiyar gado, light off na wutan ɗakin yayi tare da jawo blanket ya rufa ajikinsa, lumshe idanunsa yayi, sannu ahankali tunanin matarsa ke mamaye zuciyarsa,  ahaka bacci mai nauyi ya ɗaukesa.

Washegari
Ƙiran sallan asuban fari ya farka, nan yatashi tare da faɗawa bathroom yayi wanka haɗi da ɗauro alwala, koda yafito dogon wandon jeans da kuma white crazy shirt yasanya ajikinsa, sosai kayan sukayi masa kyau, kan kekensa ya hau inda ahankali ya buɗe ƙofar ɗakin ya fice.
Cikin nutsuwa yake tafiya da keken nasa har yakawo cikin falon na Zaleehan, É—an shiru yayi ganin wutan É—akin a kunne da kuma alamun motsi acikin É—akin nata yasa kansa tsaye yafice daga cikin falon, don ya tabbatar da cewa tatashi sallan asuba ne.

Direct masallacin dake gefen gidannasu ya nufa.
Zaleeha kuwa fitsarine ya tasheta koda taga lokacin sallan asuba yayi kuwa shine taɗauro alwala, nan tazo tayiwa Zaheera dake kwance akan doguwar kujeran dake cikin ɗakin tashin duniya amma Zaheera taki tashi, sabida gajiyan hidimr daren jiyan hakan yasa dole Zaleeha ta ƙyaleta, nan ta shumfuɗa sallaya inda ta tayar da sallah,  tana idarwa ta soma gabatar da azkar ɗinta, koda ta gama, wayarta ta jawo inda ta shiga Qur'an app nan ta buɗe suratul baƙara ahankali cikin zuciyarya take karatun sai dai tana farawa kasala da wani gyangyaɗi mara tushe ya rufeta ta rasa meyasa haka cikin kwanakin nan duk sanda zatayi niyar yin karatu sai taji wannan yanayi da kyar take iya farawa dai.

Ɓangaren Saifuddeen ma kuwa tunda yayi sallan Asuba yana nan zaune acikin masallacin, karatun Al'Qur'ani yayi sai 7 dai-dai yabar cikin masallacin, kaitsaye ɓangaren Umminsa ya nufa, dan zuwa gaisheta, kamar yanda ya sabar mata kowacce ranan duniya.
Yana shiga yasameta tana zaune afalo, yayinda gidan yayi shiru duk ana maida baccin da ba'ayiba Daren jiyan shiyasa ita da kanta ta shiga kitchin,
hannunta riƙe da carbi tana ja,  rusunawa yayi agabanta cikin girmamawa yagaisheta cikin body language kamar yanda ya saba.

Ko gama dai-daita zamansa baiyiba fitinannen ƙamshinta yayi masa sallama a hanci, lokaci guda kuma saigata tashigo cikin falon, sanye take da hijab wanda takawo har zuwa ƙasa, sosai hijab ɗin yayi mata kyau, cikin nutsuwa taƙaraso cikin falon Ummi naganinta tasaki murmushi tare da miƙo mata hannu, gefenta ta zauna, har ƙasa ta durƙusa cikin tsananin ladabi da girmamawa tace da Ummi
"Ina kwana?."
da "Lafiya Ummi ta amsa tare da tambayarta ya kwanan baƙunta? ɗan murmushin daya ƙara bayyana zallan kyawunta tayi cikin nutsuwa tace.
"Alhamdulillah!."
Da "Masha Allah!!." Ummin ta amsa, still fuskarta ɗauke da murmushi, hakanan taji wani irin daɗi ya ratsa zuciyarta don kwata-kwata bataiyi zaton haka yarinyar keda ladabi ba, shiru tayi tana kallon yatsun ƙafan Ummi haka nan taji son Ummi cikin ranta,
cikin kula da sonta Ummi ta É—an sunkuyo ta kalleta cikin sanyi tace.
"Ngd É—iya Allah ya muku al'barka ya bamu zaman lfya."
cikin tsunkuyar ds kai da alamun jin kunya murya can ƙasa tace.
"Amin Ummi."
cikin kula Ummi tai murmushin jin daÉ—i tare da cewa.
"Tashi kije ki kwanta kiyi bacci ki huta gajiyan biki."
Cikin jin daɗi ta gyaɗa kai kana ta miƙe hankali tare da ficewa daga cikin falon, ko kallon inda Saifuddeen yake batayi ba, hasalima yi tayi kamar batasan da wani abu waishi mutum awajen ba, ita kuwa Ummi bataji wani abu akan rashin kula Saifuddeen ɗin da Zaleehan tayi ba, domin azotonta sunyi nasu gaisuwar a ɗaki, domin duk atunanin Ummin Saifuddeen ɗin aɗakin Zaleehan ya kwana.
Zaleeha na tafiya Saifuddeen yaɗan zubawa Ummi shagwaɓansa sannan ya nufo part ɗin nasu.
Chapter 15 · 0% Book details