Sashe 116
Nakasa Part 2 Complete Hausa Novel · about 4 min read
Sosai kuwa Baban Khamis yayiwa Saifuddeen godiya, dan yaji daɗin zuwan Saifuddeen ɗin, saboda yayi imani badon shi ba, da Khamis ɗinsa zai jima yana aikata aikin ashsha, wanda bazai tashi ganewa ba, sai lokaci ya ƙure masa.
Haka dai suka ɗan taɓa hira da Baban Khamis ɗin, bayan sun sake yiwa yaran faɗa sosai, Khamis kam yasha kuka, musamman ma da Hamma Saifuddeen ɗin ya ƙara tunatar dashi, girman laifin Zina, da irin hukuncin da za'aiwa wanda ya aikata ta, yayi kuka sosai kuma yayi nadama ƙwarai, gaba ɗaya haka yaji ya tsani abokansa wanda su suka fara ɗorasa ahanyar, har shime yake ƙoƙarin ɗora Hayatuddeen, duk dama shi shaida ne kan cewa Hayatuddeen bai taɓayin zina ba, hasalima baya taɓa shiga sabgan ƴan mata, baya kula wata mace ko ɗaya.
Haka dai sai kusan sallan jumma'a, kafun su Hamma sukayi yunƙurin barin gidan.
Nan Baban Khamis ke ƙara yiwa Saifuddeen ɗin godiya, tare da cewa. "Ya bashi amanan Khamis ya kula masa dashi."
kasancewar Khamis É—in bashi da É—an uwa ko Æ´ar uwa, shi kaÉ—ai ne awajen su, saboda haka bayansu babu wani mesanya idan akanshi, wanda babansa kuma É—an kasuwa ne, da kuma siyasa, hakan yasa baya yawan zama agida, mamansa kuwa babbar ma'aikaciyar banki ne, itama bawai ta cika zama agida bane. Saifuddeen yaji daÉ—in hakan kuma ya amshi, amanar da Baban Khamis É—in ya basa, hakanne ma yasa koda suka tashi tafiya.
Khamis ɗin yace zai bisu, suje masallaci, dan dama daga nan gidan su Khamis ɗin masallacin jumma'a zasu wuce. Direct kuwa daga gidan su Khamis ɗin, Buba Yero Central Mosque suka nufa, wato masallacin sarki kenan. Koda aka idar da sallan jumma'an, ba gida suka nufa ba, can ƙungiyar su Saifuddeen na Jonapwd suka nufa, anan cikin mota Saifuddeen ya barsu, shikuwa ya shige wajen amininsa Ishaq, sosai suka sha hira, anan ma sukayi sallan La'asar, daga nan ne suka biya suka sauƙe Khamis agida, su kuma suka wuce gidan Adda Rahma hira sosai sukayi ta ƴan uwan juna, Dr Adnan da Saifuddeen suna falo sunata hira, nan Ya Adnan yake tuntuɓarsa batun komawarsa India, dariya ya ɗanyi tare da mishi alamun, shifa ya worke.
Adda Rahma kuwa da Hayatuddeen kitchin suke, gaba ɗaya gidan ya cika da ƙamshin zazzafan gashin kaji da Adda Rahma keyiwa Umminta duk bayan wani lokaci.
Koda ta gama a kula ta juyesu da zafinsu sunata turiri, kana ta sawa auta kura a filet, ya fita falo yanaci yana sjishita.
Ita kuwa Adda Rahma sanin Saifuddeen baya cin kazane, yasa ta zaro dangwaleliyar zabuwa a firijin, wonke zabuwar tayi a gudarta ba tare da ta yayyanka kataba ta sata cikin tukunya, wadataccen al'basa ta yanka ta zuba a kai kana ta watsa tafarnuwa akai, maggi da time da corry ta yaryaɗa, kana ta ɗebi dakekken citta da kanamfari ta yayyarfa dai-dai misali, sannan ta rufe ta ɗaura a huta, attaruhu da al'basa da tafarnuwa ta jajjaga mai rai da lafiya, wani irin fitinenne ƙamshi ya cika side ɗin nata gaba ɗaya, har zata ɗaura wata tukunyar jin kiran da Ya Adnan ɗinta ke mata yasa ta fito da sauri,
Ganin Hayatuddeen a tsayene yasata cewa.
"Ina zuwa?".
Saifuddeen ne ya mata alamar.
"Zamu tafi gida lokacin salla ya ƙara to".
Kai ta juya tare da nunawa Hayatuddeen kujera kana tace.
"Koma ka zauna bari in gasa mishi zabuwa nasan baya cin kaza".
Zama yayi tare da cewa.
"To amman dai hardani a zabuwar ma ko?".
Ya Adnan ne yayi dariya tare da cewa.
"Kai Auta wai kai baka gajiya da namane".
Da sauri ya gyaÉ—a kansa alamar eh,
Saifuddeen kuwa, hannun Adda Rahma ya kama tare da mata alamun ta bari karta damu ta sani shi ba wani damuwa da nama yakeba".
Kai ta juya tare da cewa.
"Bana son gardama Saifuddeen ku jira yanzu zan gama".
Baya iya mata musu shiyasa yace to.
Cikin awa ɗaya da ƴan mintuna tayiwa zabuwar nan wani irin fitinenne gashin tukunya mai ɗan karen daɗi da azabar ƙamshi,
a wata kekyawar kula ta saka mishi ita da zafinta sai tururi takeyi,
ta fitowa ta miƙawa Hayatuddeen tace.
"Gashi wannan kuna komawa ka kai mishi É—akinshi, ga madarar shanun shima ka kai mishi, bance da kaiba a zubuwar da madarar uban ciye-ciye".
Tura baki yayi tare da cewa.
"To ni dai gsky ki bani mgnar rabona in ba haka sai nasha nashin."
Dr Adnan ne yayi dariya kana yace.
"ÆŠauko mishi gora É—aya".
Jin haka yasa ta É—auko mishi ai da murnarshi ya amsa ya fita kana suka bishi a baya suna dariyar sangarcin autan Ummi saida Saifuddeen ya shiga gidan Baba Bello ya gaidashi kafin suka shiga mota suka wuce gida.